Hijabi Lullubin Musulunci(G)- Haramun ne ga namiji da ya kadaita da matar da ba muharramansa ba a wajen da babu mai shigansa, idan har suna jin tsoron faruwar aikata haramun; to amma babu laifi ga mutum ya kadaita da macen da ba muharramansa ba a wajen da mutane suke da 'yancin shiga. (H)- Haramun ne ga mutum ya taba jikin macen da ba muharramansa ba, haka ita macen, ya haramta ta taba jikin namijin da ba muharraminta ba, kamar gaisuwa ta hannu da dai sauransu. (I)- A yayin lalura, kamar wajen yin magani ko kuma kubutar da mutumin da ruwa yake kokarin cinyewa, yana halalta ga namiji da ya taba jikin mace ko kuma ita macen ta taba namiji, matukar dai babu macen da za ta iya wannan aiki ga 'yan'uwanta mata ko kuma namiji ga 'yan'uwansa maza. (J)- Yana halalta ga mazaje su saurari muryar macen da ba muharramansu ba ce, matukar dai ba da niyyar jin dadin ko kuma wani abin da zai kai mutum ga aikata haramun ba. Haka kuma yana halalta ga mace da ta jiyar da muryarta ta hanyar tattaunawa da kuma yin jawabi ga mazajen da ba muharramanta ba. To amma da sharadin muryar na ta ba zai janyo fitina ga masu sauraronta ba, domin haramun ne ga mace ta yi magana da mazaje cikin rangwadi da karya murya. (K)- Mustahabi ne ga mace da ta kiyaye kyau da adonta ga mijinta kawai, don kuwa jan hankali da kuma kyau suna da muhimmiyar rawa da suke takawa a rayuwar mace, kuma muhimmin al'amari ne cikin abubuwan da suke kawo jin dadin rayuwar iyali. (L)- Haramun ne ga mace da ta kwaikwayi maza (wajen sa tufafi, aiki da dabi'a) , haka shi ma namijin. (M)- Haramun ne ga mace ta bude kanta da shafa turare yayin da za ta fita waje, wato haramun ne ta sanya turare ta yadda mazajen da ba muharramanta ba za su iya jin kamshin nasa lokacin da take wucewa cikinsu ko kuma yin mu'amala da ita. Idan muka dubi wadannan shar'antattun ayyuka wadanda suke karkashin hijabin Musulunci da kyau, za mu ga cewa dukkan mazaje da mataye suna da nasu kaso cikin wannan doka, tare da jaddadawa ga mata wajen rufe dukkan jikinsu. Hakika hakan a fili yana nuna mana cewa Musulunci yana so ne ya assasa tsarkakakkiyar alaka tsakanin wadannan jinsu-na biyu; yada tsarki da mutunci tsakanin al'umma; kana da kuma kare al'umma ta hanyar kyawawan mu'amaloli. Kana kuma ba burinsa (Musulunci) ba ne ya wulakanta matsayin mace ko kuma ya kange ta daga ba da tata gudummawa ga rayuwa ba, kamar yadda wadannan dokoki da suka gabata suka nuna a fili. Hakika idan har muna so mu yi hukumci kan al'amarin rufe dukkan jiki ga mata, kana ga shi kuwa mun ce maza da mata daya suke a mahanga ta gaba daya dangane da hijabin Musulunci, to tambaya a nan ita ce: Me ya sa mace kawai ne aka kallafa mata rufe dukkan jikinta ba namiji ba? Amsa a nan, wanda babu wani cikakken mutum da zai musanta, ita ce cewa dalilin kallafa wa mace rufe jiki ita kadai yana da alaka da irin dabi'u da kuma zahirinta. Domin kuwa bangaren janyo hankalin abu da mace take da shi ya fi na namiji; tana da cikakkun abubuwan motsa rai. Don haka, ado da kyau suna daga cikin abubuwan da ake fara siffanta ta da su. Hakika idan har ba a takaita su ba, to tana iya sanya kamilin mutum, da saninsa ko kuma ba da saninsa ba, ya aikata haramun. Wannan irin siffa da mace take da shi, wanda ke ba ta daman janyo hankalin maza gare ta, shi ne babban ummul aba'isin da ya sanya Musulunci ya wajabta wa mace rufe jikinta don magance faruwar barna. Don haka bai dace a umurci namiji da ya rufe dukkan jikinsa kamar mace ba; domin kuwa namiji bai mallaki wadannan siffofi ba, kuma shi ba a halicce shi da dabi'ar yin ado da kawata kansa, don ya jawo hankalin mata ba. To amma duk da haka fa, Musulunci bai son mutum ya yi mummunan shigar da ba ta dace ba, don kada ya nuna wasu wuraren da ba su dace ba na daga jikinsa. Dangane da janyo hankali, akwai wasu abubuwa guda biyu da suke wanzuwa, daya ga mace dayan kuwa ga namiji. Wanda yake tare da mace kuwa shi ne sha'awar nuna ado da kyanta, hakan yana daga cikin dabi'unta. Na namiji kuwa shi ne sha'awar kallon mace ba wai kallo kawai ba, a'a har ma da samun jin dadi daga hakan. Duk wadannan abubuwa suna nan tare da su. Wani masani mai suna, Will Durant yana cewa, a wannan duniya babu wani abu da ya fi tabbatuwa kuma ake so a tabbatar da shi kamar sha'awar da mutum yake da ita na kallon mace.
|