Hijabi Lullubin MusulunciMuna fatan an fahimci irin bayanin da muka yi dangane da bambancin da ke tsakanin hijabi (kange-wa) irin wadda aka dauka a zamanin jahiliyya danga-ne da mu'amalolin mace, da kuma hijabin da Musu-lunci ya dauka a matsayin garkuwa da zai kare mace daga zalunci da tozarta kimarta da wasu wawaye ke yi. Abin da ya saura kawai shi ne mu yi bayani kan babban dalilin da Musulunci ya dogara da shi wajen tsara wa mace wani irin tufafi daidai da yadda Allah Ta'ala yake so ga bayinsa. To don saboda bayani kan wannan babban dalili ko manufa, ba tare da tsawaitawa ba, bari mu ambato wadan-nan abubuwa: Da farko, akwai mahanga guda biyu dangane da mu'amala tsakanin namiji da mace: Mahanga ta farko tana ganin mutum yana iya saduwa (jima'i) da kowace mace a cikin al'umma, kuma yin hakan ba zina ba ce. Mahanga ta biyu kuwa, ta takaita 'yancin jima'in mutum ga matar da suka yi aure ne kawai, kana in ba tare da aure ba, to ba shi da 'yancin saduwa da wata mace. Wannan mahanga ta farko irin ta ce a halin yanzu ake gudanarwa a Turai. Sannan mahanga ta biyu kuwa ita ce mahangar Musulunci dangane da mu'amala tsakanin mace da namiji. Wannan shi ne babban jigon wannan al'amari, wanda kuma duk wani bayani daga jikin shi aka ciro. Duk wata dabi'ar mutum dangane da mace an ciro ta ne daga wannan mahanga ta farko, wadda ke da alaka da sha'awarsa ta jima'i da mace a wuraren bukukuwa, tarurruka da wasu mataye da ba matayensa ba da kuma cakuda tsakanin jinsosi, da kuma sanya mace ta zamanto wata abin kawa da burge mazaje da dai sauran abubuwa makamantan haka. Dangane da mahangar Musulunci kuwa, al'amarin ya kasu kashi-kashi: Lalle umurnin mace da ta rufe dukkan jikinta, in banda fuskoki da tafukanta, daga idanuwan mazaje, face mijinta da danginta, kana kada ta bata lokacinta wajen zance maras amfani da kuma tafiya da mazaje da makamancin haka, sannan kuma haramta ta keban-tu da wani namiji in dai ba danginta ba, da kuma sauran mu'amaloli da fikihun Musulunci ya yi bayani, da kuma mahangar Musulunci dangane da alakar namiji da mace, duk kariya ce da kuma kiyayewa daga lalacewa da rashin kunya. Hakika idan muka yi la'akari da irin yanayin wadannan ra'ayoyi guda biyu da kuma abubuwan da suka haifar, to lalle za mu kai ga natijar cewa Musu-lunci yana tsananin kishi dangane mutuncin mace da kuma daukakarta, tsarki da girmanta, ta yadda ba za ta zama wata haja abin sayarwa ga mazaje ba. Don haka, Musulunci yake ba da muhimmanci wajen daidaitawa da tsara alaka irin ta jima'i, kana kuma ya yi kokari wajen toshe duk wata hanyar da wadannan mugayen mutane suke amfani da ita wajen tozarta mace don biyan bukatunsu na sha'awa (da ita) yadda suke so. Sannan kuma abin da ita wannan mahanga ta jahiliyya, tsohuwar ce ko sabuwar, take son ta cim ma shi ne yin rikon sakainar kashi ga wannan ka'ida don saboda amfanin maza. Babbar matsalar wannan mahanga ita ce cewa ta ginu ne kan amfanin namiji da biyan bukatansa ko da kuwa macen tana iya samun wani amfani!! Kana idan muka sake yin la'akari da irin girman amfani da ribar da mazaje sukan samu ta bangaren jima'i da tattalin arziki a karkashin wannan mahanga, za mu ga wannan al'amari na haramci da kuma dabi'ar tozarta mace da aka gudanar a zamanin jahiliyya, daidai yake da irin abin da ake gudanarwa a yau da sunan wayewa, wadda hakan cutarwa ce ga ita mace. Lalle irin iyakance mace da aka yi a sabuwar jahiliyya (ta wannan zamani) kawai ya banbanta da tsohuwar (jahiliyya) ce kawai ta bangaren zahiri da abin da ya fito fili. Amma yana nan dai a matsayinsa na sarka da ta dabaibaye mace, ta hana ta 'yancinta, kuma ta kwace mata ikonta. Don haka namiji ya mai da mace kamar wata kamammiya ko kuma baiwa ta hanyar amfani da hanyoyi daban-daban na kasuwanci, gidajen karuwai, gidajen sinimomi, gidajen radiyoyi da talabijin, jaridu da wuraren nuna kawa don biyan bukatunsa. Koda yake, a lokacin da wadansu matayen suka fara nuna damuwarsu da irin wahalhalun da suke fuskanta a karkashin irin wannan al'ada ta Turai, to an samu wasu mazaje 'yan kadan wadanda suka mike tsaye don kalubalantar irin wannan bala'i da mata suke fuskanta a Turai, saboda dabi'un wasu mazajen. Ga wadansu misalai nan da suke nuna irin wuce gona da irin da mazaje suke yi wa mataye da kuma mummunan sakamakonsa: A kasar Biritaniya, 'yan mata 9 daga cikin 12 - 'yan kasa da shekaru 20 - suna fuskantar fyade da sacewa. To amma jami'an tsaro sun sami daman kama kashi 13 cikin dari ne kawai na daga cikin masu laifin. Kana kuma a 'yan shekaru da suka gabata yanayin aikatalaifuffuka ya karu da kashi 84 cikin dari; kana kuma laifuffukan kananan yara ya karu da ninki biyar a watannin farko na shekarar 1975[13] Wata jaridar kasar Italiya mai suna "Omiga" ta fitar da wasu labarurruka kan irin laifuffukan da aka aikata a wannan kasa inda take cewa:
|