Halayen Imam Husain (a.s)An haife shi a Madina mai haske uku ga watan sha'aba na shekara ta hudu bayan hijira, kuma an kashe shi abin zalunta da takobi a hannun bani umayyawa da umarin Yazid dan Mu'awiya a waki'ar ashura da ta shahara a ranar asabar goma ga watan Muharram, shekara ta sittin da daya daga hijira, ya tsayar da salla a wurin kuma a nan ne aka binne jikinsa mai tsarki da aka yanyanka da takubba tare da wadanda suka yi shahada tare da shi bayan kwana uku da yin shahadarsu. Dansa ne Imam Aliyyu Zainul abidin ya shirya shi ya binne shi inda kabarinsa yake a yanzu a Karbala mai tsarki inda wannan waki'ar ta auku a Karbala. Falalarsa ba ta ambatuwa saboda yawanta, shi ne kanshin sanyin idanuwan manzon (s.a.w) wanda ya fada game da shi "Husain daga gareni yake kuma ni daga Husain nake"[6]. Kuma ya fada game da shi da kuma dan'uwansa Hasan (a.s) cewa: "Su ne kanshina na duniya"[7]. Kuma mai tsira (s.a.w) ya ce: "Hasan da Husain shugabannin samarin aljanna ne"[8]. kuma ya ce: Hasan da Husain shugabanni ne sun tsaya ko sun zauna"[9]. Kuma ya kasance mafi sanin mutane kuma mafi bautarsu, ya kasance yana salla raka'a dubu kowane dare kamar babansa Imam Ali (a.s) kuma yan daukar gari a kafadarsa da dare yana raba wa talakawa har sai dai aka ga kufan wajen a bayansa bayan kashe shi, ya kasance mai yawan karimci da kyauta, mai girma da daraja ne, mai yawan hakuri, kuma mai tsanantawa idan aka sabi Allah. Daga cikin baiwarsa: wani balarabe ya zo wajensa yana mai neman kyauta sai ya ce: Babu wani yankewa daga kaunarka ko daga 'yancinka, a kofar gidanka majalisin bukata Kai mai baiwa ne kuma kai madogara ne Babanka ya kasance mai kashe fasikai Ba domin abin da na farkonku suka yi ba
|