Hijabi Lullubin MusulunciKana kuma Nusaiba tare da danta da ya saura, Amarah, sun halarci yakin Uhudu. Yayin wannan yakin, lokacin da musulmai suka tarwatse, sai ta dauki jakan ruwanta tana bi tana shayar da masu jin kishirwa da kuma taimakon wadanda aka raunana ta hanyar magunguna da take da su. An ruwaito ta tana cewa: "Lokacin ana tsakiyar yakin, sai na ga dana yana gudu, sai na tsai da shi na ce masa: Ya dana! Ina za ka? Shin daga wa kake gudu? Daga Allah ko daga ManzonSa?". Nan take ta komar da shi, kana ta tsaya tana kallo daga nesa. Daga nan ne ta ga makiya sun kewaye Manzon Allah (s.a.w.a.), nan da nan ita da wannan da nata suka nufi inda Annabi (s.a.w.a.) yake don kai masa agaji. A nan ne daya daga cikin kafirai ya kashe wannan da nata, ita kuma Nusaiba sai ta dauki takobin dan nata, da taimakon Allah ta kashe wanda ya kashe mata da. Ko da ganin haka, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce mata: "An gaishe ki, Ya Nusaiba, Allah Ya yi miki albarka". A wannan yaki ne wannan jarumar mace ta sami raununnuka har guda goma sha uku, daya daga cikinsu saran takobi ne a wuyanta, sannan kuma ta rasa hannunta guda a yakin Yamama. An ruwaito cewa wannan mace mai tsananin sadaukarwa za ta dawo lokacin Imami na karshe, Imam Mahdi (a.s.) a matsayin likita (wacce za ta taimaka masa). Sayyida Zainab (a.s.), wannan jarumar 'ya ta Imam Ali (a.s.), ita ma ta kaddamar da muhimmiyar gudummawa lokacin da ta dauki nauyin isar da sakon dan'uwanta Imam Husaini (a.s.) bayan shahadarsa a Karbala a hannun azzaluman sarakunan Umayyawa, karkashin ja-gorancin Yazid bin Mu'awiyya. Ta dauki nauyin yin bayani da kuma isar da dalili da manufar wannan babban yunkuri na Imam Husaini (a.s.) a duk guri ko kuma taron da ta halarta. Kana ta tona asiran azzalumai a garuruwan Kufa, Damaskas da Madina. Sannan kuma ta dauki nauyin kare fursu-nonin gidan Manzon Allah (s.a.w.a.), wadanta suka hada da mata da kananan yara, tare da yankakken kan Imam Husaini (a.s.) daga sahara mai zafin gasken nan ta Karbala zuwa birinin Damaskas. Hakika tarihi ya rusunar da kai cikin kunya gaba ga wannan madaukakiyar mace wacce Musulunci da raunana ke gode mata, saboda irin sadaukarwar da ta yi, da kuma irin juriya, hakuri da kuma gudumma-warta ga tafarkin gaskiya. Cikin jarunta ta fuskanci azzalumai kana ta tona munanan ayyuka da tsarur-rukansu. Ta bayyanar da sakon gwagwarmaya, daukaka, mutunci da gaskiya a dukkan garuruwa. Jawabanta a fadojin wadanda suka kamo ta, suna cike da hikima da motsa rai. Lalle ta shahara ta wajen fuskantar Yazid da ta yi a fadarsa da ke Damaskas. Ta fuskance su gaba dayansu kana ta zarge su kan abubuwan da suka aikata ba tare da tsoron mutuwa ko gallazawa, wanda ya zamanto ruwan dare ga makiyan wancan hukuma. Haka ta ci gaba har karshen rayuwarta wajen tona asirin zalunci da azzalumai da kuma isar da sakon dan'uwanta (a.s.). Ta kasance mai fada da zalunci, kana ta mallaki tsarkakakkiyar dabi'a da jaruntaka a duk tsawon rayuwarta. Tana daga cikin madaukakan mutane a duk inda ta kasance. Ta ci gaba da gwa-gwarmayar Imam Husaini (a.s.) da kuma taimakon al'umma wajen fahimtar abin da ya hau kansu na yakan zalunci da babakere. Idan har muna son mu yi bincike cikin shafuffukan tarihin Musulunci, babu yadda za a yi mu mance da ayyukan Hamida, matar Imam Ja'afar Sadik (a.s.) kuma mahaifiyar Imam Musa Kazim (a.s.). Ta kasance tana kula da mabukata da marasa galihu na birnin Madina, a bisa umurnin Imam Sadik (a.s.). Inda take rarraba kudi ga fakirai da kuma ziyarar marasa galihu, don taimaka musu da abubuwan da suke bukata. Misalin wata matar kuma mai tsoron Allah wacce ta ba da muhimmiyar gudummawa a tarihin Musulunci, ita ce Salil, mahaifiyar Imam Hasan bin Ali al-Askari (a.s.). ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen kare gaskiya da kuma kulawa da shiriyar Ubangiji. Wannan mace mai daukaka ta kasance a matsayin mai sadarwa tsakanin Imaman nan guda biyu, wato: Imam Aliyu al-Hadi da Hasan Askari (a.s.), da sansanin muminai mabiyansu lokacin da wadannan Imamai suka shiga halin tsanantawa daga wajen azzaluman zamaninsu. Ita take isar da sako da umur-nonin wadannan Imamai ga muminai mabiyansu, kana ta isar da tambayoyi da sakonninsu da kuma halin da suke ciki ga wadannan Imamai (a.s.). Yana da muhimmanci mu fahimci cewa kasancewar mata a cikin al'amurran siyasa yana da matukar muhimmanci. Domin kuwa, a wasu lokuta, mataye sukan dauki rabin adadin al'ummar kowace kasa, kuma su kan iya canza alkiblar al'umma zuwa ga alheri ko sharri gwargwadon irin wayewarsu ta siyasa da kuma musharakarsu. Hakika hijabi ba ya hana irin wannan gudummawa kamar yadda bai hana kowacce daga cikin wadannan mataye da muka ambata a baya ba. A wannan zamani namu za mu ga misalin irin wannan wayewa da kasancewa a lokacin gwagwar-mayar Musulunci a kasar Iran. Inda mata duk da cewa ga jarirai a hannayensu kana ga kananan yara a gefensu, amma haka suke fitowa kan tituna don nuna rashin amincewarsu ga gwamnatin zalunci ta Sarki Shah, sanna kuma ga 'yan sanda suna karkashe su. A sakamakon haka da dama daga cikin wadannan iyaye mata da 'ya'yayensu suka yi shahada yayin zanga-zangogin da suka dinga yi. A lokacin da sakon gaskiya ya bayyana kana aka sake rayar da sautin gwagwarmaya a karni na ashirin, za mu ga yadda matan Palasdinawa, suke nuna hannu wa sojojin Yahudawa 'yan-share-guri zauna, kana a daya hannun kuma suna dauke da duwatsu suna jiran samun dama don su jefi abokan gaba. A halin yanzu, wadannan mataye da sauran mataye irinsu a duk fadin duniya, ana daukarsu a matsayin kashin bayan wannan gwagwarmaya. Hakika hijabi shi ne tutarsu kuma suna alfahari da matsayinsu na masu yaki da babban makiyin gaskiya.
|