Halayen Zamantakewa (A.S)



Fikira Da Akida

 

Fasali Na Farko: Fikira Da Akida

Hakika Ahlil Baiti (A.S) sun himmantu himma ta musamman game da janibin fikira da akida, domin su ne ake gani a matsayin asasi da za a iya gina jama’a akansu. Daidai gwargwadon karfi da daidaito da da gamewa na wannan bangre ne, jama’a zata iya zama mai karfi da iko wajan fuskantar wahalhalu da matsaloli da yanayi daban-daban da rayuwar dan Adam take doruwa a kansa.

Ta haka ne ta wannan mahanga ta bangren akida da tunani zamu samu cewa kur’ani yana himmantuwa da wannan himatuwa mai girma, yana warware matsalar al’amarin akida da tunani Kafin kowane abu, yana kuma kafa wannann al’amari a cikin al’umma.

 Muna iya la’akari da cewa wannan jama’a ta gari wacce Ahlul Baiti (A.S) suka dasa ta, ta hanyar amfani da wannan janibi na (fikira da akida) ta wadannan abubuwa ne masu zuwa:

Kur’ani Da Sunna (Su Ne) Asasin Akida

1-Lizimtuwa da jefa tunani da akida da za ake tsamo ta daga kura’ani mai girma da sunnar annabi ingantacciya, ta yadda suka zama da’iman suna kafa dalili a kan wannan akida ta hanyar amfani da ayoyin kur’ani da hadisan Annabi (S.A.W), hada da lizimtuwa da cewa wannan ya yi daidai da fidira kubutacciya ta dan Adam.

Muna iya ganin wannan a fili ta cikin nassosi da suka zo daga imama (A.S) a wajan bayanin wadannan akidoji da fikirori, haka nan sun yi amfani da wannan a cikin usulubi da hanyar kafa hujja da tattaunawa game da akidojin wasu mutanen daban[46].

Hakika Ahlul Baiti (A.S) sun bayar da muhimmanci na musamman ga hankali wajan fahimtar akida, sai dai wannan ya zama domin kafa tsarin tafarki ingantacce ne domin riskar al’amura kamar yadda zamu yi nuni da haka a magana ta hudu, da kuma samar da nutsuwar rai da yakini a tunananin akida wacce ba ya inganta a kai ga gaskiya acikinta ta hanyar riko da zato. Tare da haka ba su gafala ba game da al’amarin karfafa wa cewa dukkan akida ingantacciya da kur’ani da sunna suka zo da ita hankalin dan Adam da fidirarsa kubutacciya sun karfafe ta.

Kamala Tsakanin Akida Da Mazhaba

2- kiyaye kamalar mazhabar da ta akida a akida da fidira da rayuwa da kuma duniyar gaibi da sarari, da kuma rassan wannan akida ta wani bangaren. Ai ma’ana samun kamala tsakanin nazari da kuma dabbakawa, da kuma tsakanin akida da aiki, da kuma tsakanin asali da reshe. Mazhabar imamiyya ta tsayu ne a kan asasin akida da Ahlul Baiti (A.S) suka zama su ne suke misalta misali mai girma da ya damfaru da akida a nazari na gaba daya na musulunci, kuma imamanci ya tsiro ne daga addini wanda yake daga Allah da yake kamanta samuwar sako da kuma daukar nauyin isar da shi idan ka debe wahayi, domin imami nadawa ne daga Allah kamar yadda manzo aike ne daga gareshi madaukaki.

Hakika aikin mutum yana tasirantuwa da fahimta ta akida ta yadda ake ganin alaka tsakanin imani da wilaya da kamalar aiki.

Hakika kulaini ya rawaito a cikin ingantattun hadisai daga dayansu (A.S) ya ce: “Imani furuci ne da aiki, musulunci kuma furuci ne ba aikiâ€‌[47].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next