Tambayoyi da Amsoshi



T144: Mene ne hukuncin gumin mai janaba ta hanyar haram da kuma gumin dabban da take cin najasa?

A: Gumin rakumin da yake cin najasa najasa ne, to amma gumin sauran dabbobin da suke cin najasa in ban da rakumi, haka ma kuma gumin mai janaba ta hanyar haram ba najasa ba ne a bisa magana mai karfi, to amma Ihtiyat na wajibi shi ne kada a yi salla tare da gumin janaba ta hanyar haram.

T145: Malamai a cikin littafan fikhu sun nuna cewan kashin dabbobi da kuma tsuntsayen da cin namansu bai halatta ba najasa ne, to shin kashin dabbobin da ake cin namansu, kamar shanu, tumaki da kaji najasa ne ko kuma a'a?

A: Kashin dabbobin da cin namansu ya halatta ba najasa bane.

T146:  Idan bako  ya najasta   daya daga cikin kayayyakin gidan mai masaukinsa, shin wajibi ne ya sanar da mai gidan?

A: Ba wajibi ba ne ya sanar da shi sai dai in abinci ne ko abin sha ko kuma kwanukan cin abinci.

T147: Shin abin da ya shafi wani abin da ya najastu yana najastuwa? To idan yana najastuwa, shin hakan ya shafi dukkan abubuwan da suka shafe shi ne daya bayan daya ko kuma kawai ya takaita ga na kurkusa ne ?

A: Abin da ya shafi najasa yana najastuwa haka ma abin da ya shafe shi, kana abin da ya shafi na biyun ma bisa Ihtiyat shi ma yana najastuwa, to amma abin da ya shafi na ukun ba ya najastuwa.

T148: Idan mutum ya yi amfani da takalmin da aka yi shi da fatar dabbar da ba'a yanka ta (kamar yadda musulunci ya tsara)ba, to shin wajibi ne gare shi da ya wanke kafarsa duk lokacin da zai yi alwala kasantuwar a wasu lokuta kafar tasa ta kan yi gumi?

A: Idan har ya tabbatar da cewa kafar tasa ta yi gumi a cikin irin wannan takalmi, to wajibi ne ya tsarkake ta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next