Jagorancin Imam Sadik (a.s)



Mutanen garin sai suka amsa kiran dattijon nan, suka fita da gaggawa suka sayar wa Abu Ja’afar (Imam Bakir (a.s)) da sahabbansa da abin da suke bukata.[22]

Karshen wannan ruwaya yana nuna mana irin dirar da halifan Abbasiyawa yake yi kan mutane da kuma jabberancinsa. Bayan mutanen birnin sun budewa Imam da sahabbansa kofofin gari sai aka rubuta dukkan abin da ya faru aka aike wa Hisham. Sai ya aiko da takarda zuwa hakimin Madin da umarnin cewa ya kama wancan dattijon ya kashe. Allah ya ji kansa da rahama![23]

Tare da wannan hali, Imam yana nisantar duk wani matsanancin fito-na-fito da yin gaba da masu mulki. Ba ya daukar takobi ba ya kuma yardarwa masu garaje zare tokobi, yana dai shiryar da su ta hanyar hikima. Takobin harshe ma Imam ba ya zarewa idan ba aikinsa na gyara da sauyi daga tushe ya bukaci hakan ba. Kuma bai yardar wa dan uwansa Zaid, wanda fushi da motsin rai ya kai masa iya wuya, yin tawaye ba. A ‘a, shi dai aikinsa yana ba da karfi ne wajen shiryarwar da wayar da kai da tunani, hakan kuma gina tushen manufa (aidiyoloji) ne tare da kula da takiyya a siyasance.

Sai dai wannan salon bai hana Imam ya bayyana wa mabiyansa “harakar imamanci” ba, kamar dai yanda muka yi nuni da shi, bai kuma hana shi karfafa musu babban burin shi’an nan na kafa sahihin tsarin siyasa mai bin tafakarkin Imam Ali (a.s) ba. Wani lokaci ma yana tunzura zukatansu gwargwadon bukata saboda raya wannan burin.

 Daya daga hanyoyin da Imam Bakir (a.s) yake kwadaitar da mabiyansa ita ce ishara ga zamanin mai haske wanda zai zo nan gaba. Wannan kuma yana nuna yanda Imam (a.s) ya kwatanta zangon da yake raye a harakar imamanci. Hakam ibn Uyaina yana cewa: wata rana ina tare da Abu Ja’far (a.s) alhali gidan na cike makil da mutanen gidansa sai ga wani dattijo ya tafo yana tokarawa da mashinsa har ya tsaya bakin kofa ya ce:

Aminci da rahamar Allah da albarkarsa su tabbatar gare ka ya dan Manzon Allah  (watau ya yi sallama). Sannan ya yi shiru. Sai Abu Ja’far ya amsa masa: Aminci ya tabbata gare ka da rahamar Allah da albarkarsa. Sai dattijo ya fuskanci mutanen gidan ya ce: assalam alaikum, sannan ya saurara har jama’a suka amsa sallama gaba dayansu. Sai ya fuskanci Imam ya ce: “Ya dan Manzon Allah ka kusantar da ni gareka, Allah Ya sanya ni fansarka. Wallahi ni ina kaunarku, ina kuma kaunar mai kaunarku. Kuma wallahi ba na son ku  tare da son mai son ku saboda kwadayin abin duniya. Kuma ni ina kin mai gaba da ku ina kubuta (bara’a) daga gare shi. Kuma wallahi ba na kin shi ina kubuta daga gare shi domin wata kullalliya  da ke tsakaninmu. Wallahi ni ina halatta abin da kuka halatta shi, ina haramta abin da kuka haramta shi ina sauraron umarninku. To shin kana mini tsammanin (alheri ),Allah ya sanya ni fansar ka? Sai Imam ya ce: “ Taho nan, taho nan” ya zaunar da shi gangarsa sannan yace:-

‘Dattijo! Lallai wani mutum ya zo wa babana Ali bin Hussain (a.s) ya tambaye shi tamkar abin da ka tambaye ni sai babana (a.s) ya ce da shi:- Idan ka mutu za ka zo ga Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali da Hassan da Hussain da Ali ibn Hussaini, kuma za’a sanyaya zuciyarka, za ka ga farin ciki, za’a tarbe ka da hutawa da kyakkyawan abinci tare da Masu daraja, Marubuta ( kiramun katibuna ). Idan kuma ka rayu za ka ga abin farun cikin da Allah zai sanya ka ciki za ka kasance tare da mu cikin kololuwar daukaka”.

Cikin gigicewa saboda girman wannan albishiri,dattijo sai ya ce:`Ta yaya,ya kai Abu ja’far? Sai Imam ya maimaita masa maganar da ya yi. Sai tsohon nan ya ce:Allahu akbar! Ya Abu Ja’far idan na mutu zan zo wa Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali da Hassan da Hussain da Ali ibn  Hussaini, kuma zan ga abin farin ciki, a kuma sanyaya min zunciya, a tarbe ni da hutawa da  kyakkyawan abinci tare da Masu daraja, Marubuta idan na cika? Idan kuma na rayu zan ga abin da zai faranta mini rai, kuma in zama tare da ku a kokoluwar daukaka?” Sai tsoho ya kama kuka sai da ya kai kasa. Yayin da mutanen gidan Imam suka ga yanayin da dattijon nan ya shiga sai su ma suka kama kuka. Sai dattijo ya daga kai ya nemi Imam ya mika masa hannunsa. Sai ya sumbanci hannun ya sanya shi kan idanu da kumatunsa sanan ya yi ban kwana ya fita. Imam yana kallonsa yana cewa:- Wanda ya so ganin wani mutum daga mutanen aljanna  to ya dubi wannan (mutumin).[24]

Irin wannan fayyacewa tana karfafa ruhin buri a zukatan da suke rayuwa cikin yanayin zalunci da danniya, ta kan wanzar da tunkudawa zuwa ga manufar da ake bida wacce ita ce kafa adalin tsari na musulunci.

 Shekara goma sha tara na imamanci Imam Bakir (a.s) aka yi aiki na gudana bisa wannan mikakken layi mabayyani. Shekara goma sha tara na koyarwa kan manufar gini da dabarun kare kai da   tsare-tsare da kare haraka da takiyya da karfafa ruhin sa-rai da sauransu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next