Tambayoyi da Amsoshi



A: Salla da wankan da ba'a yi dai-dai ba, ba ta inganta ba, wajibi ne a sake ta ko kuma a rama ta.

HUKUNCE- HUKUNCEN TAIMAMA

T125: Idan abubuwan da ake yin taimama da su kamar turbaya, ko dutse da sauransu suka kasance ajikin gini ne,suke a damfare shin ya inganta a yi taimama da su ko kuma wajibi ne su kasance a kan kasa?

A: K-asantuwarsu a kan kasa ba sharadi ne na ingancin taimama da su ba.

T126: Idan na wayi gari cikin janaba kana ba zan iya yin wanka ba, har na ci gaba da kasantuwa cikin janabar na wasu raneku, to shin wajibi ne kamar yadda ya kasance a baya in yi alwala ko kuma taimama ga duk wata sallar da zan yi bayan sallar da na yi mata taimama maimakon wanka, ko kuma ina iya takaita da sau guda kawai? Kana a irin wannan yanayi shin alwala ne ya wajaba ko kuma taimama ga kowace salla.

A: Da wani abin da ke bata alwala zai bijiro wa mai janaba bayan da ya yi sahihiyar taimama maimakon wankan janaba, to bisa ihtiyat sai ya yi taimama maimakon wanka kana ya yi alwala.

T127: Shin taimama" da aka yi ta maimakon wanka tana da hukuncin wanka ne? Wato shin zai iya aikata ayyukan da suka halatta ga wanda ya yi wanka ya aikata kamar shiga masallaci?

A: Duk wani aikin da ya halatta a aikata shi da wankan, yana ingantuwa a aikata shi da taimamar da aka yi ta maimakon wanka, sai dai ban da taimamar da aka yi ta maimakon wanka saboda kurewar lokaci.

TI28: A wasu lokuta wani ruwa ya kan fita wa mutum yayin barci, to bayan farkawarsa ba zai iya tuna komai ba sai dai kawai ya ga tufafinsa jike, kuma ba shi da lokacin da zai tsaya don yin tunani saboda sallar asuba za ta tsere masa, to shin me ya kamata ya aikata a irin wannan hali? Shin zai yi niyyar taimama ne maimakon alwala ko kuma wanka? A takaice dai mene ne ainihin abin da ya wajaba a kansa?

A: Idan har ya san janaba ya samu a dalilin wannan mafarki to wanka ya wajaba a kansa, to amma saboda kurewar lokaci sai ya yi taimama bayan tsarkaka jikinsa sannan daga baya ya yi wanka, to amma idan har yana shakkan mafarki da kuma janaba, to hukuncin janaba bai hau kan shi ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next