Jagorancin Imam Sadik (a.s)Shi ma ra’ayi na biyun fonko ne kwatankwacin na farkon, kuma bai kafu bisa ilmi ba. Ra’ayin yana SAHIHIN DUBI DUBI NA UKU:- Idan muna son fahimtar yanayin rayuwar Imamai ya wajaba da farko mu fahimci falsafar Imamanci. Tafiyar da aka san ta a mazhabar Ahlulbaiti da sunan Imamanci, wacce ginshikanta mutum goma sha biyu ne daya na bin daya kuma ta dauki kusan tsawon karni biyu da rabi, bisa hakika ci gaban aikin annabci ne. Shi annabi, Allah (s.w.t) yana aiko shi ne da wata sabuwar manhajar rayuwa, da sabuwar akida da wani sabon shirin alakokin dan Adam da kuma sako wanda aka dora masa, gwargwadon shekarun da aka ba shi a wannan takaitacciyar rayuwa. Wajibi ne kira ta ci gaba a bayan Annabi domin sakon ya cimma mafi daukakan matsayin da ake bukata wajen tabbatar da manufofinsa. Kazalika dole ne mutumin da ya fi kusaci da ma’abocin sakon ta dukkanin fuskoki ya dauki nauye-nauyen ci gaba da kira, domin sakon ya kai amintaccen matsayi, ya sami turke mai karfi, tabbatacce mara yankewa. Wannan aiki, babu shakka yana bukatar amintattun mutane. Wadannan sune Imamai, wasiyyan Annabi. Kuma dukkanin Imamai madaukaka kuma ma’abota sako suna da wasiyyai da halifofi. Ba za mu san nauyin al’amarin Imamai ba sai mun san na Annanbi, wanda Alkur,ani mai girma ya bayyana da cewa: “Hakika, lalle, mun aiko manzanninmu da hujjoji bayyanannu, kuma muka saukar da littafi da sikeli tare da su domin mutane su tsayu da adalci……..†[6] Wannan daya daga cikin ayoyi masu baiyana dalilin aiko annabawa da kuma nauyin da aka dora masu ne. An aiko su ne saboda gina wata sabuwar al’umma da tuge ginshikan fasadi da sanarwa Saboda wannan nauyin ne Allah ya aiko annabawa.A matsayin Imamanci na ci gaba da daukar nauye-nauyen annabci, muna iya cewa yana daukar wadancan aiyuka. Da a ce Manzon Allah (s.a.w.a) ya rayu shekara 250 da wadanne ayyuka zai gabatar? Yanda ya aikata wajen kira haka nan Imamai suka aikata. Manufar Imamanci ita ce ta annabci hanyar daya ce watau samar da al’umma ta musulunci adila da kokarin kare ingantaccer tafarkin musulunci. Sai dai abin da zamani yake hukuntawa yana bambanta, kuma gwargwadon wannan bambancin dabaru da solon aiki na sabawa. Annabi (s.a.w.a)da kansa ya yi aiki da wani salo a farkon kira wajen tabbatar da manufofinsa bayan an kai wani zango kuma ya yi amfani da wani salon dabam. Yayin da kirar take farkonta, tana kewaye da barazana da kalubale tana bukatar wani shiri na musamman domin gudanar da aikin ida sako. Yayin da kuma ginshikan tsarin musulunci suka kafu, musulunci ya sami kafuwa a Tsibirin Larabawa sai dabaru da salo suka sake.Tabbataccen al’amari na dindindin shi ne madaukakiyar manufar da sakon ya sauko saboda ita. Shi ne kuma kokarin samar da al’ummar da a cikinta dan Adam yake iya tafiyarsa ta bidan kamala ta dukkanin fuskoki, a ciki ne kuma kwazo da karfin da ke boye cikin halittar dan Adam za su bubbugo. A nan fa kariyar wannan al’umma da tsarinta na musulunci suke. Imaman shi’a, kamar yanda Annabi ya yi, suna faskantar ainihin wannan manufar ne watau kafa adalin tsari na musulunci mai wadannan sifofi kuma bisa wannan tafarki. A dai dai lokacin da ake kafa wannan tsarin ana kuma ba da karfi wajen kariya da tabbatar da dogewarsa. Me kafa tsarin zaman jama’a da ci gaban gudanarsa yake bukata?. Da farko yana bukatar wata manufa ko akida (aidiyolojiyya) mai shiryarwa wacce daga gare ta ne wancan tsarin yake bubbugowa kuma ita take zayyana shi. Na biyu yana bukatar karfin zartarwa mai iya kutsawa cikin wahalhalu da matsaloli da kangiya domin tabbatar da manufar tsarin. Mun san cewa aidiyolojiyyar (ko kuma akida) Imamai ita ce musulunci. Shi kuwa musulunci sako ne madawwami ga dan Adam, watau sakon da ke tattare da sinadarin wanzuwa da tabbatarsa.[8]
|