Halayen Imam Mahadi (a.s)Zalunci shi ne mafi munin abu da ake fama da shi a cikin al'ummmu, kuma al'ummu a karnoni masu yawa sun cigaba da zama cikin rashi da fatara da take hakkinsu, kuma ba a taba raba baiwar da Allah ya yi wa dan Adam ta arziki bisa daidaito ba. Don haka ne sai ka ga sun cika cikinsu dam da abinci a gefe kuma ga wasu suna fama da yunwa, wasu a cikin dogayen binaye da gine-gine alhalin wasu suna kwana a kwararo mai kunci a kusa da wadannan gidaje. Karfin da ake amfani da shi ya sanya mutane sun koma masu rauni kuma sun zama tamkar bayi ne, sannan kuma ga kabilanci na farar fata da bakar fata wanda ya isa a kashe mutum domin laifinsa shi ne shi bakar fata ne. Wadannan abubuwa da wasunsu da suka cika duniyar dan Adam sun kai shi ga burin da yake dauke da shi tilo shi ne ya kai ga samun adalci da daidaito, don haka sai ya kasance wannan shi ne abin da yake jira a kodayaushe. Amma karshen sauraro zai kai ga samuwar hukumar ni'ima ta Imam Mahadi (a.s) a matsayinsa na babban jagoran adalci domin yada adalci a Duniya a dukkan bangarorin rayuwa, kuma wannan wani abu ne da aka yi bayaninsa a cikin ruwayoyi. Imam Husain (a.s) yana cewa: Idan da Duniya babu abin da ya rage sai wuni daya, da Allah ya tsawaita wannan har sai wani daga 'ya'yana ya zo kuma ya cika Duniya da adalci kamar yadda aka cikata da zalunci. Kuma haka nan na ji daga Manzon Allah (s.a.w)[2]. Da wasu gomomin ruwayoyi da suka zo game da adalcin Duniya da kuma kawar da zalunci a wannan hukuma ta Imam Mahadi (a.s). Wani abin kayatarwa kuwa shi ne; adalci da kuma hukunci bisa gaskiya suna daga cikin mafi bayyanar siffofin Imam Mahadi (a.s) da suka zo wasu addu'o'i kamar haka: "ya Ubangiji kuma ka yi tsira ga masoyin lamarinka mai tsayuwa (da adalci) wanda ake burin (zuwansa) kuma adalci da ake sauraro[3]. Haka nan ya sanya adalci ma'auninjuyinsa, domin idan babu adalci to rayuwar daidaiku da ta al'umma da kuma Duniya damutanenta zasu kasane kamarmatattu ne da ba su da rai. Imam Musa Kazim (a.s) yana fada game da tafsirin ayar nan "Ku sani Allah yana raya kasa bayan mutuwarta"[4]. Sai ya ce: Ba ana nufin cewa ana raya kasa da ruwan sama ba, amma abin nufi shi ne; Ubangiji zai tayar da wasu mutane[5] domin su raya adalci don haka sakamakon yaduwar adalci sai ya raya kasa. Wannan yana nufin cewa adalcin Imam Mahadi zai mamaye dukkan Duniya ba wani bangare nata ba kawai. Amma tsarin hukumar Imam Mahadi (a.s) zai kasance ne kamar haka: Bayan sanin hadafin hukumar Jagoran Duniya (a.s) sai mu yi kokarin sanin tsarin da zai gudanar domin kaiwa ga wannan hadafin. Idan mun duba ruwayoyi masu yawa da suka zo game da tsarin hukumarsa (a.s) zamu ga sun kasu gida uku ne kamar haka: tsarin wayewa da al'adu, tsarin zamantakewar al'umma, da, tsarin tattalin arziki.
|