Tambayoyi da AmsoshiA: Shari'a dai ba ta hana rubuta ayoyin kur'ani da sunayen ma'asumai (a's) a cikin jaridu da mujalloli da sauransu ba, sai dai wajibi ne a nesanci wulakanta su da kuma najasta su, kana da kuma taba su ba tare da alwala ba. T101: Mene ne hukuncin jefa abubuwan da suke kunshe da sunayen Allah cikin kogi ko kuma rafi? Shin za'a kirga hakan a matsyin wulakantawa? A: Ba matsala wajen jefa su cikin kogi ko rafi idan hai jama'a ba sa ganin haka wulalkanci ne. T102: Shin sharadi ne yayin jefar da takardun jarabawar da aka A: Yin bincike ba wajibi ba ne, idan dai har mutun bai san da cewa akwai sunan Allah a jikin takarda ba to jefar da ita tare da shara ba matsala, amma takardun da aka yi amfani da wani bangare nasu kana za'a iya amfani da daya bangaren wajen rubutu ko kuma amfani da shi wajen wani aiki, to konawa ko kuma jefar da ita akwai matsala a cikinsa, (wato za'a iya cewa almubazzaranci ne). T103: Wadanne ne sunaye masu albarkan da wajibi ne a girmama su kana haramun ne a taba su ba tare da alwala ba. A: Ba ya halatta a taba sunayen zatin Allah madaukakin sarki, da kuma sunayen siffofin da suka kebantu da Allah Ta'ala ba tare da alwala ba kana kuma ihtiyat a nan ya wajabta cewa sunayen Annabawa (A.S) da kuma sunayen Imamai (A.S) su ma suna da wannan hukunci da muka ambata. T104: Muna da adadi mai yawa na jaridu da muka samu daga wasu mu'assasosi, wadanda da dama daga cikin shafukansu akwai sunayen Allah da dai makamantansu, dan haka muna so ayi mana bayani yadda za mu kiyaye su? A: Kuna iya binne su a cikin kasa ko ku kai su jeji in har a cikin hakan babu wulakantarwa. T105: Wadansu hanyoyi ne shari’a ta yadda da su wajen gogewa ko shafe sunaye masu albarka da ayoyin kur'ani yayin bukatar hakan? Kana mene ne hukuncin kona takardun da suke da sunayen Allah ko ayoyin kur'ani a jikinsu idan har bukatan rabuwa da su ta taso?
|