Halayen Imam Husain (a.s)



Sannan kuma tashinsa biyayya ne ga umarnin da annabi (s.a.w) ya ba shi wanda ko da za  a kashe shi to ya hau kansa ya mike ya yi gwagwarmaya a kan hakan. Hada da cewa yana son dawo da izzar musulunci da karamarsa da aka zubar da ita a idanun duniya da aibin da ya same shi sakamakon darewar fasikai kan karagar mulki.

Sannan Imam Husain (a.s) yana son yin maganin yaudarar Banu Umayya da irin kisan gillar da suke yi wa muminan bayi da suka san suna dauke da ingantaccen musulunci da koyarwarsa mai daraja da kima.

Komai dai ya faru Imam Husain (a.s) ya yi shahada a filin Karbala kuma an ribace iyalin gidan annabi da alayensa gaba daya zuwa fadar fasiki Yazid. Sai dai duk wannan lamarin ya sanya musulunci ya girbi alheri daga makircinsu, domin makircin da suka yi ya sanya farkawar da yawan mutane da fadakarsu kan mene ne hakikanin addini, kuma ya sanya tambayoyi cikin kwakwalen mutane cewa wace irin lalacewa ce ta sami al'umma har ta kai matakin da zata kashe jikan annabi (s.a.w) da wuri haka!.

Imam Husain (a.s) ya siffantu da dukkan siffofin Manzon Allah (s.a.w) da Imam Ali (a.s) da na Imam Hasan dan’uwansa, shi ne yake misalta dabi’u da halayen wadannan zababbun bayin Allah da ba a yi kamar su ba, kuma ba za a yi ba. Kuma wadannan siffofin sun shafi siffofin jiki da na halaye duka babu bambanci, tsira da amincin Allah su tabbata gareshi.

Kuma tun da Imam Husain (a.s) shi ne mai gadon ilimin annabawa da manzanni da wasiyyansu bayan Manzon Allah (s.a.w) da babansa da dan’uwansa (a.s) don haka ne ya san dukkan wani ilmi, kuma ruwayoyi sun zo da nuni kan ilminsa da dukkan abin da wani tsuntsu yake fada. Kuma wannan duka kadan ne daga cikin ilimominsa da aka ruwaito a hadisai.

Kisan da aka yi wa Imam Husain (a.s) ba a taba yi wa wani mahaluki mummuna irinsa ba kuma bisa zalunci yana mai kokarin daukaka addinin Allah madaukaki, kama da hana shi ruwa a wannan sahara mai tsananin zafi a wannan lokacin, da kashe â€کya’yansa da danginsa a gaban idanuwansa, da yanka jaririnsa da kibiya yana hannunsa, da sauran rashin imani da aka nuna wa gidan Annabi (s.a.w).

Sannan an samu karamomi masu yawa bayan kashe shi daga abin da ya faru na kashe makasansa, da karatun Kur’ani da kansa ya yi, da yayyafin jini da sama ta yi, da jini da yake bubbugowa karkashin shuke-shuke a wannan lokaci, da jan da sama ta yi har tsawon wata shida bayan kashe shi, da sauran karamomi da suka bayyana gareshi sakamakon zaluncin da aka yi masa!

Sannan kuma akwai musibu na izina da daukar darashi da suka mamaye makasansa bayan sun kashe shi, hada da mummunan karshe da kowannensu ya yi a rayuwarsa tun daga nan duniya. 

Imam Husain (a.s) ya shahara da kyauta da baiwa da juriya da hakuri da sauran siffofin kamala, har ma ya kasance madogara kuma majinginar miskinai da talakawa da dukkan wanda bala’I ya fada masa. Ya kasance yana ciyar da maji yunwa da kishirwa, yana sadar da zumunci, yana tufatar da marasa shi, yana karfafar mai rauni, yana tausayin marayu, yana wadatar da mabukaci, da saurarn siffofin kamala da ya tattaro su.

Imam Husain (a.s) ya biya bashin Usama kusan 60000 bai saka masa da mummuna ba, duk da kuwa Usama yana daga cikin wadanda suka saba wa yin bai’a ga Imam Ali (a.s), kuma ya biya masa kafin ya mutu kamar yadda Usama ya nema. Labarun kyaututtukan Imam Husain (a.s) suna da yawa, sai dai mu takaita da abin da ya sawwaka.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next