Tambayoyi da Amsoshi



TI29: Mutum ne ya yi salla da taimama saboda karancin lokaci, to amma bayan idar da sallar sai ya bayyanar masa cewa ashe yana da lokacin da zai iya alwala, to mene ne hukuncin sallarsa?

A: Wajibi ne gare shi ya sake wannan salla.

T130: Muna raye ne a wani yanki da babu wurin da za'a yi wanka, to sai muka farka daga gabannin fitowar alfijir cikin janaba ga shi kuma cikin watan Ramalana ne, tattare da cewa mutane su ga saurayi yana wanka cikin dare da ruwan randa ko tanki babban aibi ne, kana kuma ga shi ruwan yana da tsananin sanyi, to mene ne abin yi dangane da azumin washe gari? Shin ya halatta mu yi taimama? Kana mene ne hukuncin karya azumin saboda rashin samun daman yin wankan?

A: A sabilin wahala ko kuma kasantuwan aikata wani aiki aibi ne a idon jama'a ba uzuri ba ne a fuskar shari'a face dai wajibi ne gare shi ya yi wanka ta duk yanayin da zai iya, matukar dai ba zai kasance da kunci ko cutarwa gare shi ba, to amma idan har akwai hakan to sai ya yi taimama, to zai yi taimama a wannan halin gabannin fitowar aifijir, kuma azuminsa ya inganta, in kuwa ya bari,to azumin ya baci,  amma duk da haka wajibi ne ya rike bakinsa har zuwa faduwar rana.

HUKUNCE-HUKUNCEN MATA

TI31: Mene ne hukuncin dan ruwa-ruwan da mace ta ke gani bayan tana da yakinin ta samu tsarki, tattare da cewa ba shi da wani siffa najini ko kuma jinin da ya hadu da ruwa?

A: Idan har ba jini ba ne to ba shi da hukuncin haila, banbance wannan al'amari kuwa yana hannun macen ne.

T132: Mene ne hukuncin hana yin haila ta hanyar shan magunguna don saboda samun daman yin azumi?

A: Ba wata matsala ga hakan.

T133: Idan mace ta sami matsalar zubar jini yayin da ta ke da ciki, ko da yake cikin bai zube ba, to shin wanka ya wajaba gare ta ko a a? A takaice dai mene ne ya wajaba gare ta ta aikata?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next