Halayen Imam Mahadi (a.s)



5- Da kafuwar hukumar Imam Mahadi (a.s) ne alheri mai yawa zai cika al'umma kuma kasa da sama kowanne zai kawo albarkatunsa. Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Allah zai gudanar da albarkar sama da ta kasa saboda Imam Mahadi (a.s), sama ta yi ruwa, kasa kuma ta futo da shuka[37]. Wannan juyi mai albarka maras misali na halifana na goma sha biyu, kuma wasiyyin karshe na Annabi kuma jagoran duniya Imam Mahadi a wannan zamanim zai kai mutane ga tsarkaka da takawa da imani, kuma mutane dukkaninsu zau kasnade karkashin tarbiyyar Allah, kuma alakarsu zatakasance a bisa kyawawan halaye ne, a irin wannan yanayi ne Allah yake bayar da albarkarsa. Kur'ani mai girma yana cewa; da mutanen alkaryu (garuruwa) sun yi imani kuma sun ji tsoron Allah da mun bude musu albarkatu daga sama da kasa[38];

6- A lokacin da sama da kasa suka bude albarkatunsu kuma aka cika Baitul mali, kuma aka raba dukiya da daidaito, to babu wani wuri da talauci zai samu, kuma al'umma har abada zata rabu da talauci kenan[39]. A wannan lokacin za a samu 'yan'uwantaka da kaunar juna da nisantar bin amfani da maslahar kai, kuma kowa ya zama tamkar dan uwa ga dayansa, don haka ne sai a samu yanayin na hadewa a dunkule.

Game da hukumar Imam Mahadi (a.s) ne Imam Muhammad Bakir (a.s) yake fada cewa: A kowace shekara yana bayar da kyauta sau biyu ga mutane, koma a kowane wata yana ba su sau biyu, kuma a wannan lokaci zai aiki da daidaito tsakanin mutane har sai an kai ga babu wani mai bukatar dukiyar zakka[40]. A wasu ruwayoyi ya zo cewa rashin bukatar mutane saboda wadatar zuci ne, sakamakon yarda da suka yi da abin da Allah ya ba su, kuma suna farin ciki da wannan, don haka ba sa bukatar dukiyar wasu. Manzon rahama (s.a.w) yana fada yana mai siffanta wannan daula da cewa: …Allah zai sanya rashin bukata a zukatan mutane[41].

A dunkule muna iya cewa; a zamanin Imam Mahadi (a.s) za sa mun fitar rashin buata daga zukata, kuma za a raba dukiya da daidaito, wannan kuwa yana nuna cikar kyawawan halayen mutane. Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Ubangiji zai sanya rashin bukata a zukatan al'ummar Muhammad a wannan zamani, kuma adalcin Imam Mahadi (a.s) zai mamaye ko'ina, ta yadda Imam Mahadi (a.s) zai yi umarni ga mai shela ya shelanta cewa: waye yake bukatar dukiya? Amma ba mai tashi tsakanin mutane sai mutum daya, sai Imam (a.s) ya ce da shi: ka tafi wajen mai kula da Baitul mali ka ce masa: Imam Mahadi (a.s) ya ce ka ba ni dukiya. Sai ya tafi ya gaya masa. Sai mai kula da Baitul mali ya ce: kawo tufafinka. Da an cika masa tufafinsa da dukiay, da ya dauka sai ya yi nadama, ya ce: me ya sa na fi kowa kwadayi ne a cikin al'ummar Annabi… sai ya mayar da dukiyar ya ki karba, sai a ce masa ai ba ma karbar abin da muka riga muka bayar[42].

7- Kur'ani madaukaki ya yi alkawari a wurare uku na cewa zai sanya addinin musulunci addinin Duniya gaba daya: "Shi ne wanda ya aiko Manzonsa da shiriya da addinin gaskiya domin ya dora shi a kan addini dukkanisa…"[43]. Kuma babu kokwanto Allah ba ya saba alkawari. "Hakika Allah ba ya saba alkawari"[44].

Duk da irin kokarin da Annabin rahama (s.a.w) da sauran waliyyan Allah suka yi sai dai har yanzu wannan rana ba ta zo ba[45], amma da sannu wannan rana da kalmar shahada zata filfila a kan tutar tauhidi zata zo, kuma za a kawar da kafirci da shirka har sai ya kasance babu wani kufai nasu da zai yi saura.

Imam Muhammad Bakri (a.s) yana fada game da ayan nan da take cewa: "ku yake su har sai ya kasance babu wata fitina kuma addini gaba daya ya kasance na Allah…[46]" cewa: Tawilin wannan aya har yanzu bai zo ba, duk wanda ya yi zamani da Imam Mahadi (a.s) zai ga tawilin wannan aya, a wannan zamani duk inda dare ya kai to addinin Muhammad (s.a.w) zai kai wurin, ta yadda babu wani kufai na shirka da zai yi saura a bayan kasa, kamar yadda Allah ya yi alkawari[47].

8- A Daular jagoran zamanin karshe (a.s) za a samu aminci da tsaro mafi girma wanda yake daya daga ni'imomin Allah mafi daukaka da dan Adam yake burin samu. Matukar al'umma ta kasance mai hadafi daya, kuma ta kiyaye kyawawan halaye, kuma adalci ya mamaye dukkan rayuwa mutane a daidaiku da al'umma, to tabbas za a samu kawar da rashin tsaro da rashin aminci da zaman lafiya. Imam Ali (a.s) yana cewa: …yayin da mahadinmu zai zo sai gaba ta tafi daga zukata, dabbobi ma zasu daidaita da juna, (kuma za a samu aminci da) mace kyakkyawa da ado zata yi tafiya daga Iraki zuwa Sham… amma babu wani abu da zai tsoratar da ita[48].

Tabbas wannan lamari yana da wahalar sawwalawa ga mutumin yau sai dai idan mun duba abubuwan da zasu wakana to wannan mai saukin faruwa ne. Ubangiji madaukaki yana fada: Ubangiji ya yi wa wadanda suka yi imani alkawari cewa zai sanya su halifofinsa masu maye gurbinsa a bayan kasa kuma zai canja musu da aminci bayan"[49]. Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Wannan aya ta sauka ne game da Imam Mahadi (a.s) da mataimakansa[50].

9- A hukumar Imam Mahadi asiran ilimi masu yawa na ilimomin musulunci zasu bayyana, kuma ilimin mutane zai fadada ta yadda ba a tsammani. Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Ilimi haruffa ishirin da bakwai ne, kuma abin da Manzo (s.a.w) ya kawo daga ciki harafi biyu ne, mutane har yanzu ba su da ilimi sai na wadannan haruffa biyun, yayin da Imam Mahadi (a.s) zai zo zai futo da haruffa ishirin da biyar da suka rage, kuma ya yada su a cikin mutane, wadannan haruffan za a yada su tare da wadannan haruffa biyu ne[51].Wannan ruwayoyi da wasu ruwayoyin ma suna nuni da cewa; ilimin dan Adam na masana'antu da kere-kere zai kasance yana da bambanci da na yau mai nisa kwarai da gaske[52].

Imam Ja'afar Sadik yana cewa: idan Imam Mahadi (a.s) ya bayyana to mumini da yake gabas zai ga dan'uwansa mumini da yake yammacin Duniya[53]. Kuma yana cewa: yayin da Imam Mahadi (a.s) zai bayyana, karfin gani da ji na shi'armu zai karu, ta yadda Imam Mahadi zai yi magana da Shi'arsa daga nisan baridi daya (farsahi hudu) kuma su ma suna jin maganarsa suna kuma ganinsa alhalin yana wajensa[54].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 next