Halayen Imam Mahadi (a.s)Sanannen abu ne cewa sakamakon nisanta da koyarwar Kur'ani da Ahlul Baiti (a.s) duniyar dan Adam ta samu matsaloli da fadawa cikin rushewa a wadannan janibobi na rayuwarta, amma da koma zuwa ga Kur'ani da Ahlul Baiti (a.s) togyara da cigaba da aminci zai mamaye dukkan wadannan janibobi muhimmai a rayuwar dan Adam. Bayan mun kawo bayanai a- A Daular Imam Mahadi (a.s) akwai tsari na habakar ilimi da kuma aiki na gari da al'umma zata durfafi yinsa, kuma zasu sanya wando daya da jahilci da rashin ilimi. Mafi muhimmanci a wannan janibi sun hada da: 1- Bayan tsawon lokaci da aka dauka da wurgar da littafin Allah da sunnar Annabisa, za a samu dawowar littafin Allah da sunnar Annabinsa a aikace da zarar an kafa hukumar Imam Mahadi (a.s). Game da siffanta wannan hukuma ta Kur'ani ta Jagoran Duniya Imam Mahadi ce Imam Ali (a.s) yake cewa: A lokacin da son rai yake shuganbanci sai Imam Mahadi (a.s) ya bayyana ya mayar da aiki da gaskiya mai makon son rai, kuma a wannan zamani da ake gabatar da ra'ayin mutum a kan Kur'ani sai ga shi ya mayar da tunanin mutane kan Kur'ani, kuma ya sanya shi mai hukunci a kan al'umma[6]. A wata ruwayar yana cewa: Kai ka ce ina ganin mutane yanzu a masallacin Kufa, an sanya hema, kuma ana koyar da mutane Kur'ani kamar yadda ya sauka[7]. 2- Kur'ani mai girma da koyarwar Ahlul Baiti (a.s) sun karfafi kiyaye kyawawan halaye domin wannan shi ne babban abin da zai haifar da ci gaban dan Adam zuwa ga kaiwa ga hadafin halittarsa. Kuma hadafin ma'aiki mai tsira da aminci shi ne kammala kyawawan halaye[8], domin haka ne Kur'ani yana sanar da mu cewa shi ne ya fi kowa kyawawan halaye[9]. Don haka hukumar Imam Mahadi (a.s) hukuma ce ta ubangji da a Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: "Idan Imam Mahadi (a.s) ya zo zai sanya hannunsa a Wannan al'amarin yana nuna mana cikar kyawwan halaye da zai wakana sakamakon kafa hukumar adalci ta Imam Mahadi (a.s), da kuma kamalar hankalin dan Adam, a lokaci guda kuma ga Kur'ani da sunnar Allah suna jagorantar mutane zuwa ga shiriya da aikata kyawawan halaye.
|