Halayen Zamantakewa (A.S)



Fasali Na Biyu: Siffofin Jama’a Saliha

Ba makawa cewa hadafi gama-gari yana bayyana a bisa siffofi da ake nema ga wannan jama’a, kamar yadda hadafi da siffofi suke bayyana a bayani dalla-dalla nabin da ake nema ga wannan jama’a ta gari.

Wannan shi ne abin da yake fassara mana samuwar daaidaito da kamantuwa tsakanin wasu bayanai guda uku tare da sabani a bayani dalla-dalla ko a dunkule.

Ba makawa bayan bayanin sashen hadafofi na gama-gari da suke karkashin gina jama’a ta gari mu bijiro da wasu siffoi na asasi da ba makawa ga wannan jama’a ta gari ta siffantu da su domin tsayuwa da aikinta, da kuma bayar da wannan aiki muhimmi na imamai (A.S) wajan kare musulunci da kiyaye al’ummar musulmi da zamantakewarta.

Hakika mun yi bayanin wasu daga wadannan siffofi yayin da muke bayanin hadafi na asasi da yake karkashin samar da wannan jama’a ta gari, kuma muna kokarin mu takaita jerin wadannan siffofi da aka riga aka yi nuni zuwa garesu wajan bijiro da wadannan hadafofi, da makamantansu na daga siffofi.

1- Akida Ta Gari

Hakika Ahlul Baiti (A.S) sun himmantu da gina akidar wannan jama’a da kuma kiyaye alamomin wannan akida ta musulunci ta asali, ta yadda ta kasance nesa daga dukkan tasirin wani tunani ko siyasa ko zamantakewa da al’umma ta kasance tana fusknata a wadancan karnoni da suka gabata farkon musulunci, kamar akidar Rumawa da Farisawa da Yunan wadanda suka jagoranci jama’a zuwa zindikanci da musun Allah da akidar hululi.

Haka nan ta zama kubutacciya daga cutar mayen nan na zamani da ya samu al’ummar musulmi saboda haduwarta da sababbin al’ummu a duniyar musulunci, da kuma arziki mai yawa da salon rayuwa na holewa da jin dadi da sha’awece-sha’awece.

Kuma ta nisanta daga abin da yakan kai ya kawo na rai da ruhi da wasu jama’a suka tashi suka aikata shi na bujirewa rayuwa da kuma takure rai, kamar yadda ake iya gani a wasu sashen mazhabobi na sufanci da badiniyya. Ko kuma fada wa cikin bala’in tashin hankali da tawaye a kan al’ummar musulmi da tsarin musulunci ta yadda za a wurgar da dukkan abin da yake wajibi a ajiye shi gefe guda, a yi hukunci da kuskure da bata ga dukkan zahirin rayuwa da kuma yanayin da ake ciki kamar yadda muka gani a harkar khawarijawa ko kuma karamida da makamantansu. Ko kuma makahon bangaranci da shisshigi da wuce gona da iri kamar yadda muke iya gani a mazhabar gullat da nasibawa da kidiriyya da mufawwada.

Ta haka ne imamai (A.S) suka iya kare mususlunci na gari a kan ma’aunai da akida mai kyau ga mabiyansu ta yadda suka kare musulunci sahihi da asalin akida ta wannan jama’a, suka kuma tanadar musu ikon cigaba da zamantakewa da rayuwa cikin nishadi da harka da tasiri a kan wasu ta wani bangare.

Saboda haka yayin da muka so mu kiyaye tsarin bayani na harkar wannan al’umma da tafarkinta a tsawon tarihin musulunci sai mu sami cewa wannan al’amari tun farko yana da ginshiki ta wani bangare, da yalwa da yaduwa ta wani bangare, da kuma kafewa da cijewa ta wani bangaren na uku, duk da cewa aikin kamewa da kunkumewa da kokarin kisa da kawar wa daga doron kasa da wannan jama’a ta fuskanta ba tare da ta nemi dogaro da yakin sari-ka-noke ba ko kuma gudu daga zamanatakewar al’umma ko karkata zuwa ga garuruwa da suke boyayyu. Sai dai ta wanzu ne tana rayuwa a cibiyar musulunci da daukakar ilimi da addini da wayewar duniyar musulunci kamar: Iran, Iraki da Turkiyya da Labanon da Suriya da khalij da yankin Indiyawa da Pakistan, da Asiya ta tsakiya, da Afganistan, da Azarbaijan, da Sashen yankunan Afrika masu muhimmanci kamar yadda ta hada al’ummu da jama’a daban-daban kamar: Larabawa, Farisawa, Turkawa, Kurdawa, da Indiyawa da Dukkan jama’unsu, da Barbar, balle daga Afrika bakake da makamantasnsu na daga al’ummu da aka sani.

Ta yiwu imamai (A.S) sun kasance suna ganin cewa babi wata bukata mai karfi ga mabiyansu da tafi sama da wannan kira da aiki na isar da sako a cikin musulmi, domin Akida ta gari da kanta zata iya yiwuwa ta taka wannan rawar da zarar an jefa ta cikin al’umma.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next