Halayen Zamantakewa (A.S)



Sai dai bayyanannen abu shi ne, duk da dukkan musulmi sun yi imani da samuwar wannan jama’a ta gari da ta bambanta da sauran musulmi a daidai gwargwadon tunaninsu da kuma jin daukar nauyin da wannna akida take tare da shi da lizimtuwa da shi a bayani dalla-dalla. Saboda haka imam mahadi a gunsu ba kawai mujarradin wani abu ne na tarihi da zai faru ba a nan gaba da mutum yake tunanin hankoron ganinsa, sai dai shi samamme ne rayayye da yake rayuwa kamar sauran musulmi, yake kuma ganin zogin da wadannan musulmi suke fama da shi da matsalolin zamantakewar danAdam, kuma yana sauraron dukkan muminai a wannan ranar da aka yi alkawarinta, shi fakakke ne gabarin ganin idanu sai dai shi yana ganin dukkan al’amura da yanayi da al’ummar yanzu suke rayuwa a kai.

2- Daukar Nauyi Da NemanCanji

Share fagen da wannan jama’a saliha zata aiwatar ba kawai mujarradin nazari ba ne ko lizimtuwa ta akida kamar yadda muke gani ga dukkan musulmi, har ma da wajan ma’abota wasu addinai, duk da akwai sabani a kan hakan tsakanin wadancan addinai da sauran musulmi, kamar yadda ba kawai hali na rai da kumaji ba ne, duk da kowanne daga wadannan abubuwa biyu yana da muhimmancinsa a share fagen.

Sai dai share fage wani motsi ne na siyasa ta jihadi a cikin al’umma da ta bambanta da jin nauyi da ya hau kanta a game da abin da yake gudana na al’amura, tana kuma da niyyar aiki wajan tabbatar da wannan hadafi, a lokaci guda tana aiki domin hana sallamawarta a gaban azzalumai ko takurawa ta akidar da take gaba da ita a tsawon zamuna.

3- Komawa Zuwa Ga Musulunci

Gudummuwa ta a zo a gani game da bayyanar imam mahadi (A.S) da kuma cin nasararta wajan fuskantar akidu masu musun samuwar Allah da ko in kula da addini wacce ta ke mamaye da wuyan duniyar yammanci a yau, wannan abu ne wanda nan gaba zata yaye shi kamar yadda zamu yi nuni zuwa ga nassosi masu karfafawa ga hakan. Sai dai a matsayin yau zai iya yiwuwa mu yi bayani game da rawa da wannan jama’a ta gari zata taka wajan dawowa zuwa ga musulunci a rayuwar al’umma da siyasa da akida bayan kokari da ta saba yi, ko kuma nisantar da shi da rayuwa musamman a wannan zamani[10].

Da wannan dan bayani na hadafin gina jama’a ta gari, zai iya yiwuwa mu ce: Hakikanin hadafi shi ne gudummuwar imamai (A.S) wajan tabbatar da hadafin ta hanyar samuwarsu da kuma taimakawarsu ta wani janibi, ta wani bangaren kuma wanzar da sako da muhimmin aikin imamai a al’ummar musulmi ta hanyar jama’a ta gari, bayan samuwar buya babba na imam mahdi (A.S).

saboda haka ya zama dole a samu wannan jama’a ta gari da tsari mai manufa, samuwarta ba kawai ya zamo domin al’amarin shiryar da mutane da tsayar da hujja akansu ba ne, duk da wannan yana da nasa tarsiri mai girma wajan samar da jama’a a gari wacce take imani da wilaya ta imamai goma sha biyu da matsayinsu a al’ummar musulmi.

Ta yiwu nassi mai zuwa da Kulaini ya rawaito shi a littafin Kafi daga imam Abu Ja’afar Aljawad (A.S) daga iyayensa daga Amirul muminin daga manzon Allah (S.A.W) ya zama Karin haske a kan hadafin gina jama’a ta gari, wacce wannan manzo (S.A.W) ya yi magana game da ita:

“Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Allah ya halicci musulunci sai ya sanya masa farfajiya ya kuma sanya masa haske ya kuma sanya masa Katanga ya sanya masa mai taimako; amma farfajiyarsa ita ce kur’ani, amma haskensa shi ne hikima, amma katangarsa ita ce horo da kyakkyawa, amma mataimakansa ni ne da Ahlul Baiti nawa da kuma shi’armu, ku so Ahlin gidana, da shi’arsu masu taimakonsu, ku sani yayin da aka yi isra’i da ni zuwa saman duniya sai Jibirilu ya danganta ni (ya yi bayanina) ga mutanen sama, Allah ya sanya so na da son Ahlin gidana da son shi’armu a zukatan mala’iku, wannan ajiya ce amana a wajansu har ranar alkiyama, sannan sai ya sauka da ni zuwa mutanen duniya ya yi bayanina ga mutanen kasa ya sanya amanar sona da son Ahlin gidana da son shi’armu a zukatan muminai na al’ummata, muminan al’ummata sune suke kiyaye wannan amana game da Ahlin gidana zuwa ranar alkiyama, ku sani da wani mutum daga al’ummata ya bauta wa Allah tsawon rayuwata ta duniya sannan ya gamu da Allah yana mai kin Ahlin gidana da shi’ata da Allah bai samu wani abu a kirjinsa (zuciyarsa) ba sai munafinciâ€‌.

FASALI NA BIYU

Siffofi Gama-Gari Na Jama’a Saliha



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next