Tambayoyi da AmsoshiT9: Shin za'a iya hukunta, taklidin wanda ya yi takalidi ga wanda ba A'alam ba saboda zaton cewa shi A'alam da bai mallaki sharuddan taldid ba, shin za a hukunta irin wannan taklidi da cewa bai inganta ba ? A: Ba ya halatta bisa ihtiyat yin taklidi ga wanda ba A'alam ba cikin mas'alolin da aka samu sabani a cikinsu saboda kawai zaton rash in mallakan sharuddan A'alamiyya ga A'alam. T10: Yayin da aka bayyana wasu malamai da cewa su ne A'alam a cikin wasu mas'aloli (ta yadda ko wani daya daga cikinsu A'alam ne a cikin wasu takamammun mas'aloli). Shin ya halatta komawa gare su ko kuma a'a? A: Rarraba taklid babu matsala a cikinsa, ballantana idan har A'a lamiyyar kowane daya daga cikinsu ta zamana akan mas'alar da yake masa takilidi ne to a wannan hali wajibi ne bisa ihtiyat ya rarraba taklid idan har fatawdyinsu sun bambanta. T1l: Shin ya halatta taklidin wanda ba A'alam ba tare da cewa akwai a'alam? A: Taklidin wanda ba A'alam ba cikin mas'alolin da fatawoyinsa ba su saba wa fatawoyin A'alam ba babu matsala ga hakan. T12: Dangane da Taklid, wane ne ya wajaba mu yi masa takalidi? A: wajibi ne yin taklidi ga mujtahidi wanda ya cika sharuddan ba da fatawa da kuma marjaiyya, kana kuma ya kasance A'alam a bisa ihtiyat. T13: Shin ya halatta a yi taklidi ga mamaci a farkon farawa? A: Ba a barin ihtiyat a farkon farawa, mutum ya yi taklid ga rayayyen mujtahidi wanda yake A'alam.
|