Halayen Zamantakewa (A.S)



Hakika ya zo daga Imam Rida (A.S) daga Amirul Muminin (A.S) daga manzon Allah (S.A.W) ya ce: “ Ya Ali! Farin ciki ya tabbata ga wanda ya so ka ya gaskata ka, azaba ta tabbata ga wanda ya ki ka ya kuma karyata ka, masoyanka sanannu ne a sama ta bakawai da kasa ta bakwai da abin da yake tsakanin haka, su ne ma’abota addini da tsantseni da kawaici kyakkyawa da kaskantar da kai ga Allah madaukaki, suna masu kaskantar da ganinsu, zukatansu suna masu jin tsoron Allah, kuma hakika sun san hakkin wilayarka………â€‌.[21].

A wannan fage karfafa wa ga ruwayoyi a kan wasu siffofi masu yawa da kuma alamomi na asasi ya cika:

Ibada Da Zuhudu

Zuhudu da kuma dagewa a kan ibada da dukkan sasanninta: Hakika ya zo a ruwayoyi masu yawa da aka nuna wannan misali mai kayatarwa. Kamar haka:Daga Abu Ja’afar (A.S) a ruwayar Abu mikdad ya ce: “Ya Abal Mikdad, kawai shi’ar Ali (A.S) su; masu bushewa ne saboda yunwa, masu kyafewa ne, masu yankwanewa, labbansu a yankwane suke, cikkunansu a damfare suke, launinsu a jirkice yake, fuskarsu mai yalo ce, idan dare ya yi musu sai su riki kasa shimfida su fuskanci kasa da fuskokinsu, suna masu yawan sujada, hawayensu masu yawa, addu’arsu mai yawa ce, kukansu mai yawa ne, mutane suna farinciki su suna masu bakin ciki…………â€‌.[22].

Daga ciki akwai ruwayar littafin Irshad na Mufid da kuma littafin Amali na shaikh Tusi: “An rawaito cewa Amirul muminin (A.S) ya fita wata rana mai hasken wata sai ya jagoranci wasu raunanan mutane, sai wasu jama’a da suke bin bayansa suka riske shi, sai ya tsaya musu sannan yace: ku su waye? Sai suka ce: Mu shi’anka ne ya Amirul muminin. Sai ya yi has ashen fusakunsu sannan ya ce: Me ya sa ba na ganin alamomin Shi’a a tare da ku?! Sai suka ce: Menene alamomin Shi’a ya Amirul muminin? Sai ya ce: Masu yalon fuska saboda rashin bacci, masu mici-micin idanu saboda kuka, masu karkataccen baya saobda tsayuwa, masu dafaffen ciki saboda azumi, masu yankwanannun lebuka saboda addu’a, suna da alamar masu tsoron Allahâ€‌[23].

Zamu iya fahimtar wannan darajoji masu kayatarwa a wannan sura ta wannan misali rayayye da imam Ali (A.S) ya sanya ga dan Shi’a, a wannan bayani da imam Ali (A.S) ya gabatar a hadisinsa tare da Ahnaf Dan Kais a abin da ya rawaito daga Saduk a littafinsa na siffofin Shi’a ya ce: “Yayin da Amirul muminin Ali (A.S) ya gabato basara bayan yakin mutanen jamal sai Ahnaf Dan Kais ya kira shi ya kuma yi masa Abinci, sai imam (A.S) ya kira shi ya kuma kirawo sahabbansa, sai ya fuskanto ya ce: Ya Ahnaf ka kira min sahabbaina, sai wasu mutane suka shiga wajansa suna masu kaskan da kai kamar salka mai tsiyaya, sai Ahnaf Dan Kais ya ce: Ya Amirul muminin, Menene ya same su? Shin karancin abinci ne? ko tsoron yaki? Sai (A.S) ya ce: A’aha ya Ahnaf, hakika Allah madaukaki ya so mutane ne da suka bauta masa a wannan duniya bautar wanda ya fuskanto ga abin da ya sani na kusantar ranar lahira kafin su gan ta, sai suka daukar wa kansu wahalhalunta, suka kasance idan suka tuna da ranar bijirowa ga Allah sai su ga kamar wata wuta ce da take fitowa daga wuta tana mai kora mutane zuwa ga ubangijinsu madaukaki, da kuma littafi da ake daidaita shi a gaban shaidu na abin kunya na zunubai, sai ransu ta kusa kwarara, kwarara mai tsanani ko kuma zukatansu suka tashi da fuka-fuki na tsoro tashi mai tsanani, hankulansu suna tafarfasa da su tafarfasa saboda tsoron Allah madaukaki, sun kasance suna masu kuka kukan mai jin tsoro a duhun dare, sun kasance suna tsorata daga tsoro na abin da ransu ta yi sai suka wuce suna masu yankwanannen jiki, zukatansu masu bakin ciki, fuskokinsu masu rasa bacci, lebbansu masu zaganyewa, cikkunansu masu damfarewa, kana ganinsu suna masu magagi mai raya dimuwar tsoron cikin dare. Suna masu tsoro kamar kai ka ce su kamar salka mai yoyo, sun tsarkake ayyukansu da ikhlasi ga Allah a boye da sarari, zukatansu ba sa aminta daga tsoronsa, sai dai sun kasance kamar wanda ya kwana yana gadin –rasa baccin- babban ciwonsa.

Da ka gansu a darensu, yayin da idanu suka yi bacci, muryoyi suka nutsa, motsin tsuntsaye ya dakata, a cikin sheka. Kuma tsoron ranar alkiyama ya hana su runtsawa saboda alkawarin narkon azaba, kamar yadda Allah (S.W.T) yake cewa: “Shin ma’abota alkarya sun aminta ne daga cewa azabarmu zata zo musu da dare suna masu barciâ€‌.

Sai suka tashi suna masu tsoro, suka tashi zuwa sallarsu suna masu guji da kuka, wani lokaci kuma suna masu tasbihi, suna masu tsoro a mihrabinsu suna masu ruri, suna masu zabar dare mai duhu maras hayaniya suna masu kuka.

Da ka gan su ya Ahnaf a darensu a tsaye a kafafunsu, bayansu yana karkace suna karanta juzu’o’in kur’ani na sallarsu, kukansu da nishinsu da ihunsu sun tsananta, idan suka yi kara sai a dauka cewa wuta ce ta kama su zuwa makogaro, idan suka yi gunji sai a yi tsammanin an sanya sarkoki an daure wuyayensu ne, da ka gan su da rana da ka ga mutane da suke tafiya a kan kasa da sauki suna gaya wa mutane kalmomi masu dadi, idan kuma jahilai suka yi musu magana sai su fadi kalmar aminci, idan suka wuce wajan wasanni sai su wuce suna masu girmamawa, sun kayyade diga-diginsu daga tuhuma, sun bebantar da harsunansu daga magana ga mutumcin mutane, sun rufe jinsu don kada su ji kutsawar nan ta masu zantukan banza, sun sanya wa idonsu runtsewa daga ganin sabo, sun kusanci gidan aminci da wanda ya shige ta ya kasance amintacce daga kokwanto da bakin ciki.

Ta yiwu ya kai Ahnaf kallonka ga fuska daya ne ya shagaltar da kai da take bayyanar da alama ta rashin lafiya sakamakon runtsewar fuskar ga barin ganin sabo, da kuma gida da ya shagalta da zane-zanensa na ado, da kuma labule (manya masu ado da aka suturce gidan da su) da ka rataya, da kuma iska mai dadi, da kuma shuke-shuke da â€کyar korama da ake cin â€کya’yan itaciyarta, wannan gidan naka ba gidan wanzuwa ba ne, amma sai ya shamakance ka daga gida da Allah ya halitta daga farin lu’u-lu’u, ya kuma tsaga kormu a cikinta, ya kuma dasa bishiyoyinta, ya kuma lullube ta da â€کya’yan itace nunannu, ya kuma mamaye ta da kyawawa daga hurul’in, sannan sai ya zaunar da masoyansa ma’abota biyayyarsa wannan gidan.

Da ka gansu ya Ahnaf sun gabato zuwa ga abin da ubangijinsu ya tanadar musu, idan aka bigi goshinansu sai ababan hawansu su yi wani sauti da masu ji ba su ta ba jin sauti mai kyau mai dadi irinsa ba, kuma gajimare ya lullube su sai ya yi musu ruwan almiski da radin, kuma dawakanta su yi haniniya tsakanin dashe-dashen wannan lambuna, kuma rakumansu su kusa da su tsakanin tarin damki na za’afaran, suna masu taka lu’u-lu’u da marjan da tafin kafafunsu, kuma masu gadinta suka tarbe su da minbarori na iska mai kanshi kuma wata iskar ta taso daga karkashin al’arshi sai ta yada musu yasimin da akhawan, sai su tafi zuwa kofarta sai ridwanu ya bude musu kofa suna masu sujada ga Allah a farfajiyar aljanna, sai jabbar ya gaya musu: Ku daga kawukanku, hakika ni na dauke muku wahalar bauta na zaunar da ku aljannar yarda ta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next