Halayen Imam Husain (a.s)



8. Ya tura wani kaso na mayaka ga Imam Husain (a.s) su hadu da shi kafin ya shigo Kufa, domin su tare shi a gurin da zai kasa shiga Kufa kuma zai kasa fita daga Iraki.

A lokacin da mayakan suka hadu da Imam Husain (a.s) sai suka tare shi a Karbala.

9. Bayan tare Imam Husain (a.s) a karbala sai Ubaidullahi bn ziyad ya tura mayakan da ya tanada domin yakar Imam Husain (a.s) gaba dayansu zuwa Karbala… kuma sun kasance dubbai.

Mayakan Imam Husain (a.s) kuwa ba su kai mutum dari ba.

Kuma yakin ya auku a tsakaninsu…

Sakamakon yakin dai ya kasance cewa Imam Husain (a.s) ya yi shahada shi da mabiyansa bayan jagoran mayakan Umayyawa ya ba shi zabi tsakanin bin shugabancin Yazid dan Mu’awiya ko kuma a kashe shi a aika kansa gurin Yazid… sai Imam Husain (a.s) ya zabi shahada domin kafa hujja a kan azzalumar siyasar Yazid, da kuma aikata wajabcin addini wanda yake wajabta wa musulmi sadaukar da ransa a irin wannan hali wanda dukkan hanyoyi da kayayyaki suke gazawa wajen kawar da batan shugabanni da kuma zaluncinsu…

Kuma domin musulmi su amfana daga sadaukarwar tasa da kisan nasa a wajen kawo karshen bata da kuma shugabanni wadanda suka kauce wa hanya.

Muhimmin abin da musulmi suka amfana da shi daga shahadar Imam Husain (a.s) a wajen kawo karshen Umayyawa shi ne:

1. Shahadarsa (a.s) ta buda hakikanin Umayyawa. Kuma ta tona cewa rufuwarsu da Musulunci ta kasance ne yaudara ga musulmai:

2. Ta saka jin nauyin jagorancin jama’a ga wayayyu daga cikin musulmi. Don haka ta kasance dalili guda daya tal wanda ya jawo bore da yunkurin tubabbu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next