Tambayoyi da Amsoshi



T75: Shin gudanar ruwa ga dukkan gabobin hannu sharadi ne na ingancin alwala ko kuma shafansu da sauran danshin da ke jikin hannu ya wadatar?

A: Ma'aunin tabbatuwar wankewa shi ne isar da ruwa ga dukkan gabobi ko da kuwa isar ruwan ga dukkan gabobin ta hanyar shafa hannu ne, to amma shafa da danshin da ke hannu kadai ba ya wadatarwa.

T76: Shin yayin alwala ya halatta a shafi kai da danshin da ke hannun hagu kamar yadda ya halatta da na dama ? kana shin ya halatta shafan kai daga kasansa zuwa samansa?

A: Babu wata matsala wajen shafan kai da hannun hagu, ko da yake abin da yake ihtiyat shi ne shafa da hannun dama, sannan kuma a bisa ihtiyat shi ne shafan kai ya kasance daga sama ne zuwa kasa, wato daga tudun kai zuwa wajen goshi, ko da yake akasin haka ma yana wadatarwa.

T77: Yayin shafan kai shin shafan gashi da danshin hannu yana wadatarwa ko kuma waijibi ne sai an sadar da danshin zuwa fatar kai? Kana kuma idan mutum yana amfani da gashin kanti to yaya zai yi shafar kai?

A: Shafar fatan kai ba wajibi ba ne, idan har gashin kanti(kari) ba za, a iya cire shi ba to shafa a kansa yana wadatarwa.

T78: Mene ne hukuncin jinkirtawa tsakanin gabobin alwala ko wanka?

A: Rashin gaggautawa a cikin wanka ba matsala ba ce to amma a alwala idan har jinkirtawar zai kai ga bushewar gabobin da aka riga aka wanke to alwala ya baci.

T79: Mutumin da tusa take yawan fita masa me ya kamata ya aikata yayin alwala da salla?

A: Idan har ba shi da wani lokacin da zai iya kiyaye alwalarsa har zuwa karshen sallarsa, kana kuma sassake alwala yayin salla zai zamanto kunci a gare shi, to ya halatta ya yi salla guda da alwala guda, wato ya takaita da alwala guda ga kowace salla ko da kuwa alwalar ta baci yayin sallar.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next