Halayen Imam Mahadi (a.s)3- Kawo juyin ilimi yana daga cikin tsarin hukumar Imam Mahadi (a.s) wanda shi kansa shi ne malamin wannan zamani gaba daya[11] da yake makomar ilimi. Manzon rahama ya yi nuni da wannan lamarin game da zuwan Imam Mahadi (a.s) yana cewa: "…kuma dukkan Duniya zata amfana daga iliminsa, bayan ta cika da jahilci da rashin ilimi…"[12]. Sannan kuma wannan lamarin bai bar mata a baya ba kamar yadda zamu iya ganin a cikin ruwayar hadisin Imam Muhammad Bakir (a.s) da yake cewa: A zamanin Imam Mahadi (a.s) za a ba ku ilimi da zai kai ga mace a cikin gidanta tanan yin hukunci daidai da abin da yake a littafin Allah da sunnar Manzonsa[13]. Wannan lamarin yana nuna mana ilimi mai zurfi na wannan zamani domin kuwa mun san hukunci da Kur'ani da ruwayoyi al'amari ne mai wahalar gaske. 4-Bidi'a tana sabanin sunna ce kuma tana nufin kawo sabon abu da shigar da shi cikin addini, kamar sanya ra'ayin mutum a addini. Imam Ali (a.s) yana fada game da bidi'a: "Bidi'a hanya ce tawanda yake sabawa da umarnin Allah da na Manzonsa, kuma yana aiki bisa ra'ayi da son ransa…"[14]. Don haka bidi'a sabawa ne da littafin Allah da Manzonsa da kuma sanya hukunci na son rai da aiki bisa ra'ayin mutum. Bidi'a wata abu ce da take kashe sunna da kuma tafarkin Allah (s.w.t). Imam Ali (a.s) yana fada: Ba abin da ya rusa addini kamar bidi'a[15]. Don haka ne ma ya zama wajibi a kawar da bidi'a, kuma a nuna wa mutane hanya tagaskiya. Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Duk sa'adda bidi'a ta bayyana a tsakanin al'ummata, to yana Sai ga shi har yanzu Duniya ba ta gushe ba tana sauraron mai tseratarwa wanda Kur'ani ya yi bayanin zuwansa wanda a karkashin hukumarsa za a tsige bidi'a gaba daya. Imam Muhammad Bakir (a.s) yana siffanta Imam Muhammad Mahadi (a.s) da cewa:… ba zai bar wata bidi'a ba sai ya kawar da ita, kuma ba zai bar wata sunna ba sai ya tsayar da ita…[17] b- Daga cikin alama ta al'umma mai kwanciyar hankali da yalwa shi ne dukiyar kasa ta kasance ba a hannun wasu jama'a kebantattu take ba, kuma al'umma gaba daya ta kasnace tana amfana daga wannan arziki. A cikin Kur'ani da ruwayoyin ma'asumai (a.s) an bayar da muhimmanci mai girma da yawa ga yanayin rayuwar mutane da tattalin arzikinsu. Don haka ne ma ya zo cewa Imam Mahadi (a.s) zai bayar da muhimmanci ga wannan al'amari kuma a bisa wannan asasin ne zai fuskanci haifar da kayan masarufi da kuma amfani da kayan ma'adinai da albarkatun kasa, sannan kuma dukiyar da aka samu zai raba wa al'umma bisa daidaito da zamu yi kokarin duba wasu daga ruwayoyi game da hakan.
1- Rashin amfana daga albarkatun kasa ta hanyar kwarai yana daga matsalolin da suka mamaye tattalain arziki, ba a amfana daga kasa ko ruwa, kuma ba a amfana ta hanyar raya kasa. Amma a hukumar Imam Mahadi (a.s) saobda albarkar hukumar adalci da gaskiya wannan hukumar zata kasance ta baiwa da kyauta, sannan kuma kasa zata fitar da komai na arzikinta. Imam Ali (a.s) yana cewa: …da Imam Mahadi (a.s) ya bayyana da Duniya ta saukar da ruwanta, kuma da kasa ta fitar da tsironta…[18]. Kuma Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: za a nade masa kasa, kuma taskokinta zasu bayyana gareshi…[19]. 2-Taskace dukiya da arzikin kasa a hannun wasu jama'a daidaiku –da kowane irin dalili ne kuwa- domin amfanin kashin kansu shi ne daya daga cikin matsalolin al'umma mafi girma, don haka ne ma Imam Mahadi (a.s) zai yi yaki da wannan kuma zai sanya dukiyar kasa a hannun mutane bisa daidaito. Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: idan mai tsayar da hukumar Ahlul Baiti (a.s) ya bayyana to zai raba dukiya bisa daidaito, kuma ya yi adalci a cikin al'umma...[20]. A wannan zamanin za a gudanar da asalin asasin daidaito, kuma kowa zai amfana daga hakkokinsa na 'yan'adamtaka kuma da wanda Allah ya huwace masa na arzikin kasa. Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Ina yi muku bishara da Imam Mahadi da zai zo cikin al'ummata… kuma zai raba dukiya da daidaito. Sai wani mutum ya tambaya me ake nufi da wannan ? Sai ya ce: zai yi rabo tsakanin mutane da gudanar da daidaito[21]. Da wannan ne za a kawar da talauci da fatara daga cikin al'umma kuma a kawar da bambancin dabakoki cikin al'ummu. Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: Imam Mahadi (a.s) zai yi hukunci da daidaito tsakanin mutane, har sai an rasa wani mabukaci da zai karbi zakka[22].
|