Halayen Imam Husain (a.s)



Kamar yadda labarin kyautata wa bayi da kuyangi ya shahara daga gareshi (a.s), muna gani kuyanga ta yi masa sallama sai ya â€کyanta ta, sai Anas ya yi mamakin wannan lamari, sai Imam Husain (a.s) ya gaya masa ai Allah yana umarni da idan aka yi musu gaisuwa to ku yi raddi da ita ko da abin da ya fi ta!.

Imam Husain (a.s) ya kasance cikin na farko guda hudu da Manzon Allah (s.a.w) ya fi so fiye da kowa a rayuwarsa, wannan kuwa yana nuna mana matsayinsu ne babba a wurin Allah, domin son Annabi shi ne ainihin son Allah, domin dukkan abin da ya yi to daga wahayi ne, ba don kawai yana matsayin kaka ko uba ba!.

Amma maganganun kan hikimomin Imam Husain (a.s) da hakurinsa da juriyarsa, wannan sai a yi littafi mai girma da shi, don haka mai karatu sai ya koma wa manyan littattafai da suka yi magana kan wadannan mas’aloli game shi (a.s).

Kamar yadda muka fada cewa iamm Husain (a.s) ya shahara da kyamar zalunci, mu sani yana daga abin da yake nuna girman zalunci da munin karshensa cewa, Allah (s.w.t) ya hana taimakekeniya da azzalumai, da karkata zuwa gare su. Ubangiji Madaukaki yana cewa: “Kuma kada ku karkata zuwa ga azzalumai sai wuta ta shafe ku, kuma ba ku da wasu masoya koma bayan Allah, sannan ba za a taimake kuâ€‌[1]. Wannan shi ne ladabin Kur’ani da Ahlul-baiti (a.s), hadisai da dama sun zo daga garesu wadanda suka kai matuka wajan hana karkata zuwa ga azzalumai, da alaka da su, da yin aiki tare da su a cikin kowane irin aiki, da taimaka musu ko da tsagin dibino ne.

Babu shakka mafi girman abin da aka jarrabci musulmi da musulunci da shi, shi ne sassauci ga azzalumai, da kawar da kai game da miyagun ayyukansa, da mu’amala tare da su, ballantana taimaka musu a kan zaluncinsu. Ba abin da ya jawo wa al’ummar musulmi bala’o’i sai karkacewa daga tafarki madaidaci da gaskiya, har Addini ya yi rauni tare da shudewar zamani, karfinsu ya tafi, ya kai halin da yake a yau ya koma bako. Musulmi ko kuma wadanda suke kiran kansu musulmi suka zamanto ba su da wani mataimaki ban da Allah, kuma su ba za a taimake su ba hatta a kan mafi raunin makiyansu, da mafi kaskancin masu tsaurin ido a kansu kamar Yahudawa kaskantattu, balle kuma Kiristoci masu karfi.

Sannan game da hadin kan al’umma da imamai masu daraja suka yi kokari kansa, da ilmantar da mutane, wasu suna iya cewa don me Imam Husain (a.s) ya mike don yin juyi, alhalin suna kira da hada karfi wuri guda, a kan haka muna iya cewa:

An san Ahlul-baiti (a.s) da kwadayinsu a kan wanzuwar addinin musulunci, da kira zuwa ga daukakarsa da hada kan mabiyansa, da kiyaye â€کyan’uwantaka a tsakaninsu, da cire mugun kuduri daga zukatansu, da kullace-kullace daga rayukansu, ba za a mance da matakin Amirul Muminin Aliyyu dan Abi Dalib (a.s) game da halifofin da suka gabace shi ba, duk da fushin da ya yi da su da kuma yakininsa da kwacewarsu ga hakkinsa, amma sai ya tafi tare da su, ya zauna lafiya da su, kai an boye ra’ayinsa na cewa shi ne wanda aka yi wasiyya da halifancinsa, har ya zama bai bayyana nassin ba a bainar jama’a har sai da al’amarin ya koma hannunsa, sannan ya kafa hujja da sauran wadanda suka rage daga cikin Sahabbai game da al’amarin nassin Al-Ghadir a ranar Rahba da ta shahara. Ya kasance ba ya boye shawara garesu game da abin da ya shafi musulmi ko musulunci na amfani da maslaha, sau da yawa yana fada game da wannan al’amari: “Sai na ji tsoron idan ban taimaki musulunci da ma’abotansa ba zan ga gibi a cikinsa ko rushewaâ€‌.

Kamar yadda babu wani abu da ya taba zowa daga gareshi wanda zai yi tasiri a karfafa mulkinsu, ko raunana jagorancnsu, ko rage kwarjininsu, sai ya kuntata wa kansa, ya zauna a gida duk da abin da yake gani daga gare su. Dukkan wannan saboda kiyaye maslahar musulunci ta gaba daya, da kiyaye kada a ga wani gibi a musulunci ko rushewa, har aka san haka daga gare shi, kuma halifa Umar dan Haddabi ya kasance yana fada yana kuma maimaitawa: “Kada na kasance cikin wani al’amari mai wuyar sha’ani da Abul Hasan ba ya ciki.â€‌ Ko fadinsa: “Ba don Ali (a.s) ba da Umar ya halakaâ€‌.

Haka nan ba za a mance da matakin Imam Hasan dan Ali (a.s) ba dangane da yin Sulhu da Mu’awiya, bayan ya ga cewa dagewa a kan yaki zai shafe ya kuma kawar da Alkawari mafi girma –Kur’ani- da adalci har ma da musulunci daga samuwa har zuwa karshen zamani, a kuma shafe shari’ar Ubangiji, a kuma gama da wadanda suka yi saura daga Zuriyar Manzo daga Ahlul-baiti, sai ya fifita kiyaye zahirin musulunci da sunan Addini, duk da ya yi sulhu da Mu’awiya babban makiyin Addini da ma’abotansa, mai husuma mai mugun kuduri ga Imam Hasan (a.s) da shi’arsa, tare da abin da ake tsammani na faruwar zalunci da kaskanci gareshi shi da mabiyansa, ga kuma takubban Banu Hashim da na shi’arsa a zazzare ba sa son komawa ba tare da sun yi aikinsu na kariya da gwabzawa ba, sai dai maslahar musulunci madaukakiya ita ce ta fi dukkan wadannan al’amuran.

Amma Shahidi Imam Husain (a.s) idan ya motsa to domin ya ga cewa idan aka ci gaba da halin da ake ciki, Banu Umayya ba su sami wanda zai tona asirinsu ba, to da sannu zasu shafe sunan Musulunci, su kawar da darajarsa, sai ya so ya tabbatar wa tarihi ketare iyakarsu, ya fallasa abin da suke kulla wa Shari’ar Manzon Allah (s.a.w). Ba don yunkurinsa mai albarka ba, da Musulunci ya zama wani labari ne da tarihi zai rika ambatonsa tamkar wani addinin barna. Kwadayin Shi’a a kan raya ambatonsa ta hanyoyi daban- daban ya zamanto saboda kammala sakon da yunkurinsa na dauki-ba-dadi da zalunci ne, kuma domin raya al’amarinsa na cika umarni da biyayya ga Imamai (a.s)[2].

Ziyarar Kaburbura masu daraja na Annabi da waliyyan bayin allah tana daga cikin mafi muhimancin abubuwan da musulmi suka dukufa a kanta domin samun tabarruki da ladan Allah kan hakan. Imam Husain (a.s) saboda kasancewarsa shugaban shahidai zamu ga musulmi sun shagaltu matuka da yin ziyararsa, kamar yadda akwai kuma hadisai kan falalar ziyararsa da aka karbo daga imaman gidan shiriya.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next