Jagorancin Imam Sadik (a.s)



GABATARWAR  MAI TARJAMA.[1]

Wani dan labari dangane da wannan  lacca:-

Wannan labari  yana nuna abinda rayuwa a kasar Iran gabanin Juyin Islama take tattare da shi, na aiyukan tabbatar da musulunci da kuma kalubale da karfen kafa daga  bangaren masu   adawa da kiran .

Wata rana cikin watan Shawwal  shekara ta 1394 H. kararrawar tarho ta buga a gidan  malami mai laccan  a birnin  Mashhad, mai magana a wayar shi ne Shahid Dokta  Muhammad Mufattih  daga Tehran.

Bayan gaisuwa, Sheikh Mufattih sai ya nemi Sidi da ya taho Tehran.ran 25 ga Shawwal (watau ranar wafatin  Imam Jaafar bin Muhammad Assadik (a.s) domin ya gabatar  da  wata lacca kan Imam Sadik .

Halin da ma’abocin  laccar  yake ciki ya kasance  mai kunci a wancan lokacin saboda yawan aiyuka da karantarwa da yawan jama’a masu zuwa daga nahiyoyi daban-daban  na Iran. Yana ba da laccoci a masallacin Imam Hassan da masallacin Alkarama a Mashhad, birnin da ke gabashin Iran, sannan ya tafi yammacin kasar domin gabatar  da lacca a Hamadan da Kermanshah. A cikin Mashhad din kansa  yana koyar  da  tafsiri da Nahjul balaga da hadisi ga kuma  darusan kwarewa a fikihu da usulu.

Duk wadannan  aiyuka Sidi yana gabatar da su ne a cikin  wani hali mai tsananin  matsi, ga wahalar rashin kudi ga ta kuntatawar yanayin siyasa. Ya kasance yana rayuwa  cikin matsanancin  talauci  ba tare kowa ya sani ba. Sannan masu mulki suna matsa  masa lamba suna sa ido ainun bisa duk  abin da yake yi. A wannan shekaran ne suka rufe Masallacin Alkarama, abin da ya sanya Sidi ya takaita  da karamin masallacinsa, watau masallacin  Imam Hassan ya ci gaba da aiyukansa. A cikin hunturun wanna shekarar ne masu  mulki suka sake kama shi, abin da ya kai shi  kurkuku a karo  na biyar ke nan.

To a cikin irin wannan yanayin  ne Sheikh Mufattih  ya bukaci Sidi Khamene’i da ya gabatar da lacca a kan Imam Sadik (a.s) a  Tehran a Masallacin  Javid  inda shi Sheikh Mufattih yake ba da salla. Ma’abocin laccar sai ya ba da hanzari saboda dalilan da muka ambata da kuma saninsa cewa akwai malaman da za su cike gurbinsa a can Tehran, kamar su Sheikh Mufattih kansa. Amma Sheikh ya matsa, saboda haka malamin ya yarda.

Bayan kwanaki Sheikh Mufattih sai ya sake buga waya yana cewa:-

“Yan sanda sun hana taron laccar”  Sidi ya yi  ajiyar zuciya, yana mai jin ya huta da wannan nauyin, ya kuma yi hamdala. Ba’a dade ba sai ga Sheikh ya sake bugo waya yana mai cewa:-



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next