Jagorancin Imam Sadik (a.s)da wasu baitoci irin wannan. Sai ya kalli fuskata na kalli tasa amma bai ce da ni komai ba, ni ma ban ce masa komai ba. Sai na juya ina kuka saboda abin da na gani. Sai jama’a, babba da yaro, suka kewaye mu. Sai ya tafo har ya shigo dandali, ya Wannan misali ne na alaka tsakanin Imam da mabiyansa na kusa. Yana bayyana tsananin tsari sa alaka kazalika yana nuna wani misali na matsayin hukuma Sannu a hankali bangaren fito-na fito a rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta shi’a yana tabbatar da wani fasali na rayuwar Ahlulbaiti (a.s). Nassoshin tarihi da riwayoyin hadisi wadanda suke hannunmu basu faiyace samuwar wata matsananciyar harakar fama a siyasance wacce Imam yake aiwatarwa ba. Wannan rashin bayyanannar fama yana da dalilai, kamar su wanzuwar wani yanayi na jabberanci da azabtarwa mai mamaye da rayuwar al’umma, abin da ya tisalta wa mabiyan Imam wadanda su kadai ne masu masaniya A takaice, ana iya fahimtar matsanancin matsayin da hukuma ta dauka dangane da Imam Bakir (a.s) ta fuskar mayar da martanin da take yi Daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a karshen rayuwar Imam Bakir (a.s) akwai kiransa da aka yi zuwa hedkwatar halifancin Umayyawa watau Sham (Dimashka). Halifofin Umayyawa sun yi niyyar bincikar matsayin Imam An kawo Imam fadar halifa. Kafin haka Hisham ya yi wa jama’arsa shiftar yanda za su fuskanci Imam yayin da yake shiga. Abin da ya shirya shi ne, shi halifa zai fara bijiro da tuhumce-tuhumce Abubuwa biyu yake da niyyar cimmawa: na farko shi ne raunana azamar Imam da sanya masa rashin yarda da kai. Na biyu: Kokarin sukar Imam a cikin taron da ya hada jagaban jama’ar halifanci da kuma na Imamanci a waje guda, sannan daga bisani a yada wannan cin zarfin ta hanyar kakakin fada kamar masu jawabi da masu wa’azin sarki da kuma ‘yan laken asiri, kuma da haka ne Hisham yake fatar samawa kansa nasara Da Imam ya shigo fadar halifa, sabanin yanda masu shigowa suka saba da yin gaisuwa ga halifa da sunan shugaban muminai, sai ya fuskanci dukkan mahalarta yana mai nuni ga ilahirinsu, ya ce: assalamu alaikum. Sannan ba tare da jiran izinin zama ba sai ya yi zamansa. Wannan abin da Imam ya aikata ya cinna wutar hasada da kufe a zuciyar Hisham. Nan take sai ya fara jefa muggan maganganu yana cewa: ‘ Ya Muhammad Ibn Ali ba’a gushe ba wani daga cikinku yana rarraba kan musulmi, yana kiran mutane da su bi shi, yana kuma da’awar shi ne Imami (shugaba ) saboda wauta da karancin sani ………[20]Ya dai ci gaba da sukar sa.
|