Halayen Imam Mahadi (a.s)Kuma tarihin wadanda suka hadu da su da suka bayar da ya shafi irin wannan lamarin suna da yawa, kamar dai rayuwar Hidir (a.s) da Musa (a.s) yayin da suka yi tafiya, muna ganin yadda hannun gaibi ya yi taimako ta hannun Hidir (a.s) wanda in ban da Musa (a.s) da yake tare da shi babu wani wanda ya san wani abu ya faru. To haka nan raywuar Imam Mahadi (a.s) take kasancewa Addu'o'i masu yawa da babu kamarsu a cikin tasiri ga ruhin dan Adam da suka zo wadanda suka shafi samuwar Imam Mahadi (a.s) suna da yawa, kuma lizimtar karanta su yana nuna ma kusanci da shi, domin wanda ya lizimze su yana nufin lamarin Imam (a.s) shi ne muhimmin lamari gunsa, kuma a shirye yake ya kasance cikin mataimakansa a duk inda yake kuma a kowane zamani yake, sannan imaninsa da Imam Mahadi (a.s) yana karuwa ke nan. Wasu daga malaman sunna sun tafi a kan cewa Imam Mahadi (a.s) shi ne dai wannan dan Hasan Askari (a.s) wanda yake imani na goma sha biyu daga cikin wasiyyan Manzon Allah (s.a.w) wanda zai zo karshen duniya ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci. A yankunanmu mutane masu kima da ilimi da takawa a tarihin al'ummarmu kamar shehu dan Fodio yana daga cikin wadanda suka yi imani da wannan lamari kamar yadda ya kawo a cikin littafin "Nasihatu Ahluz-zaman". Don haka lamarin Imam Mahadi (a.s) ba boyayya ba ne, kuma malamai masu yawa daga masu tsoron Allah sun yi da'awar haduwa da shi da ba su sako na musamman da yi musu horo ko nuna musu wata tarbiyya ko amsar wata mas'ala yawanci a aikace, ko kuma ya ba su amsar tambayarsu da ta rikice musu. Kusa dukkan al'ummar musulmi in ban da wanda ya fita daga cikin ittifakin musulmi zamu ga dukkan su suna sauraron wannan mai daraja mai girma domin su yi masa biyayya idan ya zo. Sannan ruwayoyi masu yawa sun zo suna nuna su waye sahabbansa, wanda suka hada da mafi shahararsu shi ne Annabi Isa dan Maryama (a.s) wanda zai kasance daga mafi girman mataimakansa, kuma zai bi Imam Mahadi (a.s) salla, wanda wannan lamari yake nuna fifikon wasiyyan Manzon Allah (s.a.w) a kan sauran annabawa, sai dai ga wadanda basirarsu ta makance. An kashe babansa yana dan karami shekaru 5 kawai, don haka ne sai ya dauki ragamar jagorancin al'umma bisa wasiyyar Manzon Allah (s.a.w) a matsayinsa na mai shiryar da al'umma, sai dai babu dadewa sai azzalumai suka nemi ganin bayansa shi ma, wannan lamarin ya sanya masa wajabcin boye kansa daga ganin mutane da umarnin Allah madaukaki bisa kuma wasiyyan Manzon Allah (s.a.w) kakansa, da ilimin da Allah ya ba shi. Sai ya kasance al'umma tana iya ganin sa idan ya so amma ba ta gane shi ne, ko kuma ta kasa ganin sa gaba daya!. Karancin shekarunsa ba ya hana masa imamanci da jagorancin al'ummar musulmi, domin Isa (a.s) ya kasance haka yana cikin tsumman goyo, sannan kakansa Imam Ali al'Hadi (a.s) ya samu imamanci yana shekaru 9 ne, baban kakansa wato Imam Muhammad Jawad (a.s) ya samu jagorancin al'umma na imamanci yana shekaru 8 ne, ga kuma babansa Hasan Askari (a.s) yana dan shekaru 22 ne lokacin da nauyin imamanci ya same shi bayan wafatin babansa Imam Ali al'Hadi (a.s). Sauraron bayyanar Imam Mahadi (a.s) ba yana nufin mutane su yi ta sabo ba don ya bayyana, ko kuma su zauna ba sa yin kyakkyawa da sunan suna jiran mai gyara ne, wadannan masu yin irin wannan sunansu batattu wadanda suka kauce wa hanya, domin umarnin Allah (s .w.t) da manzonsa (s.a.w) da na imaman shiriya (a.s) duk yana karfafa matukar gyara domin gaggauta bayyanarsa, da dukufa kan yin addu'o'i, domin lalacewar al'umma tana nuna ke nan ba shi da mataimaka, shi kuwa yana bayyana ne idan yana da mataimaka na gaskiya ba bar gurbi ba. Zalunci ya cika ko'ina a duniya ne sakamakon kauce wa hanya, sannan Imam Mahadi (a.s) yana neman masu taimaka masa ne, idan kuwa kowa ya lalace to yaya muke tsammanin bayyanarsa, yayin da wadanda ya kamata su taimaka masa su ne ma zasu yake shi din domin an kaddara su ma sun lalace. Da wannan ne zamu gane muhimmanci gyara kawukanmu da neman yin gyara cikin al'ummarmu domin da wannan ne zamu same yayewar bakin ciki, da bayyanar farin ciki da bayyanarsa mai tsira da aminci. Imani da samuwar Imam Mahadi (a.s) wata ilhama ce da Allah ya sanya ta cikin zukatan bayinsa, don haka ne ma zamu ga babu wata al'umma musamman mai addinin sama wanda yake saukakke daga Allah ko da kuwa an gurbata shi ne, sai ta yi imani da samuwar mai gyara a karshen wannan duniya. Sai dai akan samu sabani ne
|