Jagorancin Imam Sadik (a.s)Barazana da kuntatawa da matsin lamba wadanda suke tattare da ayyukan Imam Sadik (a.s) na ilmantarwa wadanda kuma riwayoyi masu yawa na tarihi ke nakalto mana, sakamakon wannan luran ne da kasancewar mas’alar mai hadari ce. Kazalika muhimmancin da Mansur ya bayar wajen A magarsa da koyarwarsa ga sahabbansa da mukarrabansa, Imam (a.s) yana kafa hujja da “yanayin holoko da jahilci na halifofi†An ruwaito zancensa (a.s):- “Mu mutane ne wadanda Allah ua farlanta biyayya gare mu, kuma kuna koyi da wanda ba’a yi wa mutane hanzari saboda jahilcinsaâ€[38] Abin nufi shi ne mutane sun baude saboda jahilcin mahukuntansu da shugabanninsu, sun dauki hata wanya bata Allah ba. Wadannan ba abin yi wa hanzari ba ne wajen Allah domin biyayyarsu ga wadannan mahukunta aiki ne na baudiya saboda haka ba zai wanke abin da ke biyo bayansa na abkawa cikin baude-baude ba.[39] A koyarwar imamai ( a.s) kafin imam Sadik da bayansa kuna ganin karfafawa Sai mai riwaya ya tambayi Imam ya ce:- Shin makamin yana rabuwa da ilmi? Imam ya ce:- A’a (watau jagorantar al’ummar musulmi wajibine ta zama a hannun wanda yake rike da makami da kuma ilmi gaba daya). Saboda haka Imam (a.s) yana ganin cewa ilmin addini da fahimtar Alkur’ani ingantacciyar fahimta daya daga sharudan imamanci ne. Ta wata fuska kuma ta hanyar aikinsa na ilmi da tara adadi mai yawa na masu kishirwa da begen ilmomin addini a gangarsa, da koyar da addini yanda ya saba cikakkiyar sabawa da hanyar da aka saba wajen malamai da masana hadisi da masana tafsiri masu alaka da tsarin halifanci. Wannan yana tabbatarwa, a aikace, da cewa janibin addini sifa ce ta asali a makarantarsa, da kuma cewa rigar addinin da tsarin halifanci da malaman fada masu daka rawarsu ke da shi ta boge ce. Da wannan hanyar hari mai tsanani mara yankewa kuma cikin tsanaki Imam yake baiwa jihadinsa wata sabuwar kusurwa. Kamar yanda muka ambata a baya, mahukuntan Abbasiyawa na farko wandanda suka sami shekaru da dama kafin su karbi mulki, suna tare da jihadin Alawiyawa kuma mataimakansu suna da masaniya 3. Kafa tsari na sirri Ya gabata cewa Imam Sadik (a.s) a karshen zamanin Umayyawa ya jagoranci wani shirin sadarwa da sanarwa mai fadi wanda kuma manufarsa ita ce kira zuwa imamanci irin na Ali (a.s) da bayyana sha’anin imamanci a
|