Hijabi Lullubin MusulunciKana ana biyun kuma ba a kula da mu'amaloli tsakanin samari da 'yan mata kamar yadda Musulunci ya tanada. Shin me ku ke tsammanin zai faru dangane da gudanar da aiki a kowane daya daga cikin wadannan misalai? Shin za a iya bayyana daki na biyu a matsayin wurin da ya dace da karatu? A takaice dai, ashe bai fito fili cewa hijabin Musulunci, duk da irin yanayinsa, bai kasance abin barazana ga 'yancin mace ko aiki ko kuma sauran mu'amaloli na rayuwa ba. Lalle gaskiya ne (hijabi mummunan abu ne) idan mutum ya yi la'akari da irin hijabin (kulle) da ake yi a kasar Indiya, Iran, Masar da sauransu a lokacin jahiliyya, inda suke kulle mata a cikin gida. Hakika dole ne mace ta ji cewa an take mata hakkinta da kuma katsalandan cikin ayyukanta, wanda abin da hakan zai haifar shi ne ruguje rabin al'umma ko ma fiye. Lalle wannan al'amari ne da ya kamata mu yi dubi cikinsa dangane da irin mummunan yanayin da irin wannan hijabin da ke kange mata daga duk wani irin aiki na ci gaban al'umma yake haifarwa. Musulunci ya yi Allah wadai da irin wannan hijabi na jahiliyya, inda ya sauya shi da wani lullubin wanda ke cike da tsarkake mu'amala karkashin sunan hijabi. Kamar yadda muka bayyana, akwai bambance-bambance masu girman gaske tsakanin wadannan nau'o'i guda biyu na hijabi. Hakika yadda masu ikirarin ci gaba suke daukan hijabi ya saba wa asalin al'amarin. Al'ummar da lalata ta yi kanta a cikinta, hakan shi ne babban dalilin rashin ci gabanta, saboda abubuwa da kuma karfin da take da su suna tafiya ne wajen al'amurran zinace-zinace, neman mata da almubazzaranci, sabanin al'ummar da tsarkakakkiyar mu'amala take gudana tsakanin mata da maza. Kana dangane da tunaninsu kan danne wa mata 'yancinsu karkashin inuwar sanya tufafi da kuma tsarkaka wanda hijabin Musulunci ya zo da shi, lalle abin da suke nufi da 'yanci a nan shi ne 'yancin zinace-zinace da duk wasu bangarorinsa wanda ake yadawa a kowane lungu da kuma yanayi. To amma dangane da sauran 'yancocin kuwa ko ma tunaninsu ma ba sa yi. A takaice dai, hijabi, a mahangar Musulunci, ba shi da wani mummunan tunani dangane da 'yancin mace ko kuma duk wani aiki nata da kuma musharakanta cikin al'amurran yau da kullum. Face ma dai hijabin Musulunci ya tabbatar da 'yancin mata ne da kuma mutuncinsu, bugu da kari kan irin babbar gudummawar da ya bayar wajen tabbatar da 'yancin mata da kuma musharakansu cikin ayyukan ci gaban al'umma. Sama da haka ma, hijabin Musulunci a ainihinsa, yana ba wa mace mutuncinta ne da kuma daukaka matsayinta a cikin al'umma. Don kuwa mutane sukan yi mu'amala da duk macen da take sa tufafi irin na Musulunci (hijabi) ta bangaren cewa ita cikakkiyar 'yar'Adam ce. Kana ita kuwa macen da ba ta kula da hijabi, ita ma jama'a suna mu'amala da ita ne a matsayin 'yar'Adam, amma saboda abin da take da shi a matsayinta ta mace da kuma jikinta da take barinsa a waje don dadinsu. Don haka, hijabin Musulunci zai ci gaba da zama wani makami na yakan bakin ciki, damuwa da wulakanci. Yana da kyau a nan a gane cewa duk da irin muhimmancin da Musulunci ya bayar wajen mace ta rufe jikinta gaba ga mazajen da ba muharramanta; yana kuma kiranta da ta kula da kanta da jikinta (wajen yin ado) a cikin gidanta, don kawata matsayin da take da shi na mace wanda Allah Madaukakin Sarki Ya arzurta ta da shi, kuma don biyan bukatunta wadanda shari'ar Musulunci ta halalta mata. Duk da cewa an hana mace nuna jiki da adonta ga sauran mutane, to amma an kwadaita mata cewa ta gyara jikinta da kuma yin ado wa mijinta. Hakika ma ana yabonta a duk lokacin da ta kawata kanta domin mijinta da kuma jin dadi tare da shi. Wani abin da ya kamata a ambata a nan shi ne cewa macen da take kula da shiga irin ta Musulunci (hijabi) baya ga irin girmamawa da mutuntawar da take samu daga wajen jama'a da kuma iyalanta, tana kuma dadadawa Ubangiji Mahaliccinta rai ne kana tana samun lada daga wajenSa saboda biyayyar da ta yi wa umurninSa. Hakika wannan babban nasara ce gare ta, don kuwa tana biyayya ne ga Alkur'ani mai girma da kuma hadisan AnnabinSa (s.a.w.a); kana tana kare al'umma ne daga munanan ayyuka da lalata. Tana mai kawar da munanan tunanunnuka da ayyuka; tana mai daga yanayin aiki da samar da abubuwan bukata da kuma kawo tsarki da daukaka ga al'umma. Duk ta sami damar gudanar da hakan ne kuwa ta hanyar amfani da hijabin Musulunci. Lalle irin albarkatun da za ta samu kan wannan babban aiki, ba zai iya lissaftuwa ba. Shakka babu, a duk lokacin da mace ta kiyaye zakin muryarta, yanayin motsin jikinta, yanayin dabi'unta da kuma sirrin kanta daga wadanda ba su da 'yancin amfanuwa da su a shar'ance, to hakan taimakon al'umma ne. Wannan babban aiki da ta dauka yana haifar da kwanciyar hankali da sauki ga sauran halittu 'yan-'uwanta, don ta haka ne za mu iya fahimtar dalilin da ya sa Musulunci ya sanya irin wannan muhimmanci a gare ta cikin sauki. Don ita ce kashin bayan al'umma kuma asasin ci gaban mutum a matsayinsa na dan-'Adam. A saboda haka ne a duk lokacin da ta lalace, to za ta lalata dukkan al'umma ne.
|