Halayen Zamantakewa (A.S)



Ya yadda ya zo a cikin nassosi masu yawa da suke kwadaitarwa a kan bin hanyar cinikayya da noma, hakika ya zo cewa kashi tara cikin goma na arziki yana cikin noma. Wannan kuma wani abu ne da zamu bincike shi a tsarin tattalin arziki.

Mika Soyayya Ga Muminai

Siffantuwa da ruhin yi wa juna adalci da taimakekeniya da kuma lamuni da taimako juna ga â€کyan’uwa muminai da wannan yake nuna kulla soyayyar mumini ga mumini, wannan shi ne ka’ida mai karfi da alakar tsakanin al’umma take tsayuwa a kai, da tabbatar da hadin kai, da cakuduwa da juna, da maganin rauni da abubuwan da sukan samu daidaiku saboda yanayi na zamantakewa, da tattalin arziki da siyasa, da kuma jin kadaitaka, da taskacewa, da rauni.

Hakika ya zo daga Ahlul Baiti (A.S) ruwayoyi masu yawa da suke karfafa siffatuwa da wannan, da kuma cewa wannan hakki ne daga hakkokin mumini a kan dan’uwansa a tsakaninsu, kamar yadda ya rigaya mun yi nuni zuwa ga hakan.

Wannan shi ne abin da da sannau zamu yi bincike kansa a tsairn tattalin arziki da kuma tsarin zamantakewa na jama’a.

Daga cikin wadannan nassosi; daga Abu Ja’afar (A.S): “Hakika daga hakkin mumini a kan dan’uwansa mumini ya kosar da yunwarsa ya tufatar da al’aurarsa ya yaye masa bakin cikinsa ya kuma biya masa bashinsa, idan ya mutu ya maye gurbinsa a ahlinsa da â€کya’yansaâ€‌[45].

 

Jin Daukar Nauyin  Hidima Ga Al’umma

Jin daukar nauyin al’umma da kuma jurewa ga hidima ga al’ummar musulmi gaba daya, wannan kuwa ta hanyar karfafawar imamai na Ahlul Baiti (A.S) ga asasin horo da kyakkyawa da hani ga mummuna da jihadi a tafarkin Allah domin dauki-ba-dadi da zalunci da shisshigi da karkata, da kuma asasin taimakekeniya ga musulmi, haka nan taimakekeniya tsakaninsu, da himmantuwa da al’amuransu, da nasiha garesu, da â€کyan’uwantaka tsakaninsu, da haramcin jininsu da dukiyoyinsu da mutumcinsu, da kuma rayuwa tare da musulmi, da makamancin wannann na daga asasai da suka hadu gabadayansu a kan ka’ida mai karfi da tsari cikakke na wannan jin nauyi da ya hau kansu, wanda da sannu zamu yi bayani ga dukkan wadannan abubuwa dalla-dalla a bahasosi masu zuwa.

 

Ka’idoji Da Dokoki

Shimfida

Yayin da imamai (A.S) suka fara gina jama’a ta gari sun sanya wasu tattararrun dokoki masu karfi don gina karfafa wannan gini akansu, mun riga mun gama bayanin wadannan dokoki da asasai na sakon addini na karshe da yake misaltuwa cikin fahimta ta gari na sakon, da kuma neman cimma wadannan hadafofi da muka ambata ta wani bangare.

Saboda haka muka samu cewa wadannan dokoki da suka siffantu da gamewa da asasi, da karfi, da dacewa, sun kasance cakude ne na dukkanin samuwa da ta cika dukkan abubuwan da ake bukata na gini mai karfi da zai iya kaiwa ga aiwatar da al’amari mai girma na kiyaye musulunci da al’umar musulmi da kuma kariya garesu ta wani bangare, da kuma samar da misali na gari na jama’a ta gari na mutuntaka a tarihin dan Adam. Wannan ka’idoji da asasai suna misaltuwa cikin Akida da Kyawawan dabi’u a Sakafa da Gina ruhi da kuma Dokokin siyasa.

Don haka ne zai zama a gabanmu akwai fasaloli biyar don wannan bincike a wannan babi da, da sannu zamu yi binciken kowanne daga wadannan fasalolin daya bayan daya, da nuni cikin magana takaitacciya wanda dasannu zamu bayyana sashen bayanai dalla-dalla game da ita ta hanyar kashi na biyu yayin da zamu yi bincike game da gini na sama na jama’a ta gari.

Duk da sanin cewa kowane daya daga cikinsu yana da cancantar bincike na musamman game da shi ta bangaren al’ada da tarihi da bayani filla-filla.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next