Hijabi Lullubin Musulunci



Hijabi Lullubin Musulunci

A- Gabatarwar Mawallafa

Hakika Musulunci ya haifar da gagarumin sauyi a tarihin mace, wadda har ya zuwa yau ba a samu na biyunsa ba. Domin ta hanyar sa ne, ta samu damar dawo da mutunci da hakkokinta da aka raba ta da su a karkashin zaluncin zamanin jahiliyya na karnoni da dama. Ta haka ne Musulunci ya kwato mata hakkokinta ta yadda za ta yi rayuwa cikin mutunci karkashin tsarin rayuwa mafificiya.

A karo na farko a tarihi, mace ta samu damar amfana da hakkokinta na dan'Adamtaka a karkashin tsari da dokoki irin na Musulunci. An yaye wa mata kangin zalunci, kana kuma ta samu damar rayuwa a matsayin dan'Adam mai mutunci, daukaka kana mai matsayi kamar dai-dai da na namiji. To amma fa dole ne wannan 'yanci ya kasance cikin iyakokin Allah Madaukakin Sarki

Wanda Ya ba wa mace dama, kana kuma Ya tsara mata hanyar da za ta iya ba da nata gudummawar wajen gina rayuwa, daukaka, tabbatar da gaskiya da kuma yada alheri.

To hakika wannan kuduri zai kasance ne kawai kamar wani mafarki da tatsuniya a wajen wadansu, idan har ba a karfafa shi da wasu ayoyi na Alkur'ani mai girma da hadisan Annabi da kuma Mutanen gidansa (Ahlulbait) tsira da amincin Allah su tabbata a gare su ) ba.

A zamanin jahiliyya, al'umma tana ganin mace a matsayin wata bi-tsami, wani abu na la'ana, matatta-rin muggan ayyukan shaidan, ko kuma sukan kwatanta ta da matsayin wata dabba da aka halicce ta a yanayin dan'adam.

To amma ko da Alkur'ani ya zo sai ya karyata wannan kuduri, wanda ya saba wa gaskiya da kuma hakika. Ya ci gaba da nuna cewa namiji da mace wasu irin 'yan tagwaye ne da suka fito daga mabubbuga da kuma manufa guda.

" Ya ku mutane ! ku bi Ubangijinku da takawa, Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata....." ( Surar Nisa'i: 4:1) " Shi ne Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya sanya daga gare ta,

ma'aurata, domin ya natsu zuwa gare ta...." (Surar A'araf: 7:189) "Kuma Allah Ya sanya muku matan aure daga kawunanku, kuma Ya sanya muku daga matan aurenku diya da jikoki...."(Surar Nahali: 16:72) Bayan bayyana matsayin mace a rayuwa da kuma samuwar dan'adam a fili,

Alkur'ani mai girma ya yi kakkausar suka ga al'adar nan ta bisne 'ya'ya mata da rai, wato Wa'id[1].

"Kuma idan wadda aka turbude ta da rai aka tambaye ta, saboda wani laifi ne aka kashe ta?"(Surar Takawir: 81:8-9) Kana kuma ya kawo karshen zamanin da ake kange mace daga aure har sai ta biya kudin fansar kanta ko kuma cikin zalunci a gaje ta bayan mutuwarta.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next