Hijabi Lullubin MusulunciHakika za a iya fahimtar yanayin yadda ake tafiyar da mace a kasashen Turai, wadanda suke ikirarin cewa su ne ma'abuta 'yanci da adalci, daga Taron Duniya Kan Mata da Kafafen Watsa Labarai da aka gudanar a birnin Athens na kasar Girka ran 20 ga watan Nuwamban shekaran 1985. A wannan taro, daya daga cikin mahalalta taron mai suna, Petra Kelly 'yar majalisar kasar Jamus, ta yi kukan cewa: " A kasar Jamus, suna tafiyar da mu (matayen Jamus) kamar 'yan tsiraru, wadanda ba su da amfani, musakan cikin al'umma kamar yara. Suna amfani da mu wajen tallen kayayyakinsu kuma suka dauka cewa zaluntarmu ba laifi ba ne. A duk cikin mintuna 15 sai an yi fyade wa wata mace." Daga baya wannan taro, ya yi kira ga majalisar kasar Girka da ta kafa dokar da ta haramta amfani da mata a talibijin don biyan wata bukata. Ko da yake an tabbatar da ana wulakanta mata a wadannan kasashe, to amma su ma matayen wadannan kasashe da suke ikirarin ci gaba su ne abin zargi. Don kuwa idan mata ba su yarda ba, to da ba a yi amfani da su wajen buga littattafa da finafinan jima'i da kuma tallace - tallace da su tsirara ba. Wannan kididdiga mai zuwa za ta nuna mana irin yadda wannan al'amari na rugujewar iyali ya zamanto a al'ummomin da ba na Musulunci ba: A Kasar Faransa: Daya daga cikin aurarraki hudu yana karewa ne ta hanyar shika; a birane ma adadin ya fi haka yana kai wa kashi 50 cikin dari. A kowace shekara kimanin masoya 600,000 ne suke yin aure, 100,000 kuma suke zaban su zauna tare ba tare da aure ba, kana a kan sami rabuwar aure guda 100,000. A Kasar Kanada Kusan kashi 40 cikin dari na aurarrakin fari, sukan kare ne ta hanyar shika. Sannan a tsakanin shekarun 1972 zuwa 1982, an sami ninkuwan wannan adadi har sau biyu. A Tsohuwar Tarayyar Sobiyet; Kimanin kashi 70 cikin dari na aurarraki sukan lalace ne cikin shekaru goma, dalilan da ke jawo hakan kuwa sun hada da shaye-shaye, rashin kudi da kuma rashin wadatuwa da juna da sirri. A Kasashen Amirka ta Tsakiya da ta Kudu: Wata jaridar kungiyar UNESCO ta Majalisar Din-kin Duniya tana cewa sau da dama ana samun 'ya'yaye masu iyaye guda (wadanda suka tashi karka-shin kulawan uwa kawai ko kuma uba kawai) ne ta hanyar irin hijirar da mataye suke yi zuwa birane da kuma samar da 'ya'yaye a aurarrakin da ba jimawa suke yi ba. A dalilan shaye-shaye da kuma gazawar miji wajen samun takamammen aiki, yakan haifar da watsewar iyali da kuma barin uwaye da 'ya'yayensu cikin tsananin talauci da wahalhalu. A duk duniya kasashen da suka fi adadin shegun 'ya'ya su ne kasashen Karebiya, Tsakiya da kuma Kudancin Amirka. Kasar Sin (China): Ko da yake adadin shika a kasar Sin yana da karanci a kan da dama daga kasashen Turai, to amma a cikin shekaru biyar, an sami hauhawansa da kashi 70 cikin dari. Mujallar Peiking Review ta kawo rahoton cewa ana samun hauhawar adadin shika a kasar . Kasar Amirka: Kimanin rabin adadin aurarrakin da aka yi suna karewa ne ta hanyar shika. Don haka ne ma kashi 60 cikin dari na yaran da aka haifa suna tafiyar da bangaren yarintarsu ne a wajen uwa ko ubansu.
|