Tambayoyi da Amsoshi



A: Idan har rashin neman ilmin hukunce hukuncen zai kai shi ga barin aikata wa|ibai ko kuma ya kai shi ga aikata haramun, to ya aikata sabo.

SHARUDDAN TAKLID

T5: Shin ya halatta yin "taldik" ga mujtahidin da ba marja'i ba Kana bai da risala?

A: Idan har ya tabbata ga baligi cewa shi mujtahidi ne da ya cika sharudda, to babu wata matsala ga hakan.

T6: Shin yin taklidi ga malamai (mujtahidai) na wasu kasashe na waje ya halatta ko da kuwa saduwa da su ba zai yiwu ba?

A: Ba sharadi ba ne ga mujtahidin da ake masa taklidi ya kasance kasa daya ko gari daya da mai yi masa taklidi (mukallafi).                     

T7: Bisa ga ra'ayin Imam khumaini (r.a) na cewa dole ne marjain da za'a yi masa takalidi ya kasance masani ne kan  al'amurran  siyasa,  tattalin  arziRi,  aikin  soja, zamantakewa da shugabanci baki daya da kasancewarsa masani kan hukunce-hukuncen ibadu da mu;amaloli, to mu a halin yanzu bayan mun kasance muna taklidi da Imam Khumaini (r.a) sai muka ga ya zama wajibi- bisa la'akari da irin shiryarwar da muka samu daga wajen wasu manyan malaman kana kuma da abin da muka gani da kanmu mu koma gare ka don yin taldid, ta yadda zai zamanto kenan mun hada shugabanci da kuma marjiiyya, to shin mene ne kake gani?

A: Sharuddan cancantar marja'in da za'a masa taklid suna nan an yi cikakken bayaninsu a cikin littafan Tahrirul wasila da sauran littattafa. To amma al'amarin gano wadannan sharudda da kuma zaben wanda ya dace dan yi masa takalidi daga cikin Fukaha'u to ya ta'ailaka ne ga shi kansa mukallaf.

T8: Shin A’alamiyya (fifikon marja'i bisa sauran' yan uwansa) sharadi ne cikin taklid ko kuma a'a ? kana yaya ake gane Aalamiyya?

A: A bisa Ihtiyat wajibi ne yin taklid ga A'alam cikin mas'alolin da fatawoyinsa suka saba da fatawoyin sauran maraji'ai. Kana Aalamiyya shi ne ya kasance ya fi sauran mujtahidai kudura kan sanin hukunce hukuncen ubangiji da kuma kuduran ciro hukunce hukuncen daga inda ake ciro  su.  kana  kuma  masaniya  kan  zamaminsa-gwargwadon abubuwan da suka shafi hukunce- hukuncen sharia da kuma sanin zamani ta yadda zai bayar da ra'ayin fikhu gwargwadon yadda ya dace da shari'a- shi ma yana daga cikin ababen da ke yin tasiri a ijtihadi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next