Halayen Imam Mahadi (a.s)Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da bayanin halayen Imam al-Mahadi (a.s) da rayuwarsa. Iyalan gidan manzon Allah (s.a.w) wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya. Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da yake kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba. Zai yi wuya mu samu wani lamari da aka yi magana kansa a musulunci da ya kai lamarin Imam Mahadi (a.s) wanda shi ne mafi girman lamarin da duk duniya take sauraro. Ruwayoyi daruruwa masu yawa daga masanan musulmi amintattu tun daga lokacin Manzon rahama (s.a.w) har zuwa wannan zamani namu ne suka zo domin su yi bayanin waye Imam Mahadi (a.s). Wani zai yi mamaki ya ga dukkan duniya tana sauraron Imam Mahadi (a.s) wanda bai kebanta da duniyar musulmi ba kawai, domin ya shafi dukkan duniya ne. Amma idan ya san mene ne ayyukan Imam Mahadi (a.s), kuma waye shi? Sannan idan ya zo wane canji ne zai kawo wannan duniya? Kuma meye aikin da ya hau Ba abin wasa ba ne zamu ga hatta da sojojin Amurka a Iraki suna neman sanin waye Imam Mahadi (a.s), kuma yaya zasu hadu da shi domin su tattauna su gana da shi, da sauran abubuwan mamaki da shi wanda ya jahilci lamarin Imam Mahadi (a.s) bai sani ba!. Wannan lamarin na Imam Mahadi (a.s) yana daga cikin abubuwan da aka jarraba mutane a kansa, har sai ya kasance wasu sun yi kokwanton samuwarsa sakamakon dadewa bai bayyana ba. Dasya daga mafi girman bahasin da yake kewaye da mas'alar Imam Mahadi (a.s) shi ne mas'alar sauraronsa da yarda da samuwarsa da jin cewa yana raye kuma yana ganin mu don haka muna bukatar mu kasance masu yarda da hakan a aikace kamar yadda muka yarda da hakan a fili. Kowannenmu ya shirya wa kansa cewa zai ji samuwar imaminsa da ba ya ganinsa a fili sai dai ya ji samuwarsa, ya nemi Allah ya yi masa dacewar ganin sad a yi masa hidima yayin bayyanarsa. Sai dai wannan yana samuwa idan mun lizimci umarninsa da haninsa sau da kafa ne. Da yawa daga Shi'a sun gafala daga wannan lamarin balle kuma wasunsu daga 'yan uwansu Ahlussunna da wasu masu yawa daga masu kokwanton samuwarsa ko ma ba su yarda da cewa akwai shi ba a yau. Mutum nawa ne yake jin cewa akwai imam Mahadi (a.s) da yake ganin ayyukansa da lamurransa kuma yana jin cewa yana kula da shi? Kuma mutum nawa ne yake jin cewa duk abin da yake yi fayel dinsa yana gaban imam Mahadi (a.s) kuma yana sane da hakan? Don haka ne addu'ar gaggauta bayyanarsa take da muhimmanci, domin tana tuna wa mumini samuwar imaminsa da idan ya mutu bai yi masa bai'a ba, to ya yi mutuwar jahiliyya. Don haka ne karfafa wannan addu'a da wannan jin a zuci yake da muhimmaci matukar gaske. Imam Mahadi (a.s) yana kula da lamurranmu duk inda muke, kuma yana kallon ayyukanmu kamar yadda ya zo a cikin ruwayoyi da kuma ayar nan da take cewa; Ku yi aiki da sannu Allah da Manzonsa da muminai zasu ga ayyukanku. Dalilai masu yawa daga ruwayoyin Ahlul-baiti (a.s) ya zo cewa muminai a wannan aya su ne Imamam kowane zamani. Ruwayoyi masu yawa ne suka zo suna nuni da wannan lamari mai muhimmanci da yake nuni zuwa ga cewa ana bujuro wa imaman shiriya ayyukan al'ummarsu domin su gani.
|