Hijabi Lullubin MusulunciAnas ya ruwaito cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Duk wanda ya auri mace don daukaka da kyawunta, to Allah ba zai kara masa nasa ba, face ma ya kawo masa wulakantuwa; duk wanda ya aure ta don dukiyarta, Allah ba Zai kara masa nasa ba, sai dai ma Ya sanya masa talauci; duk wanda ya aure ta don dangantakanta, to Allah ba Zai kara masa nasa ba, sai dai ya mai she shi ba kome ba; duk wanda ya auri mace ba don kome ba face sai don ya kalle ta (ya ji dadi), kuma ya kare farjinsa (daga aikata haramun) da kuma kulla zumunta, Allah Zai albarkace shi ta hanyarta, haka ita ma"(1). Alkur'ani mai girma yana cewa: "Kuma daga ayoyinSa, Ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku nitsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani".(Surar Rum, 30:21). (Al-Targib wa al-Tarhib, juzu'i na 3, shafi na 46) A wata ayar kuma, ana magana kan mace mai biyayya: "…..to, salihan mata masu da'a ne, masu tsarewa (yayin da mazansu ba sa nan) kan abin da Allah ya tsare....".(Surar Nisa'i, 4: 34) Kwadaitarwa Da Kuma Kulawa Da Hijabi: Musulunci, duk da irin tausayin mata da yake yi, yana kwadaita musu kulawa da hijabi a wannan aya ta Alkur'ani mai girma: "Ya kai Annabi! Ka ce wa matanka da 'ya'yanka da matayen muminai su kusantar da kasa daga manyan tufafin da ke a kansu. Wancan ya fi sauki ga a gane su domin kada a cuce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin kai". (Surar Ahzabi, 33:59) Daidaitawa
A ayoyi da dama, Alkur'ani mai girma yana magana kan daidaitawa tsakanin jinsosin nan biyu. A daya daga cikinsu yana cewa: "....kuma su matan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani...". (Surar Bakara, 2: 228) A wani gurin kuma, Alkur'ani mai girma yana cewa: "Ya ku mutane! Lalle ne mu, mun halitta ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku dangogi da kabiloli, domin ku san juna. Lalle mafificinku daraja a wurin Allah, (Shi ne) wanda yake mafificinku a takawa. Lalle ne, Allah Masani ne, Mai kididdigewa".(Surar Hujurati, 49:13) Dangane da aiki da kuma aikata kyawawan dabi'u, kuma Alkur'ani mai girma ya bayyana daukakan Musulunci da kuma daidaitawarsa ga ma'aikata. Hakika hakan wani abu ne da kasashen Turai suka gagara tabbatar da shi. Alkur'ani mai girma yana cewa: "Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan kwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhali kuwa yana mumini, to wadannan suna shiga aljanna kuma ba za a zalunce su da gwargwadon hancin dabino ba". (Surar Nisa'i, 4: 124) (Wanda ya aikata aiki na kwarai daga namiji ko kuwa mace, alhali yana mumini, to hakika, Muna rayar da shi, rayuwa mai dadi. Kuma hakika, Muna saka musu ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa). (Surar Nahali, 16: 97) A wata ayar kuma, Allah Madaukakin Sarki Ya yi alkawarin cewa: "...lalle ne Ni, ba zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sashenku daga sashe....". (Surar Ali Imrana, 3:195) Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki |
back | 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 | next |