Halayen Imam Husain (a.s)Imam Husain (a.s) ya shahara da jarumtaka da juriya da dagewa a cikin kalmomin marubuta saboda zaluncin da ya faru kansa wanda misalinsa bai faru ga wani ba a cikin fadin wannan duniyar, kuma tsananin kin sa ga zalunci ne ya sanya ake kiran sa da makiyin zalunci. Imam Husain (a.s) ya tsaya domin ganin adalci ya tsayu cikin al'umma domin tabbatar da gaskiya da imani sun kafu a kasashen musulmi, sai dai bai samu mataimaka ba. Kowa ya san irin wahalhalu da halayen da Imam Ali (a.s) ya samu kansa da kuma abin da Imam Hasan (a.s) ya fada cikinsa na rashin mataimaka kamar babansa, don haka yanayi ya yi muni matuka. Don haka sai mutane suka nemi Imam Husain (a.s) ya kama hannayensu domin ya kai su zuwa ga tsira, sai dai kamar yadda suka ci amanar babansa Imam Ali (a.s) da dan' uwansa Imam Hasan (a.s), haka nan suka ci amanarsa, sai suka bar shi tilo a filin karbala domin miyagun mutane wadanda aka tsinewa a harshen Allah (s.w.t) da manzonsa (s.a.w) suka kashe shi!. Abubuwa masu yawa ne suka sanya Imam Husain (a.s) sauraron wadannan mutane da suka hada da: Jin nauyin da yake kansa na wajbcin isar da sakon Allah (s.w.t) a irin wannan yanayi. Don haka ke nan yana da nauyi biyu da suka hau kansa, na Allah wato na shari’a da kuma na al’umma da ya hau kansa ya kawo mata gyara, kuma nauyi ne na wajibi a kansa ya yi hakan. Dukkan al'umma tana mika wuya gareshi domin su nuna masa cewa sun yanke nasu hanzari domin su a shirye suke su taimaka masa kuma shi suke jira. Kuma rashin amsa musu yana nufin ya koma abin zargi domin a zahiri al'umma ta nuna ta gane kurenta na da. Umarnin Allah da yake kansa na tsaya da tashi a irin wannan halin da ya samu kansa a ciki, wanda rashin tashinsa yana nuna bayar da halacci ga hukuma irin ta Yazidu fasiki. Tsayar da hujja kan al'umma domin su sani cewa shi ya sauke nasa nauyin, amma su masu ha'inci ne ko gaban Allah (s.w.t), don haka ba za a sake damun wani Imami ba bayansa. Kariya ga musulunci daga hadarin Yazidu da hukumarsa wadanda suka mayar da musulunci a matsayin abin wasa da isgili, wanda yin shiru kan hakan yana nuna wa duniya ke nan hukumar Yazidu tana kan shari'a ta gari ke nan.
|