Halayen Imam Mahadi (a.s)



Sannan akwai hikimomi masu yawa da suke cikin boyuwarsa, domin wasu sukan yi kokarin cewa; idan zai yi gyara to don me ya buya, sun manta cewa sauran bayin Allah da suka zo gyara su ire-irensu ne suka yi yunkurin kashe su, don haka akwai hikima sosai ta boye shi har sai ranar da dan Adam ya gaji da kansa ya nemi cewa ya tuba daga abin da ya yi wa ubangijinsa na butulcewa masu gyara da ya turo musu, kuma a shirye suke su karbi wannan ragowar na Allah da ya rage masu. Don haka ne idan shi ya bayyana mutane ba zasu yi wasa da shi ba, kuma ba zasu yi kasa a gwiwa ba wurin taimaka masa (a.s).

Sannan wasu suna tambayar cewa kamar yaya zamu iya cewa Imam Mahadi (a.s) zai iya kawo canji alhalin wannan bai faru ba ga al'ummar da ta gabace shi? Wannan ma muna iya cewa ya taso ne sakamakon jahiltar karfin Allah da zai ba shi, domin idan Allah ya ga dama ya yi komai zai yi, sai dai ba mu manta da sharuddan da Allah zai tanadar masa ba, wadanda wani mutum hatta da kakanninsa ba su samu irinsu ba, hada da mataimaka da zai samu wadanda wani bai samu irinsu ba.

 

Amma game da bayyanarsa da abin da zai faru bayan ya gyara duniya muna iya cewa; Bayan tafiyar gajimare mai duhu sai hasken rana ya haskaka domin ya bayyana a idanuwan masu sauraro. Don haka ne bayan yaki da kawar da ma'abota barna da karya da masu ashararanci, sai a samu batun tabbatar hukumar adalcin Allah da kowa da komai zai zauna a matsayinsa, kuma kowane rabo ya zama a mahallinsa. Daga karshe Duniya da 'ya'yanta zasu ga hukumar adalci ta gaba daya, kuma ba zasu sake ganin mafi kankantar zalunci ba. Daula ce ta bayyanar siffofin Allah (s.w.t) da kyawunsa, kuma a nan ne dukkan mutane zasu manta da gurace-guracensu.

 

Hadafin hukumar Imam   Mahadi  (a.s) suna da bayani kamar haka ne; Mutum yana da hadafofi guda biyu da yake son cimma a cikin rayuwarsa ta Duniya da suka hada da hadafin zahiri da na badini domin kai wa zuwa ga kamalar da yake bukata, don haka hadafin hukumar Imam Mahadi (a.s) duk ya shafi duka bangarorin biyu ne, wadanda zamu kawo su a nan gaba.

A hukumar dagutanci zamu ga dan Adam yana mancewa da kyawawan dabi'u gaba daya, maimakon kyawawan halaye kamar; gaskiya da taimakekeniya da sadaukarwa da kirki, sai ya maye gurbinsu da munanan halaye kamar; son zuciya, laifi, rashin mutunci, karya da son kai, daga karshe sai kimar rayuwa da alherinta ya tafi, sai dan Adam ya fada cikin rushewa. Amma hukumar Imam Mahadi (a.s) zata zo domin raya zukatan mutane da ruhuinsu da ba su sabuwar rayuwa mai kanshi da kyau.

"Ya ku wadanda kuka yi imani ku amsa wa Allah (s.w.t) da Manzo (s.a.w) zuwa ga abin da suke kiran ku na abin da yake raya ku…"[1].

Mu sani rayuwar badinin mutum ita ce take ba wa mutum bambanci tsakninsa da dabbobi, kuma domin wannan rayuwar ne ake kiran sa "Adam", kuma da ita wannan rayuwar ne yake samun kusanci zuwa ga Allah (s.w.t).

A lokacin Imam Mahadi (a.s) rayuwar badini da kyawawan halaye zata mamaye ko'ina na samuwar dan Adam, kuma za a samu tsarkakar badini, da kaunar juna, da sadaukarwa, da cika alkawari, da gaskiya, da duk wani abu da ake kira kyau, amma mu sani kaiwa zuwa ga wannan hadafi mai girma yana bukatar tsari mai zurfi sosai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 next