Halayen Imam Mahadi (a.s)
Imam Ridha (a.s) yana fada game da siffanta Imam Mahadi (a.s): Idan ya bayyana sai Duniya ta haskaka da hasken Ubangijinta, kuma a sanya ma'auni na adalci tsakanin mutane, babu wani da zai zalunci wani.
Abubuwan Da Hukuma Zata Samar
Masu son hawa kan karagar mulki sukan yi bayanin hadafin hukumarsu, amma ba kasafari sukan isa kaiwa ga wannan hadafin ba, wannan kuwa yakan kasance ne saboda hadafinsu ba na hakika ba ne ko kuma tsarin da aka dauka yana da matsalar da ba zai iya kaiwa ga nasara ba, ko kuma rashin sa'ar samun masu gudanarwa marasa dacewa. A hukumar Imam Mahadi (a.s) hadafinsa na gaskiya ne, kuma tsari ne mai kamala karkashin Kur'ani da sunnar Ahlul Baiti (a.s) a dukkan fagagen gudanarwa, don haka ne ma za a samar da wani juyi mai girma da Duniya zata fuskanto zuwa gareshi, kuma a samu cikar hadafofi da dukkan kamala ta Duniya da ta lahira. A nan zamu ga wasu ruwayoyi da suke nuna wasu daga sakamakon da aka cimma na nasara a daular Imam Mahadi (a.s).
1- Ya zo a cikin Kur'ani mai daraja da ruwayoyi masu yawa cewa babban hadafin hukumar Imam Mahadi (a.s) shi ne samar da adalci a ko'ina a Duniya a dukkan fagen rayuwa. Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: na rantse da Allah, adalci zai kutsa cikin gidajen mutane, kamar yadda sanyi da zafi suke kutsawa cikin gidaje. Wannan yana nuna yaduwar adalci da hatta a cikin gidajen mutane daidaikun 'ya'yan gida daya ba sa zaluntar junansu, kuma suna zama tsakaninsu da adalci, kuma wannan adalci ne da zai tsayu a karkashin koyarwar Kur'ani da kyautatawa.
2- An yi bayanin cigaban tunani da kyawawan halaye da tsaro a hukumar Imam Mahadi (a.s)a wasu ruwayoyi.Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: a zamanin da Imam Mahadi zai bayyana zai sanya hannunsa a kan bayin Allah sai da albarkacin hakan hankulansu su kammala. Kuma mun sani cewa dukkan kyawawan ayyuka suna karkashin cikar hankalin dan Adam ne, hankali shi ne ma'aikin badini mai hukunci kan rayuwar mutum, da gyaruwarsa ne ayyuka da tunanin mutum zasu gyaru. An tambayi Imam Ja'afar Sadik (a.s) mene ne hankali? Sai ya ce: hankali shi ne abin da ake bauta wa Allah madaukaki da shi, kuma da shi ne ake shiryuwa zuwa ga hanyar aljanna.
Amma a wannan al'umma yau da muke gani wacce take ba tare da Imami ba muna ganin yadda sha'awa ta yi galaba kan hankali, da yadda aka manta da kyawawan halaye na shari'ar Allah.
3- Ya zo a cikin ruwayoyi masu yawa cewa; a hukumar Imam Mahadi (a.s) mutane zasu kansane cikin soyaya da kaunar juna kuma a kawar da duk wata gaba daga zukantasu Imam Ali (a.s) yana cewa: "Idan mai tsayawar cikinmu (da juyinmu) ya bayyanar… kuma gaba da juna zata tafi daga zukatan bayi…". A wannan zamani babu wani hakki na wani da zai tafi, kuma hankali shi ne mai tafiyar da rayuwa ba son rai da sha'awa, don haka babu wata gaba da ta yi saura a cikin zukata, kuma za a samu hadin kai da kaunar juna a zukata karkashin hukumar 'yan'uwantaka ta Kur'ani da koyarwar Ahlul Baiti (a.s). Imam Ja'afar Sadik yana fada game da hakan: a wannan zamani Ubangiji zai sanya haduwa da kauna a tsakanin zukata masu rarraba da kiyayya.
Ba don ludufin Allah da taimakonsa ba, da dan Adam da yake cikin wannan yanayi da kiyayya da gaba da rufewar idon son Duniya bai kai ga hakan ba. Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: A lokacin da Imam Mahadi (a.s) zai tsayar da hukuma za a samu abota ta kauna ta gaskiya, kuma duk mabukaci yana iya daukar gwargwadon abin da yake bukata daga aljihun abokinsa, kuma shi abokin nasa ba ya hana shi.
4- Cututtuka hatta da masu wahalar magani a Duniya suna daga cikin mafi girman matsalar dan Adam a Duniya, wadannan kuwa sun faru ne sakamakon rashin yanayi da mahalli mai lafiya da kayan nukuliya, da atom, da maikrob, da kuma alaka ta haram tsakanin mutane, da kawar da dazuzzuka, da ruwa da kuma abubuwa masu jawo cututtukan da suka hada da kuturta, da annoba, da shan inna, da bugawar zuciya da gomomin cututtuka na zahiri da badini wadanda suka gurbata rayuwar mutane kuma ba zasu juru ba.
A cikin daular jagora kuma limamin al'umma, wasiyyin Annabi na karshen Imam Mahadi (a.s) yaduwar adalci da kuma hukuma madaidaiciya zasu sanya kawuwar wadannan cututtuka na jiki da na ruhi. Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: yayin da Imam Mahadi (a.s) zai tsayar da hukuma, Allah zai kawar da dukkan wasu cututtuka daga muminai, kuma lafiya zata dawo musu.
Da wannan ne duk wata cuta maras magani zata kau, kuma lafiya da koshin lafiya su mamaye ko'ina albarkacin samuwar Imam Mahadi (a.s). Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: duk wanda ya riski Imam Mahadi (a.s) idan ba shi da lafiya to zai warke, kuma idan yana da rauni to zai yi karfi.
|