Halayen Imam Husain (a.s)Kare matsayin halifanci da Banu Umayya suka dare kan mulkinta ba tare da hakkin shari'a ba, don haka ne yake son ya nuna mutane cewa wadannan fasikai ba su cancanci halifancin shari'a ba, kuma su ba ahalinta ba ne. Sannan Imam Husain yana son ya 'yanta 'yancin tunanin al'umma da ta rasa a lokacin Mu'awiya da Yazid, ya dawo mata da amincinta da 'yancin fadin ra'ayi da albarkacin bakinta, don haka sai ya tashi domin kawo wannan gyara muhimmi cikin al'umma. Haka nan Imam Husain (a.s) yana son kwato 'yancin tattalin arzikin al'umma da Banu Umayya suka mamaye tun lokacin Usman dan Affan kuma aka dawo da shi lokacin Mu'awiya, bayan wafatin Imam Ali (a.s), don haka Imam Husain (a.s) ya so dawo wa al'umma da hakkinta na tattalin arziki da daidaito tsakanin mutane kamar yadda musulunci ya zo da shi. Haka nan Imam Husain (a.s) yana son dawo wa al'umma da abin da aka zalunce su aka kwace musu shi na dukiyoyinsu bisa zalunci, da danniya, don haka sai Imam Husain (a.s) ya motsa da kiran mutane domin su taimaka masa dawo da kafa adalci da kawar da zalunci. Sannan Imam Husain (a.s) ya tashi domin dawo da abin da aka shafe na ambaton ahlul-bait (a.s) musamman Imam Ali (a.s) da hatta da mai sunansa ana kashe shi ne. Labarun kin Ali (a.s) da kuma duk wani mai sunansa ya shahara a wannan lokaci, balle kuma wanda yake son sa. Ga abin da Mu'awiya ya yi na neman shafe sunan Manzon Allah (s.a.w) a kiran salla da ikama sai dai bai samu nasara ba, amma ambaton Manzon Allah (s.a.w) shi kansa ya yi karanci, don haka Imam Husain (a.s) ya tashi domin ganin ya dawo da martabar wannan gida mai daraja domin sanar da al'umma wanda ya cancanci su koma masa domin samun rabauta da shiriya. Rushewar al'ummar musulmi tana daga cikin abin da ya sanya Imam Husain (a.s) tashi domin dawo wa al'umma da martabarta da kimarta, da matsayinta na al'umma mai dauke da sakon Allah madaukaki. Sannan kuma yana son dawo da abin da aka rusa na kimar musulunci da dabi'unsa na gari, don haka sai ya kasance babu wata hanya sai ta hanyar kawar da ire-iren wadannan mutane fasikai da suka mamaye al'amuran musulmi suka hana su sakat. Sannan Imam Husain (a.s) yana son kare hakkinsa da tashin da ya yi, domin dukkan alkawuransa da na dan uwansa babu wanda aka cika musu, hasali ma wannan jagorancin nasa ne amma Mu'awiya ya dora Yazid a kai. Sannnan akwai abubuwan da Imam Husain (a.s) ya kawo a cikin hudubobinsa yayin da ya tashi domin kawo adalci da suka hada da umarni da kyakkyawa, da hani ga mummuna, da tsayar da hukuncin Allah, da kawar da bidi'o'in da aka haifar aka dasa su cikin al'ummar musulmi.
|