Halayen Zamantakewa (A.S)



Wannan ta wani bangare ke nan, ta wani bangaren kuma hukuncin shari’a zai zama ba shi da wani abin da zai biyo baya na mutumtaka, sai ya zama hukunci ba komai ba ne sai bayani na iradar ubangiji na shar’anta hukunci ga bayi ba tare da wata manufa ba da sakamakon abin da zai biyo baya.

Amma sabanin haka, zamu ga koyarwar Ahlul Baiti (A.S) ta karfafa al’amari biyu a wannan fage:

Na farko: Al’amarin riskar mutum ga kyakkyawa da mummuna a cikin abubuwa a dunkule, kamar yadda yake riskar munin azabtar da wanda aka tilasta, da munin kallafa wa wanda ba shi da irada, kuma wannan riska ta al’amuran kyawawan dabi’u shi ne yake shiryar da mutum zuwa ga sanin dayawa daga hakikanin al’amuran ubangiji.

Na biyu: Hukuncin shari’a ya zo domin ya yaye ya kuma iyakance wa mutum wannan riska a dunkule, ya kuma haskaka masa hanya domin isuwa zuwa ga hakika da Allah ya halitta shi a kanta. Ta yadda hukuncin shari’a na Allah zai zama ba kawai lizimtawa da tilasatwa da kuma furuci da Allah (S.W.T) yake yi da ikonsa maras iyaka ba, sai dai a janibin wannan yana misalta adalci da hikima ta Allah da wadata madaukakiya ga ayyukan wannan mutum, wanda yake nuna maslaha da fasadi da ya damfaru da rayuwar mutum da kuma hanyarsa ta kamala a wannan rayuwa da take ma’abociyar samuwa da abin da ta kunsa na kyawawan dabi’u.

Da wannan ne zamu fahimci mahimmancin kutsawa cikin al’amuran kalam da Ahlul Baiti (A.S) suka kutsa cikinsa suka kuma iyakance bangaren kyawawan dabi’u a hukunce-hukncen shari’a ta hanyar al’amarin riskar abu kyakkyawa da mummuna a iradar mutum, da kuma jefa fikirar “Babi tilas babi fawwalawa al’amarin al’amari ne tsakanin wadannan al’amura biyuâ€‌ a alakar irada ta mutum da iradar ubangiji, ayyukan mutum wadanda su ne mahallin hukuncin shari’a, aiki ne da ya gangaro daga iradar mutum, kuma shi ne yake daukar nauyinsu, sai dai mutum da dukkan samuwarsa shi abin halitta ne na Allah madaukaki kuma Allah ya halicce shi mai nufi, shi mutum da dukkan samurwarsa da wanzuwarsa da ikonsa yana karkashin nufi da iko na ubangiji ne, ba ya iya tasarrufi shi kadai ba, ba tare da taimakon Allah ba da ya ba shi rayuwa da samuwa da iko.

Ahlul Baiti (A.S) sun yi amfani da wannan muhimmancin kyawawan dabi’u daga kur’ani mai girma ta yadda zamu samu kur’ani yana buga misali ga mutum da yake karfafa masa iko da nufi ga dan Adam, kamar misalin fadinsa madaukaki: “Allah ya buga misali da bawa abin mallaka da ba ya iya komai…â€‌[57]. Ko kuma ya jefa masa tambaya ta hankali misali: “Shin wadanda suka sani zasu daidaita da wadanda ba su sani ba?â€‌[58]. ko ya jefa masa ma’anoni (kamar kyau da muni) misali: “Kyakkyawa da mummuna ba sa daidaitaâ€‌[59]. ko adalci da zalunci, ko gaskiya da karya, ko rowa da zabin wani a kan kai, da makamantansu na daga dabi’u, hakika kur’ani yayin da yake magana kan dukkan wannan yana so ne ya yi magana da mutum da wadannan mariskai na fidira na samuwarsa ta badini da take ita ce asasin ayyukansa na kyawawan dabi’u, wannan al’amari kur’ani mai girma ya iyakace ma’anarsa dalla-dalla, abin da muke ce masa; Kyakkyawa da mummuna na hankali.

Ba ma so a nan mu yi bincike na bahasin kalam da kyawawan dabi’u sai gwargwadon yadda muke so mu fadakar da cewa Ahlul Baiti (A.S) yayin da suka fuskantar wa mabiyansu lizimtar wannan akida, ya kuma zama daya daga asasin mazhabarsu wanda shi ne lizimtar (adalcin Allah), suna son ta wannan hanya su assasa ka’ida ta kyawawan dabi’u wajen gina ruhi da sirrin badinin mabiyansu, su samar da nau’i na tsari na ruhi da zai kare su fadawa ga karkatar kyawawan dabi’u mai muni, kamar zalunci da shisshigi, ko taimaka musu, ko shiru gabarin hakan alal akalla.

Bambanci Tsakanin Musulunci Da Imani

2-Karfafa al’amarin bambanci tsakanin musulunci da imani a dabi’ance kamar yadda kur’ani mai girma ya zo da hakan; “Larabawan kauye suka ce: Mun yi imani, kace ba ku yi imani ba, sai dai ku ce mun musulunta har yanzu imani bai (wada) shiga zuciyarku ba tukuna, idan kuka bi Allah da manzonsa babi wani abu daga ayyukanku da zai tauye muku, hakika Allah mai gafara ne mai rahama. Kawai muminai su ne wadanda suka yi imani da Allah da manzonsa sannan ba su yi kokwanto ba, suka yi jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu a tafarkin Allah wadannan su ne masu gaskiyaâ€‌[60].

Da wannan ne musulunci da karbar shaida biyu, da ranar lahira, da lizimtuwa da salla, da azumi, da hajji, da zakka, suke a daraja ta farko a tsanin akidar musulunci, da kuma wannan ne ake kare jini, da dukiya, da mutunci, da kuma gudanar rayuwa ta zmaantakewa ta gaba daya akansu, sai dai ta nahiyar kyawawan dabi’u wannan yana sassabawa sakamakon lizimtar musulunci da kuma sakamakonsa.

Amma imani shi ne yake misalta daraja madaukakiya na kafuwar akida da kuma tabbatar ta da lizimtar hukunce-hukuncenta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next