Tambayoyi da Amsoshi



T70: Idan aka sami idaniyar ruwa tana bubbugowa daga wani guri (kasa) wanda yake gurin mallakar wani mutum ne to idan muna so mu jawo wannan ruwa ta hanyar amfani da bututun ruwa zuwa ga wani guri da ke da nisan kilomitoci hakan zai tilasta mana bi da wadannan bututu cikin filin wannan mutumin da kuma filayen wadansu mutane, to idan har wadannan mutane ba su yarda da hakan ba, shin ya halatta ayi amfani da wannan ruwa dan alwala da wanka da sauran ayyukan tsarki?

A: Babu matsala wajen amfani da ruwan idan har wannan idaniyar ruwa tana bubbugowa ne da kanta, kana kuma kafin gudanarta akan kasa aka ja ruwan nata zuwa cikin wadannan bututu, kana kuma an yi amfani da shi gefen filin da idaniyar ruwan yake da kuma gefen sauran filayen ne ba dan komai ba sai domin kawai ya zama wuri ne na wucewa da bututun, to a wannan hali ba matsala, matsawar ba za'a iya ganin amfani da idon ruwan kamar amfani ne da filin da idon ruwan yake ciki ko kuma amfani ne da filayen sauran mutanen ba.

T71: Yayin wanke fuska da hannaye lokacin alwala idan da mutum zai dinga budewa da kuma rufe famfon da yake alwala da shi, to mene ne hukuncin wannan taba famfo da yake yi da hannunsa mai danshi.

A: Babu matsala ga hakan, ba ya cutar da ingancin alwala, to amma bayan gama wanke hannun hagu kafin yin shafa da shi idan da mutum zai sanya shi a kan ruwan da ke kan famfon to akwai matsala wajen ingancin alwalarsa idan dai har aka dauka ruwan da ke hannunsa da ruwan da ke famfon sun cudanya.

T72: Wasu mata suna da’awar cewa sanya jan farce akan farce ba ya hana alwala, kana kuma yin shafa akan safa mara kauri (shara-shara)yana halatta, shin mene ne fatawarka kan hakan?

A: Idan har jan farcen yana hana isar ruwa zuwa ga faratu to alwala ta baci, sannan shafa akan safa ba ya inganta komi shara-sharansa.

T73: Saboda ciwon shan inna da na samu a kafata sai ya zamanto ina amfani da wani takalmi na musamman da kuma sanduna biyu wajen tafiya, to saboda cire wadannan takalma yayin alwala ba zai yiwu ba, don Allah ina son ayi min bayani kan abin da ya wajaba a kaina dangane da shafan kafa?

A: Idan har cire takalmin dan shafan kafa zai zamanto kunci gare ka, to shafa a kansa ya wadatar kana ya inganta.

T74: Yaya mutum mai yawan waswasin alwalarsa zai yi salla; ko karatun kur’ani da ziyarar kabarin ma'asumai (a. s)?

A: Ba'a damuwa da shakkan tsarki bayan alwala, ya halatta gare shi da ya yi salla da karatun kur'ani matukar dai bai sakankance da bacin alwalarsa ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next