Halayen Zamantakewa (A.S)



Hada da cewa hadafin wannan matsayi na siyasa ya kasance tunani ne da koyarwa ta Ahlul Baiti (A.S) da jama’a ta gari suke dauke da shi, don gudun kada ta sake ta sanya fitar da fatawa daga hukunce-hukuncen shari’a ya zama ya kaskantar da kai ga tasirin azzalumai da abin da suka yi gini akai, ta yadda suka misalta aiki na ginshikin â€کyancin kai a matsayin jama’a ta gari daga mahukumta a aikace da kuma nazari, da kuma rarrabe al’amarin ijtihadi daga yanayin siyasa mai hukunci karkatacce, wannan yana daga cikin abin da mabiya Ahlul Baiti (A.S) suka kebanta da shi.

Ijtihadi A Bisa Asasin Kitab Da Sunna

Na biyu: Wanzuwar kofar ijtihadi a bude amma a cikin farfajiyar asasi da dokoki da suka dogara kai tsaye a bisa madogarai ingantattu da mafi muhimmancinsu su ne (Littafi Da Sunna), a yayin da cewa wata jama’ar musulmi ta dogara a kan wasu madogarai daban (saboda dalilai masu yawa) kamar kiyasi da istihsani da masalihir musila da zancen sahAbu da sauransu, wanda daga karshe ya tilasta masu bayan duk haka suka kulle kofar ijtihadi abin da ya kai ga cutuwa mai tsanani da shari’a ta samu a aikin fitar da hukunci da dabbaka hukuncin shari’a a kan dokokinsa na asali da kuma sababbun maudu’ai, wanda yakai ga sanya shari’a cikin hadari mai girma na karkatarwa. Wannan kulle kofar ijtihadi ko iyakancewa ta haifar da abubwa munana masu girma a kan aikin fitar da hukunci, da kuma karfin shari’ar musulunci wajan warware mas’alar sabon cigaba da ya fuskanci al’ummar dan Adam, fikihu ya zama yana rayuwa a halin fari (bushewa) da tsanani tsakankanin mutane, al’amarin da ya sanya mafi yawan mutane da malamai a lokuta da zamuna daban-daban suna da sabon tunani na burin sake bude kofar ijtihadi musamman a wannan zamani.

Sabanin siffar da wannan jama’a ta gari daga mabiya Ahlul Baiti (A.S) suka kebanta da ita na aikin fitar da hukuncin shari’a bisa dokokinta, ta yadda ya zama mai cigaba domin sabuntuwa ba tare da samun wani hadari na karkacewa ko afkawa karkashin tasirin tunanin yamma da wayewar masu musun samuwar Allah ba, ta kuma wanzu tanan mai bayar da sakamako tare da kiyayewa ga asalinta a madogarar shari’a da littattafai da madogara tsarkakkiya, kuma duk da haka ta zama jama’a mai iko a kan kiyare shari’a da gadon musulmi.

 Ã¢â‚¬Ú©Yancin Tunani

 Na uku: Iko a kan â€کyancin tunani da la’akari da tadabburi da bincike a al’amura daban-daban na falsafa da kalam da siyasa mai nisanta daga dukkan yanayi sandararre ko dabaibayi na tunani da aka tilasta samuwarsa a siyasance da a manzhabance. Al’amarin da ya sanya wannan jama’a mai iko wajan nakadi da suke abin da ba daidai ba na tarihin musulunci bisa dalilai, da kuma farar da wani abu da cigabantar da shi wajan fahimtar bahasi na falsafa ko kalam da kuma shiryawa domin fuskantar kalubalen nazarori na fikirori da falsafa a zamuna daban-daban.

Duk da samun kokari muhimmi a wannan fage na tarihin musulunci, misali kokarin mu’utazila da ikhwanis safa, sai dai sun samu tasgaro da rushewa, sakamakn rabuwarsu da asalin asasin tunani na asali da kuma taskace mahangarsu da mazhabar da take mai iko a wannan lokuta.

Jin Tsoron Allah Da Adalci

Na hudu: Dasa takawa da adalci da aminci a dabi’ar mutum da kuma aikata aiki mai girma kuma mai muhimmanci da asasi a rayuwar zamantakewar dan Adam da yake siffantuwa da gaskiya da kyawawan dabi’u, ba a karbar wilayar wanda ba a adali ba, ko shaidarsa, wannan sharadi ne hatta ga limamin jam’i, da shaidun saki da hukunci da alkali, kuma ba makawa mai rawaito hadisi ya zama amintacce, ba tare da la’akari da bangarensa na siyasa ba, sai a karbi ruwayar mukhalif (wanda ba Shi’a ba) a mazhaba da akida idan ya kasance amitacce, a kuma ki karbar hadisi daga mai karya mai rauni komai son sa da wilayarsa ga Ahlul Baiti (A.S), ba a karbar hadisi sai daga amintacce ko kuma akwai aminci da cewa ya zo daga manzo (S.A.W).

wannan kuma ya taka rawa muhimmiya wajan kare nassosi da kuma tantancesu, saobda haka ne ma duk abin da ya zo na hadisi ya zama yana iya kasancewa karkashin nakadi da tantancewa a sanadinsa da mantaninsa gaba daya.

Ba ma iya samun wani littafi daga littattafan hadisi da yake karbabbe sake-ba-kaidi gun jama’a saliha[6], sabanin sauran al’ummar musulmi da suka lizimci cewa akwai wasu littattafai da cewa ingantattu ne kai tsaye ba kebancewa, duk da cewa akwai masu ruwayoyi sanannu da karkatarciyar akida da karya a sanadin hadisan littattafan.

Kamar yadda a kwai hadisai masu yawa da littattafan hadisai masu yawa da ba su kawo su ba saboda kawai masu ruwaito su sun kasance sun karkata zuwa ga mazhabar da ta saba da tasu, sai al’amarin karbar hadisi ya zama al’amari da siyasa ta zama asasi kuma asali wajan karbar hadisi.

Rubutawa Da Kiyayewa

Na biyar: Himmantuwa da rubutawa da kiyaye wa ga hadisai da nassosi da ta haka ne wannan jama’a ta iya kiyaye da yawa daga hadisai masu yawa a maudu’ai masu yawa na shari’a da na rayuwa, haka nan a tafsiri da addu’a da wasiyya da hudubobi da tarihi, duk da yanayi mai wahala da suka fada a wannan lokuta daban-daban, da kuma karancin kayayyaki da dama, ta yadda abin da â€کya’yan jama’a ta gari suke mallaka na gadon musulunci ya fi yawa da fadi da gamewa daga dukkan abin da duk sauran jama’ar musulmi suke mallaka, al’amarin da ya saukake kiyaye shari’a da kuma tafarkin musulunci na asali mai nisanta daga dukkan son zuciya da karkacewa ko hidimar azzaluman mahukunta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next