Tambayoyi da Amsoshi



T80: Mutum ne ya yi wankan janaba, to sai bayan awa 3 zuwa 4 ya so ya yi salla to amma bai san cewa shin wankansa ya baci ne ko kuma a'a, to shin akwai matsala idan ya yi alwala dan samun kwanciyar hankali (ihtiyat)?

A: A bisa wannan yanayi da ka ambata sake alwala ba wajibi ba ne, to amma yin "ihtiyat" ya halatta.

T81: Mene ne hukuncin wata gaba daga cikin gabobin alwala da ta najastu bayan wanke ta amma kafin idar da alwalar?

A: Hakan ba ya cutar da ingancin alwala, na'am wajibi ne a tsarkake wannan gabar idan za'a yi salla.

T82: Shin kasantuwar  digo- digon ruwa akan kafa yana cutarwa yayin shafa?

A: Wajibi ne a busar da wurin shafa daga duk wani digo na ruwa kafin yin shafan?

T83: Shin shafan kafar dama yana faduwa idan har hannun daman a yanke yake daga asalinsa?

A: A'a ba ya faduwa, face dai wajibi ne a yi shafan da hannun hagu.

T84: Mene ne hukuncin mutumin da yajahiici karyewar alwalarsa sai bayan ya gama ya fahimci hakan?

A: Wajibi ne ya sake alwalar, haka kuma ya sake duk wani aikin da ke bukatar alwala kamar salla da ya yi a baya da wannan alwalar.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next