Tambayoyi da AmsoshiCI GABA DA TAKLIDIN MAMACI T24: Wani mutum bayan rasuwar Imam al-Rahil (r.a) ya yi takalidi wa wani marja'i, to amma a yanzu yana so ya sake komawa ga taklidin Imam (r.a) a karo na biyu, shin hakan ya halatta a gare shi? A: A bisa ihtiyat canza takalidi daga rayayyen mujtahidi wanda ya cika sharudda zuwa ga mamaci ba ya halatta, na’am idan har shi rayayye bai mallaki sharuddan takalidi ba to komawa gare shi tun farko bai inganta ba, dan haka, kenan har yanzu yana nan a kan taklidin waccan mamacin kuma yana da zabi imma dai ya ci gaba da taldidin mamacin ko kuma ya koma ga rayayyen mujtahidi wanda ya halatta a yi masa takalidi. T25: Mene ne hukuncin ci gaba da takalidin mamaci idan har mamacin shi ne A'alam? A: Bisa dukan hali ci gaba da takalidin mamaci ya halatta ko da yake ba wajibi ba ne, to amma ya kamata kada abar Ihtiyat wajen ci gaba da takalidin mamacin da yake shi ne A'alam. T26: Shin neman izinin A'alam wajen ci gaba da takalidin mamaci sharadi ne ko kuma za'a iya neman izinin kowane mujtahidi? A: Ba wajibi ba ne takalidin A'alam cikin mas'alar ci gaba da takalidin mamaci, idan dukkan fukaha'u sun yarda da hakan. T27: Bayan rasuwar Imam (r.a) na zaci cewa ba ya halatta a ci gaba da taklidin mamaci kamar yadda fatawarsa ta nuna, don haka sai na zabi wani mujtahidi rayayye don in masa taklid to shin ya halatta in sake komawa ga Imam (r.a) a karo na biyu? A: Ba ya halatta gare ka ka koma gare shi (Allah ya rahamshe shi) bayan ka canza takalidinka cikin dukkan mas'alolin fikihu daga gare shi zuwa ga wani rayayyen mujtahidi, sai dai idan fatawar shi wannan rayayyen mujtahidi ita ce wajibcin ci gaba da takalidin mamacin da yake A'alam kana kuma kai ka yarda da cewa imam (r.a) shi ne A'alam kan wannan rayayyen mujtahidi, to a wannan hali wajibi ne gare ka ka ci gaba da takalidin marigayi Imam (r.a). T28: Shin wajibi ne ga masu takalidin Imam (r.a) kana kuma suke son ci gaba da yi masa takalid su nemi izinin daya daga cikin rayayyun maraji'ai ko kuwa ittifakin da yawa daga cikin marajiai da many an malamai kan halaccin ci gaba da takalidin mamaci ya wadatar?
|