Hijabi Lullubin Musulunci



" Ya ku wadanda suka yi imani ! ba ya halalta a gare ku, ku gaji mata a kan tilas. Kuma kada ku hana su aure domin ku tafi da sashen abin da kuka

ba su...."(Surar Nisa'i: 4:19 Sannan kuma ya yaye musu irin zalunci da wulakanta su da mazaje suke yi.

Don haka ne ma Alkur'ani ya ba da muhimmanci mai girman gaske kan tausaya musu yayin mu'amala da su: " …Kuma ku yi zamantakewa da su da alheri. Sa'an nan idan kun ki su, to, akwai tsammanin ku ki wani abu, alhali kuwa Allah Ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa."(Surar Nisa'i: 4:19) Koda yake a da, talauci ma ya kan sa mutane su kashe 'ya'yayensu musamma ma 'ya'yaye mata, don haka Alkur'ani ya kawar da wannan al'amari (daga kanta: (Kuma kada ku kashe diyanku saboda talauci, Mu ne Mu ke arzurta ku da su..."(Surar An'ami: 6:151) Kana kuma Musulunci ya bayyana cewa ma'aunin daukaka ba wai ya dogara kan mazantaka ba ne face kan imani (da Allah) da ayyuka na kwarai. Duk wanda ya aikata wani aiki to zai sami sakamakonsa, shi namiji ne ko mace": Lalle, Musulmi maza da Musulmi mata da Muminai maza da Muminai mata, da masu tawali'u maza da masu tawali'u mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu hakuri maza da masu hakuri mata, da masu tsoron Allah maza da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata, da masu tsare farjojinsu maza da masu tsare farjojinsu mata, da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambatonSa da yawa mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma." (Surar Ahazabi: 33:35) Kana Musulunci ya ci gaba da nuna cewa muminai sashensu majibincin sashe ne. Sun kasance masu yada alheri a tsakaninsu kana suna umurni da abu mai kyau, sannan suna hani da munana: " Kuma Muminai maza da Muminai mata, sashensu majibincin sashe ne, suna umurni da alheri kuma suna hani daga abin da ba a so, kuma suna tsayar da salla kuma suna bayar da zakka, kuma suna da'a ga Allah da ManzonSa. Wadannan Allah Zai yi musu rahama….." ( Surar Tauba: 9:71) Hakika Musulunci ya tsaya wajen bayyana irin yanayin mu'amalar da ke tsakanin mace da namiji ta hanyar aure: " Su tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su…." (Surar Bakara: 2: 187)

" Kuma akwai daga ayoyinSa, Ya halitta mu ku matan aure daga kanku, domin ku nitsu zuwa gare su, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku..." (Surar Rumi: 30:21) Baya ga tsara dokoki kan hakkokin da 'yancin mace, hakika Alkur'ani mai girma ya mai da hankali kan wajibcin girmamawa da kuma kulawa gare ta, kana da kuma bata cikakkun hakkoki da 'yancinta.

Manzon Allah, Muhammad (s.a.w.a ) yana cewa: "Babu wadanda za su girmama mata, face masu mutunci, kana babu wadanda za su cutar da su face marasa mutunci[2]. "Kada ku nuna bambanci wajen kyauta a tsakanin 'ya'yayenku, hakika da za a ba ni zabi wajen taimako, lalle da na zabi mata ( don taimaka musu)[3]."Ba na tsammanin mutum zai samu karuwa a imaninsa, ba tare da kaunar mata sosai ba[4].

Sannan bugu da kari, akwai tsarkakan nassosi masu yawan gaske da suke kira ba a tabbatar da mace a kan matsayin da take da shi a cikin al'umma. Kana kuma Musulunci ya ba da wasu muhimman abubuwa ga mace. Ya tsara mata sutura ta musamman don tabbatar da daukakarta da kuma kare mata mutuncinta daga lalacewa da rugujewa. Don haka ana iya cewa ta hanyar hijabi

(Lullubin Musulunci), Musulunci ya sami cim ma manyan manufofi guda biyu: Na farko, ya kare mata akidarta, yayin da take aikata abubuwan da suka hau kanta na wajen ba da gudummawarta ga al'umma, ci gaba da kuma Sakon Musulunci da kuma gudanar da al'amurran da suka shafi rayuwarta gwargwadon yadda Musulunci ya tsara.

Na biyu, yana kare tsarkakan mace da kuma toshe duk wata hanya da za ta kai ga aikata duk wani aiki da zai kai ta ga fadawa ga munanan ayyuka; ko kuma ya juya ta ta zama wani makami da ke lalata al'ummar da take rayuwa a cikinta -kamar yadda yake faruwa a kasashen Turai -. Baya ga irin nasarar da hijabi ya samu wajen kare mace da kuma tsara mata irin suturar da za ta

sa da kuma haramcin da Musulunci ya yi na cakuduwan (mata) da wadanda ba muharramansu ba, da dai sauran ka'idoji, za mu ga irin matukar kokarin da Musulunci ya yi wajen kare namiji da mace, da kuma dukkan al'umma, daga yaduwar munanan ayyuka da kuma rayuwar da ba ta da amfani.

angane da wadannan ka'idoji da dokoki, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: Dangane da wadannan ka'idoji da dokoki, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: Ka ce wa Muminai maza da su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa. Kuma ka ce da Muminai mata da su kawar da idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu, kada kuma su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi, kuma su dora mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna kawarsu face ga mazajensu ko ubanninsu, ko ubannin mazajensu, ko diyansu, ko diyan mazansu ko 'yan'uwansu, ko diyan 'yan-'uwansu mata ko matansu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya wasun masu bukatar mata daga maza, ko jarirai wadanda ba su tsinkaya a kan al'aurar mata. Kuma kada su yi duka da kafafunsu, domin a san abin da suke boyewa daga kawarsu. Kuma ku tuba



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next