Tambayoyi da Amsoshi



T38: Shin wadannan ibarori: "Fihi Ishkal""mushkil""la yakhlu min Ishkal"(wato bai fita daga cikin matsala ba)"la ishkal flhi" (wato babu matsala a cikinsa) fatawoyi

A: Dukkansu ihtiyati ne in banda kore ishkal shi fatawa  ne.

 T39: Mene ne banbanci tsakanin rashin halacci da haramun? 

A: Babu wani banbanci tsakaninsu a wajen aiki.

MARJA'ANCI DA WILAYA

T40: A shari'ance mene ne ya wajaba kan musulmai kana kuma mene ne ya wajaba su aikata lokacin da aka sami sabani tsakanin fatawar shugaban musulmai (waliyu amril muslimin) da fatawar wani marja'i cikin mas'alolin zamantakewa, siyasa da al'adu? Shin akwai haddi da ke banbance hukunci da ya fito daga wani marja'i da kuma wanda ya fito daga "waliyul Fakih"? misali idan ra'ayin wani marja'i kan sauraren kida ya saba da ra'ayin "waliyil fakih", shin a cikinsu wanne ne ya zama wajibi a bi shi kana wanne ne bin sa ke wadatarwa?

A bin nufi a nan dai shin wadansu hukunce- hukunce ne ake kira "Ahkamul Hukumatiyya"(wadanda) hukuncin "waliyul fakih" a cikinsu yana da fifiko kan fatawar marja'i?

A: Fatawar waliyu amril muslimin ita ce za a bi (kuma ita ce abin bi)a lamurran da suka shafi hukuma da hukuncin l(asa ta musulunci hakana fatawarsa ita ce abin bi cikin ababen da suka game musulmai duka amma lamurran da suka shafi daidaikun mutane, to kowane baligi zai iya tuntuBar marja'insa a kansu.

T41: Misali idan na kasance ina takalidi wa wani marja'i, sai "waliyu amril muslimin" ya ba da umumin fita

yaki dan fuskantar karirai azzalumai ko kuma ya wajabta jihadi, to amma marja'in da nake masa takalidi bai ba ni izinin shiga yakin ba, to shin zan bi ra'ayinsa ne ko kuma a'a?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next