Jagorancin Imam Sadik (a.s)Shekara goma sha Amma hakan bai yiwu ba domin Imam ya tabar da burinsu ya kuma sa wannan dama ta kubuce musu saboda ya sanya wafatinsa ya zama tushen shiryarwa, musabbabin farkawa sannan kuma hanyar wayar da kai mai dorewa. Imam ya umarci dan sa Sadik(a.s) a karshen rayuwarsa, ya umarce shi da wani aiki wanda samfuri ne mai gwanin ban sha’awa daga samfur-samfur na takiyya da kuma salon kira wadanda Imam Bakir (a.s) ya yi amfani da su a zangon zamani wanda ya kebance shi . A cikin ruwaya daga Abu Abdillah Sadik (a.s) ya ce: ‘Babana ya ce da ni: Ka ware abu kaza daga dukiyata saboda a mini zaman makoki na tsawon shekara goma a Mina a ranakun Minanâ€.[25] ..Ita wannan ruwaya , wadanda suka yi bincike Zaben Mina kuwa yana nufin wanzar da aikin a tsakiyar taron jama`a masu tahowa daga dukkanin sassan duniyar musulunci a dai dai lokaci guda daya tak da ake zaune wuri guda yayin aikin haji. Saboda dukkan ayyukan haji ana gabatar da su ne cikin halin motsawa ba tare da sararawa ba idan ba a Mina ba, inda ake kwana biyu ko uku, saboda haka alhazai suna samun isashshen lokaci domin sauraro da ganin kukan rasuwar Imam a wannan wuri zai kuma sa a yi tambaya kan ko wane ne wannan mamacin? Za’a kuma sami jawabi wajen mutanen Madina wadanda suka yi zamani da shi. Za su ce shi daya daga ‘ya’yan Manzon Allah ne, kuma shi ne malamin fukaha`u da masana hadisi. Za’a kuma tambayi dalilin da ya sa ake makokinsa a wannan guri, shin mutuwarsa ta bambanta da ta saura ne? To wane ne ya kashe shi ko ya sanya masa guba? Shin ya kasance wata barazana ga mulkin Umayyawa ne? Da dai sauran su. Gomonin tambayoyi aka yi ta jefowa yayin da ake kukan rasuwar Imam a wannan wuri, sannan masu tambaya suna samun amsa. Kuma labarin ya yi ta watsuwa cikin garuruwa, sako sako, bayan komawar alhazai kasashensu. Akwai kuma masu zuwa daga Kufa da Madina takanas saboda amsa wadannan tambayoyi da yada ruhin shi’a suna daukar damar taron musulmi, damar da ba’a samun tamkar ta a wancan lokacin. Haka Imam ya rayu, haka kuma ya tsara al’amura domin abin da zai zo bayan wafatinsa. Tsira ta tabbata gare shi ranar da aka haife shi da ranar da ya yi jihadi da ranar da ya yi shahada a tafarkin Allah da kuma ranar da za’a tashe shi rayayye. Imam Bakir (a.s) ya rasu yana da shekara hamsin da bakwai a duniya, a zamanin Hisham bin Abdulmalik, wanda yake daya ne daga sarakunan Banu Umayya wadanda suka fi iko. Duk da matsaloli da wahalhalun da suka addabi sarautar Banu Umayya a wancan zamanin wannan bai hana su aikata makida ga zuciyar shi’an nan mai bugawa, watau Imam Bakir, ba. Hisham ya yi ishara ga barorinsa cewa su sanya wa Imam guba, da haka ne kuma ya cimma burinsa na hallaka mafi hadarin abokan gabansa. JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S). Imam Sadik (a.s) ya dauki nauyin ci gaba da wannan tafiya a cikin yanayi mai tsananin sarkakiya da wahala. Bore ya kunno kai a ko ina a daular musulunci, hakimai sun shagaltu da tara kazamar dukiya alhali ga annoba da fari sun aukawa yanki mai yawa wanda ya hada da Kurasan da Irak. Masu mulki kuwa suna tursasawa da zalunci ba tare da rahama ba ko kankani, da haka suke jefa mutane cikin halin kaskanci da mika wuya. Kuma galibi hadarin masu shagaltuwa da ilmomin musulunci kamar fikihu da hadisi da tafsiri bai kasa na ‘yan siyasa da mahukunta ba. Alhali kuwa su ake tsammanin zamansu mafaka ga mutane. Yawa yawan wadannan malamai na kawata fatawowi saboda dadada wa sarki da hakimansa. Da yawa daga cikinsu suna shagaltar da kansu da ma mutane da mas’alolin da basu taka kara sun karya ba, suna ta da jayayyar da ba bakin komai take ba cikin mas’alolin ilmul kalam kuma babu abin da ya danganta ta da musulunci ko wahalhalun da al’umma ke ciki. Nauyin da ya rataya a wuyan Imam Sadik (a.s) a wannan yanayi mai duhu shi ne abin da muka ambata Na biyu:
|