Halayen Imam Husain (a.s)Imamancinsa: Imam Husain (a.s) ya karbi mukamin Imamanci bayan rasuwar dan'uwansa Hasan (a.s) a shekara ta (50 bayan hijira). Kuma daga cikin muhimman ayyukan da ya yi a lokacin da ya karbi Imamanci su ne: 1. Ci gaba da kare da'awar Musulunci. 2. Yakar batan da ya shigo cikin al'ummar musulmi. 3. Jagoranta da kuma fuskantar da kungiyar musulmi a Kufa masu yin fada da shugabancin Umayyawa wanda ya kauce hanya. 4. Sadaukar da ransa da ya yi a ranar Ashura domin raya addinin Musulunci wanda zalunci da karyar Umayyawa ya kusan kawo karshensa. Abin Da Ya Faru A Karbala: Yazid dan Mu'awiya shugaba daga Umayyawa wanda ya yi zamani da Imam Husain (a.s) ya kasance mai barna kuma wanda ya kauce wa hukunce–hukuncen Musulunci da koyarwarsa. kuma azzalumi a cikin mulkinsa da hukuncinsa, ta yadda yanayin siyasa da na zamantakewar jama'a ya munana a lokacinsa kuma ya lalace babbar lalacewa. Musulmai masu tsarkin zukata da yin aiki domin Allah daga cikin mabiya Ahlul-baiti (a.s) a cikin Iraki sun kasance a koda yaushe suna yin kokarin gyara yanayin siyasa da na zamantakewa ta hanyoyi masu yawa na zaman lafiya, amma ba su samu nasara ba, sai suka kafa gungiyar wariya suna nufin cire Iraki daga cikin mulkin Umayyawa da kuma zabar Imam Husain (a.s) a matsayin halifan musulmai. Kuma bayan Imam Husain (a.s) ya karbi halifanci a Iraki, zasu yi kokarin gyara yanayi na gaba daya a cikin ragowar garuruwan Musulunci a bisa jagorancinsa (a.s) da kuma tsamo su daga azzalumar gwamnatin Umayyawa. Sai suka kame komai da komai a cikin garin Kufa. Kuma suka rubuta wa Imam Husain (a.s) cewar ya taho daga Madina zuwa Kufa domin ya karbi shugabanci a cikinta… Sai Imam Husain (a.s) ya aika musu Muslim bn Akil dan wan mahaifinsa domin ya san halin da ake ciki a can kuma ya karbi shugabanci na dan wani lokaci zuwa lokacin da Imam Husain (a.s) zai iso Kufa.
|