Halayen Zamantakewa (A.S)Na biyu: Amfani da hankali da yake shiryarwa zuwa ga gaskiya da binta, daga ciki akwai ilimi da sani, a daya bangren kuma akwai jahilci da son rai, da fadawa karkashin tasirinsu. Saboda haka ne azaba da lada suka zama daidai gwargwadon hankali, da kwadaitarwa a kan shawara da hankali da rinjayar da bangaren hankali a kan janibin sha’awa a al’amuran da mutum yake fuskanta a rayuwarsa. Na uku: Tsoron Allah da kamewa da gyara kai yayin karkata zuwa ga sharri da sha’awa, da nisantar sabo da kuskure da zunubi, sannan da iyakance matsayin mutum da motsinsa wajan tarbiyyar rai, da kuma kiyaye karkatarta da kuma aiwatar da karfinsa a cikin iyakokin shari’a. Kuma samuwar alamomin cigaba ko tawaya na zatin mutum a rayuwarsa yana da alaka da wannan lizimtuwa ne. Na hudu: Hakuri wajan biyayya da lizimtuwa da wajibai, da hakuri kan barin sabo da nisantar haram, da kuma dauke nauyin takurar rai ta waje, da kuma rashin yi mata saranda, da rashin karbar don abin da take so –rashin ba ta dama-, da kuma cigaba a tafarkin biyayya da nisantar sabo da karfafa abin da zai kawo hakuri, da kuma karfafa nufi da iko a kan juriya da kuma fin karfin rai, da tasirantuwa ta hanyar karfin nufi. Na biyar: Yi wa rai hisabi da kuma lura da ayyukanta da take yi, da kuma kula da halaye, da ji a zuci, da sanin iyakacin yadda ya kai na dabbakuwa tsakanin aikinsa da abin da ya kudure na zuciyarsa, da shu’urinsa tare da huknce –hukncen shari’a da na kyawawan dabi’u din musulunci da siffofin kamala da kuma hadafi madaukaki da Allah madaukaki ya sanya ga mutum a tafiyarsa da motsinsa zuwa ga kamala. Na shida: Tuba da koma wa zuwa ga Allah yayin fita daga tafarki madaidaici da tafarkin daidaito da alaci da fadawa zunubi da sabo ko aikata zunubai, da kuma gaggauta komawa zuwa ga Allah ta hanyar jin nadama, da furuci da laifinsa da niyyar lizimtar ayyukan shari’a, da kuma mayar da abin da ya zalunci mutane na dukiya da na abin da ya tauye musu na daga cin hakkinsu. Na bakwai: Gano inda ake samun takurawar nan ta son rai, kamar son juciya da sha’awar mata, da tara â€کya’ya da dukiya na daga zinare da azurfa, da kuma dabi’u na rai na dan Adam kamar fushi da hassada da son shugabanci da girman kai da zato da kwadayi da kasala da kabilanci da nuna wariyar launin fata da â€کyan garanci da hamiyyar (ki ko so da aikin) jahiliyya, ko zalunci da ketare iyaka da cin hakkin wasu da sauransu, sannan kuma kokarin maganin wannan bayan an gano shi da fadakarwa a kan hakan. Na takwas: Samar da wani makari da kuma dauki-ba-dadi da zuciyarsa da kame kai, da kula da kowane mataki daga matakai da zai iya takawa domin kamalar dan Adam a tarbiyyar ransa, wannan kuma yana iya samuwa ta hanyar lizimtuwa da wajibai da ladubba da mustahabbai da makruhai, ta yadda zai iya saka wata katanga da kariya da zasu hana ransa fadawa tasirin son rai, ya kuma samar da karin kamala na dan Adam. Ana iya la’akari da cewa bayan wadannan tsarurrukan musulunci na gaba daya, a kwai tsarin yin addu’a da ambaton Allah da imamai (A.S) suka sanya, wanda ya hada da na rana da na dare, hade da himmantuwa da raya dare musamman darare na musamman kamar daren lailatul kadari, da na jumma’a, da idoji, da bukukuwan msuslucni (mauludin Annabi, da ranar aike, da idin gadir, da rabin watan sha’aban…dss), ko raya wasu ranaku na musmman kamar ranakun tara na farkon zulhajji, da ranakun tashrik, da idi biyu, da ranar gadir, da ranar mauludi, da ranar aike, da ranar ashura, da sauransu. Haka nan tsarin salloli mustahabbai na musamman da ake danganta su zuwa ga ma’asumai sha hudu daya bayan daya, da sallar Ja’afar, da makamantansu, ko salloli na gaba daya na raya darare, da dararen Ramadan, da kuma bukukuwan musulunci. Da tsarin wasu ibadoji kamar mustahabbai da ittikafi da hajjin mustahabbi, da umra, da ziyarar Annabi (S.A.W) da imamai (A.S) da salihai daga bayin Allah, da zikirori, da kuma ciyarwa a tafarkin Allah, da sadar da zumuncin makwabta da muminai, har ma da sadar da zumuncin dukkan musulmi. Dukkan wannan akwai bayaninsa dalla-dalla da za a iya gani a littattafan hadisai, kamar babin tarbiyyar rai da zamantakewa, da â€کyan’uwantaka, da kuma aiki kyakkyawa, ta yadda sakamakon zai zama shi ne samun daukaka zuwa ga kyawawan dabi’u da lizimta da kuma da karfi da dagewa a matsayin dan Adam na daidaiku da zamantakewar al’umma na gaba daya, Wadanda da sannu zamu yi bayaninsu in Allah ya so a bahasin tsarin alamomi da ibadoji. |
back | 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 |