Hijabi Lullubin MusulunciLalle kan wannan mummunar dabi'a ga mace wanda ya hada da tsoratarwa, kulle ta a cikin gida da kuma kange ta daga duk wani nau'i na rayuwa da jin dadi, domin kuwa tarihi ya hakaito kange mace da aka yi, wato kange ta daga taka rawa cikin al'amurran rayuwa, da kuma hana ta 'yancin da take da shi. Hakika irin wannan bakar akida ta kange mace da ya faru a zamanin jahiliyya, da kuma duk fadin duniya har da kasar Iran (ta wancan lokacin), Indiya, Masar, Turai da kuma kasashen larabawa kana da kuma irin yadda ake tafiyar da mace, shi ya ba da dama wajen kirkiro kungiyoyin kira ga kwato wa mata hakkinsu. To amma irin lamurran hijabi da kuma kula da mace da Musulunci ya zo da shi, ya saba wa irin kangewar lokacin harem, wa'id da kuma lokacin cinikin bayi inda mata suka wahala da gasken gaske. Mahangar Musulunci Dangane Da Hijabi
Hakika, irin nau'in hijabi (kangewa) da Musulunci ya dauka, nesa ba kusa ba, ya saba wa irin nau'in kangewar zamanin Jahiliyya da kuma mummunan irin yanayin da ya wanzu a fadojin wasu sarakunan Umayyawa da Abbasiyawa dangane da amfani da mata don cim ma burinsu na sha'awa. Kai hatta ma dai hakikanin wannan kalma ta hijabi, ba ta shiga rayuwar Musulmi ba face kwanannan. To koma dai mene ne za a ce dangane da mace, al'amarin dai guda ne cewa saboda irin muhimmancin da Musulunci ya bawa mace, shi ya sa har ya tsara mata wani irin nau'in tufafi, wanda haka yana nuna irin girma da daukakan da Musulunci yake ganin mace tana da shi, da kuma kula da tsabtarta. Lalle dai a Musulunci, da kuma duk abin da ya kunsa, babu wata doka ko ka'ida da ta hana mace musharaka cikin al'amurran rayuwa, ko kuma ya tsare ta a cikin gida kamar yadda ya faru a zamanin Jahiliyya. Hatta ma dai wannan kalma ta hijabi kwanan nan aka fara amfani da ita cikin akidar Musulunci[12]. Bugu da kari kan irin tufafi na musamman da mace take sa wa yayin da za ta fita daga gidanta- kamar yadda za mu yi bayani nan gaba- to Musulunci ya yi amfani da kalmar "sitr" (lullubi) ne ga wannan irin aiki. Hakika Musulunci ya wajabta wa maza da mata da su kawar da idanuwansu daga kallon juna, face dai matayensu, mazajensu ko kuma muharramansu. A bangare guda kuma, Musulunci ya wajabta wa mace sanya hijabi, kana a daya bangaren kuma ya sanya wasu dokoki ga shi ma namijin. Idan har an tsara wa mace wani nau'i na tufafi don ta kare kyawun jikinta; to shi kuma namiji a daya bangaren, an wajabta masa kawar da idanunsa daga kallon mataye, face dai muharramansa da kuma kare farjinsa. Don samun daidaituwar wannan kalma ta hijabi da ainihin manufan Musulunci da kuma abin da yake nufi, to yana da kyau mu yi bayanin cewa: Lullubi da kamewa a Musulunci ya hada da maza da mata ne; to amma yanayinsu ya sha banban ne ta yadda dai za su iya kiyaye kyawawan dabi'u, kare dabi'u da kuma girmama matsayin mace a dukkan rayuwa. Domin shi Musulunci ba ruwansa da tsarewa ko kuma kange mace daga tafiyar da 'yancin da Allah Ya bata, kana a cikin tsari da ka'idojinSa, babu cutarwa da kaskantar da darajar mace. Hakika ya zamanto abin alfahari ga Musulunci, cewa saboda tabbatar dokokinsa ne aka kawo karshen yanayin wulakanci da bautar da mata, da mazaje suke yi a zamanin Jahiliyya, wanda ya bakanta tarihin dan'Adam, kafin bayyanar Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma sakonsa. A takaice za a iya fassara hijabi (lullubin) Musulunci da cewa wani irin nau'i ne na sutura da kuma takaita alaka tsakanin maza da mata, wadanda ba muharraman juna ba, da sanya mace a tsarkakakken tafarki na girmamawa da kuma tabbatar mata da 'yancinta. Me Ya Sa Hijabi Kawai?
|