Halayen Zamantakewa (A.S)



Matsayinsu wannan yana da tasiri mai girma wajan kafewa da cijewar jama’ar musulmi a gaban duk wani mummunan tunani na â€کyan mulkin mallaka mai yakar fikirar ahlul baiti (A.S) da kuma kariya ga asalin riko da zama a bangaren gaskiya kodayaushe da wanzar da tunanin ki ga zalunci da kuma hayewa da rintse ido game da al’amarin duniya.

Mutumtaka Da Kuma Fadin Tunani (Yalwar Kirji)

 Kashe wutar kAbulanci da bangaranci tsakanin musulmi, musamman tsakanin kAbulun larabawa wacce ta samo asali daga lokcin jahiliyya, kuma ta taso sakamakon bude-buden yakokin musulmi mai fadi da cakuduwar musulmi da mawali, kuma an samu bayyanar wannan al’amari a lokacin umayyawa a fili, wanda ya sanya jayayya da yake-yake tsakanin musulmi da kasa su zuwa larabawa da mawali, sannan abin ya ci gaba zuwa lokacin abbasawa da usmaniyawa.

Shi’ar Ahlul Baiti (A.S) sun kasance a ayyukansu na addini suna misalta ruhin â€کyan’uwantaka tsakanin musulmi, ba sa jin bambanci tsakanin al’ummu ko kAbulanci, wannan kuma ya kasance ne sakamakon tasirantuwa da imamansu a wannan fage da aka samu da kiyaye shi tsakannin wannan jama’a mai rauni da ta karbi msusulunci bayan bude-bude, wacce ta kasance tana fama daga nuna mata kAbulanci da bambanci na zamantakewa, da daukar su a matsayin jama’a mai daraja ta biyu a kasa.

Daga nan ne aka samu irin jifa da kalma da tuhuma da Shi’a suke fuskantarsa, ba su gushe ba kuma har yanzu suna fuskantar jifarsu da cewa su ajamawa ne, domin su sun kasance suna rayuwa tare da kowa da juciya daya da jin â€کyan’uwantaka cikakkiya, kamar yadda suka kasance suke tausaya musu tsakanin mutane da mawali da ajamawa sakamakon budadden tunani da suke da shi.

Sadaukarwa Da Shahada

Dasa tunanin sadaukarwa da fansa da kiyaye wannan tsakanin al’ummar musulmi da kuma yada tunanin kin zalunci da dagutanci, saboda haka ne suka zama suna da muhimmin aiki da suka gabatar ga wannan al’umma ta gari a tsawon tarihin musulunci a zamuna daban-daban, wajan haifar da tashi tsaye domin neman â€کyanci da kawo gyara ga yanayi gurbatacce a cikin jama’ar musulunci, ta yadda suka kasance suna tsayuwa da wannan suna jagorantar hakan kai tsaye ko kuma ta hanyar tasirin wannan canji a tsakanin al’umma da jama’ar musulmi gaba daya[3].

Wannan al’amari ya ci gaba da bayyana a tafarkin mabiya Ahlul Baiti (A.S) da alakarsu a tsakninsu da sauran al’ummar musulmi har zuwa zamaninmu wannan wanda wannan tasiri na yau da kullum ya bayyana a fili.

Mafi muhimmancin wannan hususiyya da mabiya ahlul baiti (A.S) suke kebanta da shi shi ne lizimtarsu da haramci na sake-ba-kaidi a mu’amala ko alaka tare da azzalumai da ja’iran shugabanni sai dai a halin da aka toge[4].

Kare Shari’ar Musulunci Daga Karkacewa

Hakikan kare shari’ar msusulunci yana daga manyan hadafofi da imamai suka dauka don gina jama’a ta gari, yayin da imamai (A.S) suka kasance suna kokarin cimma wannan hadafi a lokacin rayuwarsu domin kada a jarrabci shari’a bayan fakuwarsu da karkacewa da gurbacewa da tozarta, sakamakon yananin siyasa da son rai da sauran dalilai da suka zama sabAbun gurbacewar sauran addinai da tozartarsu, al’amarin da ya tilasta samar da jama’a ta gari da ba makawa gare ta da daukar wannna nauyi na bayan nan, musamman cewa wannna sakon na musulunci shi ne sakon karshe da ya zama wajibi a kiyaye shi daga tozarta, wannan kuma duka ba ya takaita da kiyaye maslahar danadam da cigabansa ba wanda ya ke tabbata wajan riko da dokokin na gaskiya na sakon ba kawai, sai dai ya hada da wajabcin tsayar da hujja daga Allah a kan al’umma a kowane zamani, “Domin kada ya zama akwai hujja ga mutane a kan Allah bayan manzanni[5]â€‌.

Saboda wannan muhimmin lamari da mabiya ahlul baiti (A.S) suka tsayu da shi wajan kare shari’ar muslulunci da kuma tafarkinsa na asali zamu yi nuni zuwa ga bayanai masu zuwa game da jama’a ta gari mai misalta biyayya ga Ahlul Baiti (A.S):

Asasin Dauki-Ba-Dadi

Nan farko: Lizimtuwar akida da tunani da asalin riko da siyasa wajan gaba-da-gaba da azzalumai da fuskantarsu wanda yake mabiya Ahlul Baiti (A.S) sun siffantu da shi, ta yadda wannan asali kuma asasi na musulunci ya samu hare-hare domin kawar da shi da bice shi, ko ta hanyar kisa da kora, ko ta hanyar batarwa da karkatarwa. Hakika an sanya nassosi da hadisai da yawa na karya na kage ga manzo (S.A.W) domin gyarawa da hallata mika wuya ga azzalumai da kuma karbar hukuncinsu da sarauntarsu, ta yadda wannan ya yi tasiri ga dukkan al’ummar musulmi, jama’a ta gari mabiya Ahlul Baiti (A.S) ta wanzu ita tana mai bin wancan tafarki da kuma lizimtuwa da hanyar siyasarsa, kuma jama’a bayan jama’a sun nakalto mana wannan labari ba kawai a matsayin nazari ba shi ke nan, sai dai ya hada har a matsayin aiwatarwa da matsayin siyasa a aikace.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next